Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Eid-al-Fitr: El-Rufai ya jinjina wa Musulmi kan dokar kulle

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo karshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin kanun labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • Mutum fiye da dubu 100 sun harbu da korona a Afirka
    • An yi wa dubban fursunoni afuwa a Masar saboda alfarmar Idi
    • Yadda aka yi bikin Idi a cikin dokar kulle
    • Buhari ya yi Idi a gida tare da iyali
    • Venezuela na farin ciki da sabuwar alaƙarta da Iran ka man fetur
    • Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Fadar Shugaban Najeriya
    • Buratai ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar Sallah
    • Ma'aikata 164 na wani kamfani sun kamu da cutar korona
    • Yunwa ta harzuƙa ɓeraye a Amurka
    • Sallar Idin Sabon Sarkin Kano ta farko tare da gwamna
    • Harin bam ya kashe mutum 4 ana tsakiyar shagalin sallah
    • Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Masallacin Makkah

    Duba ƙasa domin karanta labaran da wasu muhimmai...

  2. An soma shari’ar Firai Ministan Isra’ila Netanyahu kan zargin cin hanci

    An fara zaman sauraren shari’ar Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan zargin cin hanci, kwanaki kaɗan bayan an sake rantsar da shi a matsayin firai minista a wani sabon wa'adin.

    Mista Netanyahu ne firai minista na farko da ke kan karagar mulki a tarihin Isra'ila da aka yi shari'a da shi kan zargin aikata laifi.

    A daidai lokacin da ya isa kotun wadda da ta fara sauran ƙarar a birnin Jerusalem, Mista Netanyahu ya bayyana cewa an yi ƙarar shi ne domin yunƙurin hamɓarar da shi ta kowane hali.

    Ana zargin Netanyahu kan laifuka uku da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa.

    Ana ganin cewa shari'ar za ta ɗauki watanni ko kuma shekaru ana yin ta.

  3. Eid-al-Fitr: El-Rufai ya jinjina wa Musulmi kan dokar kulle

    Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Malam Nasir El rufai ya jinjina wa Musulmi bisa haƙurin da suka yi wurin yin azumi a yayin da ake tsaka da dokar kulle.

    Gwamnan ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter don taya Musulmi murnar ƙaramar sallah.

    Ya kuma yi jinjina ga jama'ar Musulmi dangane da juriya da haƙuri da suka nuna a sakamakon azumi da aka yi a lokacin kulle.

    Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da suka fara ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaduwar cutar korona fiye da watanni biyu da suka gabata.

  4. Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Masallacin Makkah

  5. Labarai da dumi-dumi, Harin bam ya kashe mutum 4 ana tsakiyar shagalin sallah

    Harin bam ya kashe mutum hudu a Somalia a daidai lokacin da ake shagulgulan ƙaramar sallah a ƙasar.

    Waɗanda suka shaida kai harin sun bayyana cewa bam din ya tashi ne a daidai lokacin da jama'a ke cikin rera waƙoƙi tare da rawa a garin Baidoa da ke ƙasar.

    Babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai harin, sai dai shekaru da dama, kungiyar nan da ke iƙirarin jihadi ta Al Shabab ce ke kai akasarin hare-hare a ƙasar.

    Ƙungiyar ta fi mayar da hankali ne wurin kai wa sansanonin sojoji hari da sauran manyan wurare a ƙasar.

  6. Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Ghana

  7. Sallar Idin Sabon Sarkin Kano ta farko tare da gwamna

  8. Yunwa ta harzuƙa ɓeraye a Amurka

    An gargaɗi mazauna Amurka da su yi hankali da ɓeraye sakamakon suna neman duk wata kafa da za su shiga gidajen mutane.

    Hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta ƙasar ta bayyana cewa a 'yan kwanakin nan ana yawan samun rahotanni kan yadda ɓeraye ke ɓarna sakamakon abincin da suke samu ya ragu.

    Akasarin ɓerayen na samun abinci ne daga bolar da aka fitar ta gidajen abinci da wuraren kasuwanci, a halin yanzu duk babu irin wannan tarin bolar wanda hakan ya harzuƙa berayen fita neman abinci.

    Hukumar CDC ta gargaɗi jama'a da su toshe duk wata ƙaramar kafa da za ta bai wa ɓeraye damar shiga gidajensu ko wuraren kasuwanci.

  9. Ma'aikata 164 na wani kamfani sun kamu da cutar korona

    Wani kamfanin haƙar ma'adanai a Afirka ta Kudu ya bayyana cewa mutum 164 sun kamu da cutar korona.

    Kamfanin ya bayyana cewa tuni aka killace duka waɗanda suka kamu da cutar kuma an tsayar da gudanar da dukkan ayyuka a kamfanin.

    Sama da mutum 20,000 ne suna kamu da cutar korona a Afirka ta Kudu kuma ita ce ƙasa ta daya a nahiyar Afirka a yawan masu cutar ta korona.

  10. Buratai ya kai wa Gwamna Zulum ziyarar Sallah

    Hafsan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai ya kai wa Gwamnan Borno ziyarar Sallah a fadar gwamnatin jihar ranar Lahadi.

    Da yake tarɓarsa, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce da ma can yana da ƙwarin gwiwa kan rundunar a yaƙin da take yi da Boko Haram duk da irin saɓanin da aka samu.

    "Wannan gwamnati a ƙarƙashin mulkina za ta ci gaba da yin amanna da sojojin Najeriya," in ji Gwamna Zulum a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar.

    A nasa jawabin, shi ma Janar Buratai ya gode wa gwamnatin Borno "bisa haɗin kai da take bai wa sojoji" sannan ya gode wa rundunar musamman ta Operation Lafiya Dole.

    Buratai ya koma Jihar Borno da zama domin jan ragamar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

    Rundunar sojin ta ce ta kashe 'yan kungiyar ISWAP 48 ranar 7 ga watan Mayu.

  11. Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Fadar Shugaban Najeriya

  12. An yi wa mutum fiye da miliyan ɗaya gwajin korona cikin kwana daya a Wuhan

    A Wuhan, birnin China da ke yankin Hubie inda kuma cutar korona ta faro, an yi wa mutum fiye da miliyan ɗaya gwajin cutar ta korona, a cewar hukumomin lafiyar yankin.

    Jumillar mutum miliyan 1.1 aka yi wa gwajin, ƙasa da miliyan 1.4 da aka yi wa a rana kafin wannan.

    An fara gwajin na kan me uwa da wabi ne bayan an samu wani wuri da mutane da yawa suka kamu. Hukumomi sun yi alƙawarin yi wa mutum miliyan 11 gwajin cikin kwana 10.

    An yi amannar cewa cutar ta samo asali ne daga wata kasuwar dabbobi da ke birnin na Wuhan, wadda tuni ta yi ajalin mutum fiye da 341,000 a duniya.

  13. Venezuela na farin ciki da sabuwar alaƙarta da Iran ka man fetur

    Ƙasar Venezuela ta yaba wa Iran a daidai lokacin da tankar man fetur ta farko a cikin guda biyar ta shiga iyakokin ruwanta daga Iran ɗin ɗauke da mai sama da ganga miliyan ɗaya.

    Ministan man fetur na Iran, Tareck El Aissami, ya ce haɗin gwiwar gwamnatinsu da Iran, abu ne da zai amfani dukkan ƙasashen biyu.

    Tankokin man fetur ɗin Iran, na samun rakiyar dakarun sojin sama da na ruwan Venezuela. Amurka wadda ta ƙaƙaba takunkumi kan ƙasashen biyu, ta ce tana bibiyar rukunin jiragen ruwan.

    Ƙasashen Venezuela da Iran sun gargaɗin mahukuntan Amurka da su kiyayi wannan jigila.

    Venezuela na fama da ƙarancin tataccen mai, duk da ɗumbin arziƙin rijiyoyin man fetur da take da su.

  14. Taliban ta tsagaita wutar kwana uku don bikin Ƙaramar Sallah

    Ƙungiyar Taliban ta ba da sanarwar tsagaita wutar kwana uku da gwamnatin Afghanistan wadda za ta fara aiki daga ranar Ƙaramar Sallah a Lahadin nan.

    Matakin na zuwa ne bayan ƙaruwar hare-hare daga ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-baya masu tsattsauran ra'ayi kan dakarun gwamnati cikin makwannin baya-bayan nan.

    Shugaba Ashraf Ghani ya yi maraba da sanarwar, kuma ya ce sojojinsa za su mutunta sharuɗɗan wannan yarjejeniya.

    Yarjejeniyar ta tsawon kwana uku mai yiwuwa ne ta haɓɓaka fatan raguwar ayyukan tarzoma na tsawon lokaci a ƙasar.

    Sai dai ba a iya tsawaita wata makamanciyar wannan yarjejeniya da aka cimma saboda sallar idi ba a shekara ta 2018.

  15. Bayanan baya-bayan nan daga Nahiyar Asiya

    • Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi, ya ce mafarki ne kawai mutane ke yi idan har suka yi tunanin cewa ƙasarsa za ta biya fansa saboda yaɗuwar annobar korona
    • China, inda cutar ta faro a shekarar da gabata, ta bayar da rahoton ƙarin mutum uku da suka harbu da korona, kwana ɗaya bayan an shafe awa 24 ba tare da wani ya harbu ba. Mutum kusan 83,000 ne suka kamu jumilla, da kuma sama da 4,600 da suka mutu
    • Koriya ta Kudu ta samu wasu mutum 23 da suka kamu ranar Asabar, mafi yawa a birnin Seoul, inda hukumomi suka rufe dubban wuraren casu da na shan barasa domin daƙile yaɗuwar cutar
    • Ƙasar Indonesia ta samu ƙarin mutum 949 da suka harbu ranar Asabar, abin da ya kawo jumillarsu zuwa 21,745 da kuma mutuwar 1,351
  16. Gwamnan Borno ya yi Sallar Idi, ya ce a ci gaba da addu'a

    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya gabatar da Sallar Idi a masallacin gidan gwamnatin jihar tare da Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi.

    Wata sanarwa da fadar gwamnatin Borno ta wallafa a shafukan zumunta ta bayyana cewa an yi gajeriyar huɗuba yayin sallar, wadda aka gudanar a Dandalin Ramat, a wani salo na yaƙi da annobar korona.

    Kazalika sanarwar ta ce Zulum ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da yi wa jihar addu'a domin maganin annobar da kuma dawowar zaman lafiya.

  17. Buhari ya yi Idi a gida tare da iyali

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da Sallar Idi a fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja tare da Uwar Gida Aisha da kuma sauran iyali.

    Da ma Buhari ya ce a gida zai yi Idin sannan kuma ya ce kada wanda ya kawo masa ziyarar Sallah.

    "Hatta a lokacin da muke bikin Eid-el-fitr (Ƙaramar Sallah), muna sane da irin halin da muke ciki," in ji Buhari, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    "Mu lura da darussa da albarkar wannan lokaci sannan mu ci gaba da ɗabbaƙa su a nan gaba. Ina yi muku Barka da Sallah."

  18. Yadda aka yi bikin Idi a cikin dokar kulle

    Kamar yadda alamu suka nuna tun kafin lokacin ya yi, miliyoyin al'ummar Musulmi a faɗin duniya sun yi bikin Ƙaramar Sallah a cikin dokar kulle saboda annobar korona.

  19. Hukumar NCDC na yi muku Barka da Sallah

    Hukumar da ke bayar da alƙaluman annobar cutar korona da sauran cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, na taya ɗaukacin Musulmin Najeriya Barka da Idin Ƙaramar Sallah.

    Kamar yadda aka saba, NCDC ta yi kira da kada a manta da ɗaukar nauyin kare kai daga cutar korona, wadda tuni ta yi ajalin mutum 221 a Najeriya sannan 7,526 suka kamu da ita.

    Idan ana neman agajin hukumar ko ana son bayar da rahoton kamuwa da korona, to ga lambar da za a iya samun ta 080097000010

  20. An yi wa dubban fursunoni afuwa a Masar saboda alfarmar Idi

    Shugaban Ƙasar Masar wato Egypt, Abdel Fattah al-Sisi, ya yi afuwa ga dubban fursononi saboda alfarmar Idin Ƙaramar Sallah.

    A cikinsu har da mutumin da ya kashe wata mawaƙiya 'yar ƙasar Lebanon, Suzanne Tamim. Mohsen al-Sukkari, tsohon ɗan sanda ne da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 25 a gidan yari saboda aikata kisan kai fiye da shekara 10 a Dubai.

    Saurayin Suzanne Tamim - wanda hamshaƙin ɗan ƙasa ne a Masar da ke hada-hadar gidaje - ya biya dala miliyan biyu domin a aikata kisan kan.

    Al'ada ce ga shugabannin Masar su karrama bukukuwan addini da na ƙasa ta hanyar yin afuwa ga ɗaurarru.