Kasuwar saye da musayar 'yan ƙwallon ƙafa, Makomar Coutinho da Willian da Haaland da Sancho da Pochettino da Kavertz
Chelsea, Manchester United da kuma Leicester sun tuntubi wakilin dan wasan Barcelona Philippe Coutinho domin dauko shi a bazara, sai dai dan wasan na Brazil dan shekara 27 ya fi son komawa Chelsea.
Dan wasan Chelsea mai shekara 31 na kasar Brazil, Willian ya nuna alamar zai iya sanya hannu a kan yarjejeniya ta takaitaccen lokaci zuwa karshen kakar wasa ta bana a yayin da ake sa ran kakar wasan Premier za ta zarta ranar 30 ga watan Yuni, wato ranar da kwangilarsa za ta kare.
Tsohon dan wasan Liverpool John Barnes ya ce dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, yana da dukkan kwarewar da ta kamata wajen maye gurbin Roberto Firmino a Anfield.