COVID-19: Za a rage albashin ma'aikata a Masar
Gwamnatin Masar ta sanar da daukar matakan yin tsimi domin samun damar farfado da tattalin arzikinta wanda ya tabarbare sakamakon annobar korona.
Cikin matakan har da rage kashi daya cikin dari na albashin ma'aikata sannan za a rage kashi hamsin cikin 100 na kudin fansho da ake bai wa tsofaffi.
Za a soma aiwatar da matakan ne daga watan Yuli kuma za a yi shekara guda ana aiwatar da su. Sai dai lamarin ba zai shafi ma'aikatan da ke karbar kasa da $125 a duk wata ba.
Kazalika lamarin ba zai shafi ma'aikatan da ke aiki a fannin yawan bude ido ba, wanda annobar korona ya shafa sosai.