Rufewa
To masu bibiyarmu nan muka kawo karshen kawo muku bayanai kai tsaye a yau. Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu. Mun gode.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.
Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail
To masu bibiyarmu nan muka kawo karshen kawo muku bayanai kai tsaye a yau. Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu. Mun gode.

Asalin hoton, Getty Images
Ana dab da fara gwajin wani maganin zazzabin malariya don ganin ko zai iyi magance cutar korona a Lagos, cibiyar kasuwancin Nigeria.
Kwamishinan lafiya na jihar Lagos ya tabbatar da cewa za a bada chloroquine ko kuma wata kwayar maganin ta fankanfayau watau placebo a turance.
Gwamnatin jihar Lagos ce za ta gudanar da gwajin farko a yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO za ta gudanar da gwaji na biyu.
Ana saran samun sakamakon gwajin na gwamnati cikin wata daya zuwa biyu.
A yayin da za a yi gwajin bisa bin dokokin kiwon lafiya, hukumar ta WHO ta yi gargadin cewa duk wadanda suka yi amfani da wadannan magungunan ba tare da izinin likita ba, lallai za su iya yi wa kansu lahani.
Kawo yanzu maganin Choloroquine bai nuna alamun zai iya warkarwa ko kuma hana kamuwa da cutar korona ba, kuma maganin ka iya jawo ciwon zuciya.
Kwamishinan lafiyan na jihar Lagos , Farfesa Abayomi ya ce gwamnatin jihar ta soma amincewa masu cutar korona su killace kansu a gidajensu kuma ba dole bane sai an kwantar da su a cibiyoyin killace masu korona da gwamnati ta kebe.
A cewar gwamnatin jihar ta Lagos wannan matakin zai kawo karshen layar zana da wasu mutane kan yi da zarar gwaji ya nuna suka dauke da cutar korona.

Asalin hoton, ZSTG
An tube Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Alhaji Shehu Muhammad Faru tare da mataimakinsa daga muƙaminsu bayan wata tara da hawa karagar mulki.
Rahotanni daga jihar sun bayyana cewa tuni aka rantsar da Muhammad Sirajo Madugu a matsayin sabon shugaba, wadda ita ce ƙaramar hukumar Gwamna Bello Matawalle.

Asalin hoton, Mamuda
Tun farko dai an tsige Alhaji Ahmad Abubakar ne daga muƙamin sannan aka naɗa mataimakinsa Shehu Muhammad Faru, abin da har yanzu shi Ahmad Abubakar ke ƙalubalanta a kotu kafin kuma yanzu a bayar da sanarwar tuɓe su baki ɗaya daga muƙamin.
Yunƙurin BBC na ji daga gare su ya ci tura amma rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Ahmad Abubakar ya kasance mai biyayya ga tafiyar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari.
Kabiru Muhammad Danwanti, wanda shi ne Kansilan Mazaɓar Dosara/Birnin Kaya ya bayyana cewa an tsige shugaban ne sakamakon rashin gudanar da aiki yadda ya kamata.
An yi ta samun rashin jituwa a siyasance tun bayan da kotu ta ƙwace kujerar gwamnan jihar Zamfara daga jam'iyyar APC ta bai wa PDP, inda ta ce APC ba ta da ɗan takara a zaɓen 2019 da aka gudanar.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ƙasar Tanzania John Magufuli ya bayar da sanarwa cewa ɗaliban jami'a da kuma ɗaliban shakarar ƙarshe na sakandare za su koma azuzuwansu daga ranar 1 ga watan Yuni.
Harkokin wasanni waɗanda aka dakatar kusan tsawon wata biyu domin daƙile yaduwar cutar korona, su ma za su ci gaba.
Sai dai sauran ɗaliban sakandare da firamare ba za su koma ba zuwa lokacin.
'Yan Najeriya uku da suka maƙale a filin jirgin saman Suvarnabhumi na ƙasar Thailand suna gab da komawa gida, a cewar hukumomi a Najeriya.
Matafiyan sun maƙale ne tun watan Maris bayan saka dokokin hana zirga-zirga domin daƙile yaɗuwar annobar korona.
Hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasar waje ta ce ofishin jakadancin Najeriya a Bangkok, babban birnin ƙasar, ya yi ta tuntuɓar mutanen domin taimaka musu.
Hukumar ta gode wa wani ɗan Birtaniya a shafinta na Twitter bisa yaɗa halin da mutanen suke ciki a shafukan sada zumunta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar, ta ce bai kamata a yi taron Sallar Idi ba saɓanin yadda wasu jihohi ke bayar da damar yi.
Kwamitin fatawa na ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Alhusainy ya tatattauna tare da fito da matsayarsu game da sallar yayin annobar korona kamar haka:

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta tabbatar da sabbin mutum 2,532 da suka harbu da cutar korona da kuma 2,562 da suka warke.
Yanzu jumillar waɗanda suka kamu da cutar ya kai 65,077, sai kuma waɗanda suka warke 36,040, a cewar wata sanarwa daga Ma'aikatar Lafiya a cikin rahoton jaridar Saudi Gazette.
Ma'aikatar ta kuma ce wasu 12 sun mutu, abin da ya kai jumillar adadin zuwa 351.

Asalin hoton, FCTA
Hukumar Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta FCTA ta kama mutum 84 da suka keta dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi, ciki har da motar ɗaukar kaya ta Dangote.
Hukumar ta bayyana haka ne a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter yau Alhamis, inda ta yi holan waɗanda ta kama ɗin ciki har da mata da ƙananan yara.
Da yake magana, mai gabatar da mutanen ya ce sun yanke shawara cikin tausayi cewa za a mayar da mata da yaran inda suka fito amma za a ci gaba da riƙe mazan da aka kama domin ɗaukar mataki a kansu.
Mafi yawan motocin da aka kama na haya ne, wasu maƙare da kayan da suka wuce kima.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Lissafin da masana ilimin taurari suka yi a Saudiyya ya nuna cewa abu ne mai wuya a ga jaririn watan Shawwal na Karamar Sallah a yammacin ranar Juma'a, ranar da azumi yake cika 29.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito hasashen da suka yi na nuna cewa wata zai riga rana faɗuwa ranar Juma'a, saboda haka ranar Idi ita ce Lahadi 24 ga watan Mayu, yayin da za a yi azumi 30.
Wata cibiyar masana taurari ce a Saudiyya da ke Jami'ar Majmaah a kusa da birnin Riyadh ta bayyana hakan.
Cibiyar binciken ta ce: "Bisa hasashen da masana ilimin taurari suka yi wanda aka wallafa, ya ce rana za ta faɗi da ƙarfe 6:39, yayin da wata zai faɗi da ƙarfe 6:26 ranar Juma'a. Hakan na nufin wata zai faɗi minti 13 kafin rana ta faɗi.
"A ranar Asabar, 30 ga watan Ramadana, daidai da 23 ga Mayu, rana za ta faɗi da ƙarfe 6:40 sannan jaririn wata ya faɗi da ƙarfe 7:23, abin da ke nufin watan zai ci gaba da kasancewa har tsawon minti 43 bayan faɗuwar rana," a cewar cibiyar.
A gefe guda kuma, Dr. Abdullah Al-Mosnad, Farfesa a sashen Kimiyyar Ƙasa na Jami'ar Al-Qassim, ya jaddada cewa wata zai faɗi minti 10 kafin rana a ranar Juma'a a birnin Makkah, saboda haka sai ranar Lahadi za a yi Idi bayan cikar azumi 30.
Zakkar Fidda-Kai kamar yadda Bahaushe ke kiranta - ko kuma Zakatul Fiɗr a Larabce - zakka ce da ake yi bayan kammala azumin watan Ramadana.
Magidanci zai auna sa'i huɗu - mudun nabi - na abincin da mutanen gida suke ci a matsayin abincin mutum ɗaya da ke ƙarƙashin ciyarwarsa sannan a bai wa mabuƙata, kamar yadda Malam Dr Jabir Sani Maihula ya yi bayani.

Asalin hoton, Twitter/Nigerian Army
Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar ta ce "ta kashe 'yan bindiga 49" a cikin abin da bai kai mako biyu ba a yankin arewa maso gabas da kuma jihohin Katsina da Zamfara da Borno da Benue.
Daga cikin waɗanda rundunar ta ce ta halaka, 20 'yan Boko Haram ne sai kuma 'yan fashi 29 tun daga 11 ga watan Mayu.
Rundunar dai tana bayar da bayanai ne game da gudummawarta game da yaƙi da annobar korona a Najeriya cikin wata sanarwa da John Enenche, wani jami'in bayar da bayanai na rundunar ya fitar ranar Alhamis.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarunta sun kuma yi nasarar ceto wasu 'yan kasashen China da Ghana da Ivory Coast da 'yan fashin kan teku suka sace ranar Juma'a.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Wani jariri ɗan kwana biyu ya rasu a Afirka ta Kudu bayan mahaifiyarsa da ta haife shi a matsayin bakwaini ta harbu da cutar korona.
Shi ne mutum mafi ƙanƙantar shekaru da ya mutu sakamakon annobar korona a ƙasar.
Ministan Lafiya Zweli Mkhize ya ce jaririn yana da matsalar numfashi kuma ya buƙaci taimakon na'ura jim kaɗan bayan an haife shi.
"Mahaifiyar ta kamu da korona kuma daga baya shi ma jaririn ya kamu. Ya kamata kada mu manta cewa bakwaini ne," in ji ministan.
Afirka ta Kudu wadda ta fi kowacce ƙasa a Afirka yawan masu cutar korona, ta bayar da rahoton mutuwar wasu mutum 27 ranar Laraba, inda jumillarsu ta zama 339.
Sabbin waɗanda suka kamu guda 803 ne, jumillarsu kuma 18,003.

Asalin hoton, @LadanSalihu1
Jihar Bauchi ta shiga sahun jihohi na baya-bayan nan da suka bai wa jama'a damar ci gaba da gudanar da tarukan addini, ciki har da sallolin Juma'a da Idi.
Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Bauchi, Ladan Salihu ne ya bayyana hakan ranar Talata a shafinsa na Twitter. Sai dai ya ce babu bukukuwa kamar daba, a cewar umarnin da Gwamnan jihar Bala Mohammed ya bayar.
Ranar Asabar ko Lahadi ake sa ran yin Idin Ƙaramar Salla, kuma tuni jihohi irinsu Kano da Borno da Jigawa da Adamawa da Gombe suka bayar da damar buɗe masallatan Idi domin gudanar da sallar da ake yi saboda kawo ƙarshen azumin watan Ramadana.
Sai dai gwamnatin tarayyar Najeriya na ƙorafi kan sassauta dokokin kulle da gwamnonin ke sassautawa a jihohinsu, inda ta ce "muna tufka jihohi na warwarewa" a yaƙin da ake yi da annobar korona a ƙasar.
Ya zuwa ranar Alhamis, mutum 224 ne aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Bauchi, yayin da 5 suka rasa rayukansu sannan 130 suka warke a cewar alƙaluman hukumar NCDC.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Hukumomi a Sudan ta Kudu sun ce akalla mutum 300 sun mutu sannan da dama suka jikkata a sabon rikicin kabilancin da ya barke a jihar Jonglei da ke gabashin kasar.
Ma'aikatan agaji uku, ciki har da likitocin Médecins Sans Frontières, suna cikin wadanda aka kashe.
Rikicin ya barke ne ranar Asabar tsakanin kabilar Murle da Lou Nuer. Wani dattijo a yankin ya shaida wa BBC cewa matasa 'yan kabilar Murle sun cinna wuta kan kauyuka a gundumar Uror kafin a fatattake su.

Ma'aikatan lafiya sun ce akasarin mutanen da suka mutu suna dauke da harbin bindiga. An kwashe wasu daga cikinsu a jirgin sama zuwa Juba, babban birnin kasar domin a yi musu magani.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ta Kudu ya turo da masu wanzar da zaman lafiya yankin. Wasu mutanen sun yi yunkurin komawa gidajensu amma aka koma da su inda suka fito saboda fargabar sake barkewar rikici.
Hukumomi sun ce an kashe kimanin mutum 800 tun da aka soma kai hare-haren ramuwar-gayya a watan Fabrairu.
Majalisar wakilan Najeriya ta kaddamar da bincike kan yawan kashe fararen hula da ake zargin wasu jami'an tsaron kasar na yi yayin aiwatar da dokar kullen da aka kafa.
A wasu sassan kasar jama'a na kokawa kan halayyar wasu jami'an tsaro ta azabtarwa da kuma karbar cin hanci a wasu lokutan ma har da kisa.
Ko da a watan da ya gabata, sai dai hukumar kare Hakkin bil-Adama ta ce yawan mutanen da jami'an tsaro musamman yan sanda suka kashe ya haura yawan wadanda ita kanta annobar ta kashe.
Hukumomin tsaron dai a nasu bangaren na cewa suna daukar matakan dakile aukuwar hakan.
Yusuf Adamu Gagdi dan majalisar wakilai ne daga jihar Filato, shi ne kuma ya gabatar wa majalisar kudurin neman yin bincike.
Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraren karin bayanin da ya yi wa Is'haq Khalid:
Cutar korona ta kama mutum fiye da miliyan biyar a fadin duniya, a cewar sabbin alkaluman da Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka, wacce take bin diddigin cutar.
Ya zuwa ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2020, cutar ta kashe mutum 328,172.
Jami’ar ta kara da cewa mutum 1, 899, 675 ne suka warke daga cutar.
Amurka ce a kan gaba a kasashen da suka fi kamua da cutar, inda 1,551,853 suka harbu da ita

Asalin hoton, Getty Images
Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da safiyar Alhamis.
Muna fatan za ku kasance da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.
Za ku iya bibiyarmu a shafukan sada zumunta inda za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku.