India da Bangladesh za su fuskanci guguwar Cyclone
Kasashen India da Bangladesh na ta faman jigilar kwashe miliyoyin al'ummarsu da ke zaune a bakin ruwa a yunkurin kawar da su gabanin mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa da ke tunkarar kasashen biyu yanzu haka.
Ana hasashen guguwar za ta afka kan jihohin India guda biyu na Bengal ta yamma da Odisha da kuma wasu sassan kasar Bangladesh.
Masana yanayi sun hasashe cewa guguwar za ta afka wa wani wuri ne da ke kan iyakokin kasar guda biyu ranar Laraba.
Duk da cewa kasashen guda biyu na da kwarewa wajen tun karar irin wannan guguwa idan ta taso saboda sabo da suka yi da ibtila'in, cutar korona na yi wa shirin kwashe jama'ar cikas.
An kafa karin tanti-tanti a wuraren da za a tsugunar da mutanen domin tabbatar da samun tazara tsakaninsu sannan kuma ana raba wa mutane takunkumin fuska domin kariya daga annobar korona.