Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ganduje ya amince a yi Sallar Juma'a da Idi

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Coronavirus: Tattalin arziki mafi karfi na uku a duniya ya shiga rudani

    Kiyasi daga Japan ya nuna cewa tattalin arzikin kasar wanda shi ne na uku mafi girma a duniya ya fada cikin matsi a karon farko tun shekara ta 2015.

    Ma'aunin tattalin arzikin kasar ya tsuke a karo na biyu cikin watanni uku tun daga watan Maris.

    Japan na gab da fadawa cikin yanayi tattalin arziki irinsa mafi muni tun yaki duniya na biyu saboda fama da ake da annobar korona.

    Rahotanni sun ce akwai fargabar tattalin arzikin zai sake durkushewa a watannin 4 na tsakiyar shekarar nan ganin yadda daga Maris zuwa Afrilu rashin fitar mutane ya girgiza tattalin arzikin kasar.

    Tuni dai gwamnatin Shinzo Abe ta sanar da shirin rage radadin tasirin tattalin arziki inda za ta raba tallafin dala triliyan guda ga 'yan kasar -- sannan akwai wasu shirye-shirye da za su biyo baya nan gaba a cikin wannan watan

  2. An sallami karin mutum 20 da suka warke daga korona a Bauchi

    Gwamnan jihar Bauchi, Bala mUhammad ya sanar a shafinsa na Twitter na cewa karin mutum 20 sun warke daga cutar korona kuma tuni aka sallame su daga wurin da ake killace da su.

    Bala muhammad ya kara da cewa hakan ya kawo adadin mutanen da suka warke a jihar zuwa 89.

    Sai dai ya kara yin kira ga 'yan jihar da su bi umarnin jami'an lafiya dangane da matakan kariya daga annobar.

  3. Coronavirus: Halin da ake ciki a Sao Polo

    Magajin yankin Sao Paulo birnin mafi girma a Brazil, ya umarci mazaunan yankin su daina karya dokar kulle, yayin da ya yi gargadin cewa fanin lafiyarsu na gab da durkushewa.

    Alkaluma sun nuna cewa akasari al'ummar Sao Paulo sun yi biris da umarni bai wa juna tazara, abin da ya harzuka Magajin.

    Bruno Covas ya ce mawuyancin yanayi ne a ce mutane sun mayar da yanayin da ake ciki na wasa suna yadda suka ga dama.

    Mista Covas ya ce asibitocin gwamnati na gab da kai wa kololuwa domin yanzu an ci karfinsu da kashi 90 cikin 100, kuma yana tattauna wa da gwamnan jihar kan kara tsaurara matakan kulle kafin a rasa asibitin kai mara lafiya.

  4. 'Yan majalisa sun bai wa hammata iska a Hong-Kong

    Rikici ya barke tsakanin 'yan majalisa a Hong Kong inda 'yan siyasa magoya bayan tsarin demokradiya da masu goyan bayan gwmanati suka bai wa hammata iska.

    Bangarorin biyu na rigima ne a kan shugabancin wani babban kwamiti mai muhimmanci.

    Wannan yanayi ya kai ga dambe inda 'yan majalisar suka rinka cakuman juna da bankade-bankade da yi wa juna ihu.

    Jami'an tsaro sun fitar da manyan masu goyan bayan tsarin demokradiya biyu daga zauren majalisar a lokacin hantsaniyar.

  5. Coronavirus: Ana sassauta dokar kulle a Italiya

    Italiya ta sake fadada matakan da take dauka na dage dokar kullen mako 10 sannu a hankali.

    A yau za a bude shaguna da kantunan sayar da abinci da barasa da shagunan gyaran gashi, sannan za a bude coci.

    Sai dai za a tsaurara matakan tsafta inda iyalai kadai ne za su iya zama tare a wuraren sayar da abinci sannan shagunan gyaran gashi ba za su amince da kwastomimi da ke shiga kai tsaye ba.

    Har wa yau, malaman coci za su rinka amfani da safar hannu.

    Kasar Portugal ma ta shiga mataki na biyu na sassauta dokar kulle, inda mutane yanzu za su koma hada-hadarsu a kan tittuna.

    Su kuwa Jamhuriyar Ireland da Ireland ta Arewa yanzu za su soma daukan matakan farko na sassauta dokar hana zirga-zirgar, koda yake kowacce da irin nata ka'idojin.

  6. Jihar Kano za ta mayar da almajirai 2000 jihohinsu

    A yau Litinin ake sa ran gwamnatin Kano za ta fara mayar da almajiran su 2000 da ta killace a wasu kananan hukumomin jihar.

    Matakin killace almajirai a Kano na zuwa ne a dai-dai lokacin da ce-ce ku-ce da ya kunno kai a kan mayar da almajiran da gwamnatin ta Kanon ta yi zuwa wasu jahohin da ke arewacin kasar, bayan samun almajiran dauke da cutar korona.

    Da yake yi wa BBC karin bayani kwamishinan ilimi na Kano kuma shugaban kwamitin mayar da almajiran ga iyayen, na gwamnati Kano Muhammadu Sanusi Kiru ya ce za su mayar da almajiran ne zuwa jahohinsu tare da takardar sakamakon gwanjin cutar korona da ke tabbatar da cewa ba sa dauke da cutar.

    A baya dai jihar ta mayar da almajiran ba tare da an yi musu gwaji ba, inda wasu jihohin suka gwada su kuma suka same su da cutar, al'amarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

    Gwamnonin jihohi da dama sun zargi jihar Kano da shigar da cutar korona zuwa jihohin ta hanyar mayar da almajiran da ke dauke da cutar ta korona.