Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta hana fita ranar Asabar

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Wasu daga cikin 'yan Najeriya da aka kwaso daga Dubai na da korona

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya bayyana a yau Lahadi cewa gwaji ya nuna uku daga cikin 'yan Najeriya da aka ɗebo daga ƙasar Daular Larabawa ko kuma Dubai sun kamu da cutar korona.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa tuni aka kai su cibiyoyin killace masu cutar domin ɗaukar mataki na gaba.

    Kazalika ya jaddada cewa Legas za ta ci gaba da ɗabbaƙa dokokin killacewa domin daƙile cutar - Legas ce cibiyar cutar korona a Najeriya da mutum 2,373 da suka kamu da ita.

    Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya ce za a riƙa killace 'yan ƙasar da aka kwaso zuwa gida daga ƙasashen waje na tsawon mako biyu a Abuja.

    Wasu daga cikin ƙasashen da aka kwaso 'yan Najeriya sun haɗa da Birtaniya da Amurka da Dubai.

  2. Kamfanonin da suka samu riba da asara lokacin annobar korona

    Annobar cutar korona ta kawo durkushewar tattalin arziki amma dokokin kulle da suka taƙaita zirga-zirga sun taimaka wa wasu masana'antu wajen ci gaba.

    Misali, mutane da yawa sun koma sayayya a shafukan intanet, kuma hakan ya kawo ci gaba sosai ga ɓangaren saye da sayarwa ta intanet.

    Tabbas hakan ya taimaka wa wasu kamfanoni, amma alkaluman da ke fitowa daga babban kamfanin saye da sayarwa ta intanet na Amurka, Amazon, sun nuna cewa lamarin ba haka yake ba.

    Ƙarƙashin jagorancin mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya, Jeff Bezos, Amazon ya yi suna a tsakiyar watan Afrilu a matsayin ɗaya daga cikin kamfanonin da suka amfana da annobar cutar korona, inda kwastomomi suka riƙa tururuwar shiga shafin suna kashe kusan dala 11,000 duk daƙiƙa ɗaya.

  3. Waɗanda na ƙuntata wa da dokar kulle su gafarce ni – El-rufai

    Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai ya nemi afuwar jama'ar jihar bisa matakan kulle da ya sanya domin daƙile yaɗuwar annobar korona, yana mai cewa "matakan sun zama wajibi ne".

    Wani bidiyo da fadar gwamnatin Kaduna ta wallafa a Twitter ya nuna El-rufai da mai ɗakinsa Aisha Garba El-rufai zaune a kan kujera suna gode wa al'ummar Kaduna da suka bi umarnin zama a gida.

    "A matsayina na gwamnanku, ina neman afuwarku, amma hakan [matakin dokar kulle] ya zama wajibi sai an ɗauka domin daƙile yaɗuwar wannan annoba," in ji El-rufai.

    Gwamnan ya ƙara da cewa a matsayinsa na ganau ba jiyau ba, "wannan cuta ce mai haɗarin gaske wadda za ta iya halaka mutum," sannan kuma hanya guda ɗaya da za a kawo ƙarshenta shi ne "a hana mutane zirga-zirga".

    A nata ɓangaren, uwar gida Aisha gode wa ma'aikatan lafiya ta yi bisa kasancewarsu a kan gaba wurin yaƙi da cutar sannan ta jaddada kira ga mutane da su ci gaba da zama a gida.

    Tun a makon farko da El-rufai ya saka dokar hana fita a Kaduna gwamnati ta kama wasu malamai biyu da laifin karya dokar bayan sun gudanar da sallar Juma'a a masallatansu.

    Hukumar NCDC ta ce mutum 138 ne suka harbu da cutar korona a Jihar Kaduna ya zuwa daren Asabar.

  4. Babu wanda ya kamu da korona a Kano ranar Asabar

    Ma'ikatar lafiya ta Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ba a samu wanda ya harbu da cutar korona ba ranar Asabar a jihar, sai dai biyu daga cikin masu dauke da cutar sun mutu.

    Da ma dai alkaluman da hukumar NCDC ke fitarwa na baya-bayan nan na nuna cewa ana samun raguwar yaɗuwar cutar, hasali ma an sallami ƙarin mutum biyu a ranar Asabar ɗin, abin da ya kawoi jumillar waɗanda aka sallama zuwa 93.

    Jihar Kano ce ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya da yawan masu cutar a yanzu 633.

    Ma'aikatar lafiya a jihar ta ce ya zuwa ƙarfe 11:55 na daren 16 ga watan Mayu, mutum 761 ne jumilla aka tabbatar sun harbu da korona a Kano, sannan 35 sun mutu da kuma 93 da suka warke kuma aka sallame su.

  5. Brazil ta zama ƙasa ta huɗu a yawan masu korona a duniya

    Brazil ta zama ƙasa ta huɗu mafi yawan waɗanda suka harbu da cutar korona a faɗin duniya.

    Alkaluma daga Hukumomi a ƙasar sun nuna an samu mutum 14.000 da suka kamu da cutar a cikin sa'a 24, wanda hakan ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa dubu 250, inda take bin ƙasashen Amurka da Rasha da Birtaniya.

    'Yan Brazil sama dubu 15 ne suka mutu sakamakon annobar.

    Wakiliyar BBC ta ce ƙwararru sun ce da ana gwaji yadda ya kamata da alƙaluman sun ninka hakan sau 15.

    Duk da wannan yanayi da ake ciki a kasar, Shugaba Jair Bolsonaro ya dage kan cewa yana son gwamnonin jihohi su ɗage dokar nesa-nesa da juna - yana mai cewa hakan zai ƙara haifar da rashin aikin yi da talauci.

  6. Barka

    Jama'a barkanku da safiyar Lahadi, da fatan ana ci gaba da hutun ƙarshen mako lafiya - ga waɗanda ba sa cikin zaman daɓaro.

    Umar Mikail ke kasancewa da ku a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da suke faruwa a sassan duniya musamman game da annobar korona.