An saka ranar dawo da tafiye-tafiye a Italiya
Gwamnatin Italiya ta sanya hannu kan wani daftarin doka da zai bai wa 'yan ƙasar damar soma tafiye-tafiye daga ciki da wajenta daga ranar 3 ga watan Yuni, yayin da take ƙoƙarin sassauta matakan kulle kan annobar korona.
Kazalika za ta ba da damar zirga-zirga tsakanin yankuna - wanda a yanzu aka tsaurara haramcinsa - daga dai wannan rana.
Wannan yunƙuri yana da mahimmancin gaske ga ƙasar da ke yunƙurin sake buɗe harkokin kasuwancinta bayan kusan wata biyu komai da komai yana rufe.
Fiye da mutum 31,600 ne suka mutu a Italiya sakamakon annobar korona, ƙasa ta uku kenan bayan Amurka da Birtaniya a yawan waɗanda cutar ta yi ajalinsu.