Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ganduje ya ƙaddamar da rabon takunkumin fuska 'miliyan ɗaya'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya da ma karin wasu labaran daban.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa

    Mun zo karshen bayanan da muke kawo muku na wannan rana.

    Sai ku tare mu ranar Talata domin sanin halin da duniya ke ciki.

    Da fatan za ku duba kasa domin karanata labaran da muka wuni muna kawo muku, ko kuma ku leka safukanmu na sada zumunta don karin bayani da kuma tafka muhawara.

    Mun gode

  2. Masu cutar korona 'suna tserewa a Zamfara'

    Masu cutar korona a jihar Zamfara da ke Najeriya suna tserewa daga cibiyar killace masu dauke da cutar saboda rashin kyawunta.

    Wasu da aka killace a cibiyar sun shaida wa BBC cewa rashin kyawun wurin musaman rashin makewayi ya sa ba sa iya sukuni.

    A cewarsu, da farko an kai su wani wuri a Damba da ke wajen Gusau, babban birnin jihar amma ganin rashin kyawunsa ya sa an dauke su zuwa asibitin kwararru na Ahmed Sani Yariman Bakura.

    Daya daga cikinsu ya ce akwai sakaci na ma'aikatan lafiyar asibiti, yana mai cewa an batar da sakamakon gwajin da aka yi musu na cutar inda aka bukaci su sake mika kansu domin a kara gwada su.

    Sai dai hukumomi sun sa alwashin daukar mataki a kan batun.

  3. Ganduje ya ƙaddamar da rabon takunkumin fuska 'miliyan ɗaya'

    Gwamnan Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin rufe baki da hanci miliyan daya a jihar da zummar dakile cutar korona.

    Gwamna, wanda ya kaddamar da bayar da takunkumin ranar Litinin a Kano, ya ce akwai bukatar mazauna jihar su dauki karin matakai na kula da lafiyarsu a wannan lokaci da cutar korona take ci gaba da addabar duniya.

    Ya ce za a raba makarin fuskar ne a kananan hukumomi takwas da ke kwaryar birnin Kano, yana mai shan alwashin hukunta duk wanda aka kama ba tare da sanya makarin fuskar ba.

    Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa ta dauki mutanen da ta kira 'dakarun tsafta' wadanda za su yi yaki da cutar korona.

    "Daukarku wannan aiki da aka yi, an yi tunanin kwarai da gaske; aka zabo matasa, maza da mata, masu jini a jiki wadanda za su shiga lungu-lungu da kasuwanni...a tabbata cewa an yi safta yadda ya kamata," in ji Gwamna Ganduje.

  4. An kama shugabannin IS a Afghanistan

    Hukumar leken asirin Afghanistan ta ce ta kama shugaban kungiyar Islamic State reshen Kudancin Asia da Gabas Mai Nisa a Kabul, babban birnin kasar.

    An kama Zia ul-Haq, wanda aka fi sani da suna Sheikh Omar Khorasani, tare da wasu shugabannin kungiyar ta IS biyu.

    Taliban ce babbar kungiyar masu tayar da kayar-baya a Afghanistan amma IS tana da karfi a wasu yankuna kuma tana kai hare-haren bama-bamai a Kabul.

    Wakilan BBC sun ce kama manyan jami'an na IS wani babban koma-baya ne ga kungiyar idan ya tabbata.

    Saura shugabannin da aka kama sun hada da kakakin kungiyar Saheeb da jami'in leken asirinta Abu Ali.

  5. Covid-19: Najeriya za ta karɓo ganyen shayin tazargade daga Madagascar

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin karɓo kason Najeriya na ganyen shayin Madacasger da shugaban kasar ya ce yana maganin cutar korona.

    Sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da korona ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani, kamar yadda aka saba kan cutar korona a Najeriya da kuma matakan da gwamnati ke ɗauka.

    Ya ce shugaba Buhari duk da ya amince a karbo maganin na Madagascar, amma ya ce dole sai ya bi tsari na tabbatar da ingancin magunguna.

    Madagascar tuni ta aika wa kasashe da dama na Afirka da maganin kyauta, kuma ta tura zuwa Guinea Bissau. Najeriya ta ce ya kamata ta karɓo nata kason daga Guinea Bissau.

  6. WHO ta yi gargadi kan ɗage dokar kulle

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi ga ƙasashe kan ɗage dokar kulle inda ta ce sai idan an gano bakin zaren daƙile yaɗuwar cutar ya kamata a ɗage dokar.

    Gargaɗin na zuwa bayan ƙara samun yaɗuwar cutar a ƙasashen Ƙoriya ta kudu da Jamus da China bayan sassauta dokar kulle.

    WHO ta shawarci ƙasashe kada su ɗage dokar sai idan za su iya kula da ƙaruwar yawan masu kamuwa da cutar kuma sun yi tanadi na ganowa da killace sabbin waɗanda suka kamu.

    WHO ta kuma fitar da sabbin shawarwari da za a bi kafin bude makarantu da wuraren aiki, tana mai cewa dole a tabbatar da yin nesa nesa da juna.

  7. Ƙarin mutum 33 sun warke daga korona a Legas

    Hukumomin lafiya a Legas sun ce ƙarin mutum 33 sun warke kuma dukkaninsu an sallame su.

    Sanarwar da Ma'aikatar lafiya ta jihar ta fitar a Twitter ta ce maza 24 ne da mata 9 aka sallama daga cibiyar killace masu cutar korona a Onikan da kuma Eti Osa.

    Yanzu adadin mutum 502 suka warke daga cutar korona a jihar Legas.

  8. Putin ya ɗage dokar kulle duk da bazuwar korona

    Shugaba Putin na Rasha ya sanar da ɗage dokar kulle daga ranar Talata, duk da yaduwa da cutar ke ci gaba da yi.

    A jawabinsa ga ƴan kasa ta kafar talabijin, shugaba Putin ya ce za a fara bude fannonin ayyuka da noma da makamashi tare da yin kira ga shugabannin yankuna su sassauta dokar kulle.

    Rasha ta samu ƙaruwar yawan masu cutar korona da sama da mutum dubu goma sha ɗaya a rana ɗaya, inda yanzu ta kasance ta uku a cikin kasashen da cutar ta fi yaduwa.

    Sai dai Rasha ta ce an samu ƙaruwar yawan masu cutar saboda faɗaɗa gwaji da aka yi

  9. Afghanistan ta kama shugaban IS na kudancin Asiya

    Hukumar leƙen asiri ta Afghanistan ta ce ta kama shugaban kungiyar ISIS na yankin kudancin Asiya da gabas mai nisa.

    An kama Zia-ul-Haq, wanda aka fi sani da Umar Khorasani, da wasu manyan ƴan ƙungiyar biyu yayin wani samamen soji a Kabul babban birnin ƙasar.

    Taliban ce ƙungiyar masu ɗauke da makamai mafi girma a Afghanistan, amma IS na da tasiri a wasu yankunan kasar.

    Wakilin BBC ya ce ƙungiyar ta kai hare-haren bama-bamai da dama, abin da ya janyo mutuwar ƴan shi'a marasa rinjaye da wasu mutane da dama.

    Har yanzu ana dakon samun ƙarin bayani kan yadda aka kai samamen.

  10. Gwamnatin Burtaniya na shan suka kan dage dokar kulle

    Gwamnatin Birtaniya na shan suka a kan shirinta na sassauta dokar kullen da ta kafa.

    Jagoran ‘yan adawa na jam'iyyar Labour Keir Starmer, ya ce babu wani karin haske a kan kalaman Firai minista Boris Johnson da ya bukaci jama'a su koma bakin aiki, amma su kaurace wa wuraren hawa motocin haya.

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya Domic Raab, ya shaida wa BBC cewa dole ne a yi takatsantsan wajen janye dokar kullen.

    Ya ce mun ga yadda ta faru a wasu kasashe da suka kafa dokar kulle, daga bisani suka janye ba tare da bin matakan da suka kamata ba, abin da ya janyo sake dawowar cutar.

    Scotlad da Wales ma bakin su yazo daya, kan cewa ya yi wuri a jingine batun zaman gida a yanzu.

  11. Harkoki sun fara dawowa a kasashen Turai

    Miliyoyin jama'a a nahiyar Turai na komawa harkokinsu, yayin da kasashe da dama suka soma sassauta dokar zaman gida da suka kafa don yaki da cutar korona.

    A Faransa, an bude wasu makarantun firamare yayin da dalibai ke shirin komawa a makon nan.

    Harkokin kasuwanci da dama kamar kantuna da shagunan abincin na sake dawowa, ko da yake dumbin ma'aikata na cigaba da aiki daga gida.

    A Spaniya ma al'amura na cigaba da kankama sannu a hankali.

    A kusan rabin kasar, shaguna na budewa mutane na iya taruwa fiye da su goma sannan kuma otal-otal sun soma budewa amma dukka bisa kiyaye sharadin nesa-nesa da juna.

  12. An kashe 'yan fashi 17 a Kaduna

    Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe 'yan fashi 17 a gari uku da ke cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

    A wata sanarwa da John Enenche, mai magana da yawun hidekwatar rundunar da ke Abuja ya fitar ranar Litinin, ya ce an kai harin na ranar Alhamis ne bisa haɗin gwiwar rundunoninta na musamman irin su Gama Aiki da Thunder Strike.

    Samamen ya yi sanadiyyar kashe 'yan fashi 17 a cewar rundunar, sannan wasu suka tsere da raunuka a garuruwan Galbi da Damba da Kabarasha da Gwagwada dukkaninsu a Ƙaramar Hukumar Chikun.

    An lalata gidaje uku "wadanda babu mutane a ciki" da wani ginin coci a Kabarasha yayin farmakin amma ba a samu mutuwa ko rauni ba daga bangaren jama'ar gari, a cewar rundunar.

    Ta ƙara da cewa ta kafa kwamitin bincike kan lamarin tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Kaduna.

  13. An tsare fiye da mutum 2,300 saboda saba dokar kulle a Lagos

    Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, CP Hakeem O. Odumosu, ya shaida wa manema labarairanar Litinin cewa sun kama mutum 2,300 bisa laifuka masu alaka da kullen da jihar ta sa da manufar dakile cutar korona.

    CP Hakeem ya ce tuni suka gurfanar da mutum 2,185 a gaban kuliya inda aka yanke musu hukunci daban-daban.

    Kwamishinan 'yan sandan ya ce sun kuma saki mutum 125 da ake zargi da karya dokoki wadanda suke da kananan shekaru.

    Har wa yau, rundunar 'yan sandan ta jihar Legas ta sha alwashin tabbatar da 'yan jihar sun bi dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya da aka fara ranar 4 ga watan Mayu 2020, inda CP Hakeem ya ce sun dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin mutane ba sa zirga-zirga tsakanin karfe 8:00 zuwa 6:00 na yamma.

    Ya kara da cewa za su sanya kafar wando daya da duk mutumin da aka samu ya karya dokar sanya takunkumi.

  14. Labarai da dumi-dumi, Boris Johnson zai yi taron manema labarai game da sassauta dokar kulle

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi taron manema labarai a yau da karfe 7:00 agogon Najeriya bayan sanar da shirinsa na sassauta dokar kulle a Ingila ranar Lahadi.

    Boris zai amsa tambayoyin jama'a da na 'yan jarida yayin taron.

    Gwamnatin Birtaniya na yunkurin wallafa wani kudin tafiyar da sassaucin dokar mai shafi 50.

  15. Ma'aikatan lafiya 47 ne suka kamu da cutar korona a Kano

    Akalla ma'aikatan lafiya 47 ne a Kano suka kamu da cutar korona kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

    Babban jami'i a kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yaki da cutar korona, Dr Tijjani Hussain ne ya tabbatar da hakan yayin wani jawabi ga manema labarai ranar Lahadi.

    Dr Tijjani ya ce an tabbatar da kamuwar ma'aikatan lafiyar da cutar ne a 'yan makonni da suka gabata, inda ya ce ba a samu karin wani ma'aikacin lafiyar da ya sake kamuwa ba.

    Jihar Kano ce dai jiha ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan adadin masu dauke da cutar korona a Najeriya.

    Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 602, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar.

  16. Rasha ta samu sabbin masu korona ana daf da kawo karshen dokar kulle

    Russia ce yanzu kasa ta uku mafi yawan masu dauke da cutar korona a duniya, inda ta yi Burtaniya da Italiya fintinkau.

    An samu sabbin masu dauke da cutar 11,656 a cikin sa a 24 a kasar, inda yanzu haka kasar ke da masu cutar 221,344.

    Kasar Amurka da Spaniya ne kawai suka sha gaban Russia.

    Har w ayau, kasar ta sake samun wadanda suka mutu sakamakon annobar mutum 94, inda take da adadin mutum 2,009 da suka mutu saboda korona.

    Shugaba Vladimir Putin na shirin yi wa 'yan kasar jawabi bayan yin waiwaye kan dokar kulle a kasar ranar Litinin. A yanzu dai ranar Talata ne dokar kulle a Russia ke zuwa karshe.

  17. Shugaba Ramaphosa ya yi gargadi kan yiwuwar sake barkewar korona

    Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bukaci 'yan kasar da su ci gaba da dabbaka abubuwan da aka umarce su da su a yayin anobar korona kasancewar za su shekara suna dabbaka su.

    Ramaphosa ya ce jama'a su ci gaba da nesa-nesa da juna da sanya takunkumi da kuma wanke hannayensu na dan wani lokaci.

    Shugaban ya kuma yi gargadi cewa "dole rayuwa ta sauya ba kamar yadda muka san ta a baya ba" duk da cewa za a sassauta dokokin kulle.

    Har wa yau, Mista Cyril ya kara jan kunnen 'yan kasar tasa cewa akwia yiwuwar samun karuwar masu dauke da cutar a nan gaba.

    Afirka ta Kudu na da mutum fiye da 10,000 da ke dauke da cutar ta korona.

  18. Kenya ta saki fursunoni 7,000 saboda korona

    Kasar Kenya ta saki fursunoni 7,000 a wani mataki na rage cunkoso a gidajen yarin kasar sakamakon annobar korona.

    Ministan Cikin Gidan kasar, ya shaida wa majalisar dokoki cewa an samu mutum biyu masu dauke da cutar a wani gidan yari da ke birnin Nairobi.

    Tuni dai ma'aikatar lafiyar kasar ta fara aiwatar da yi wa jama'a gwaje-gwaje a gidajen yari da ke fadin kasar.

    Kasa ta Kenya dai na da mutum fiye da 672 masu dauke da cutar korna inda mutum 32 suka rasu.

    Gwamnati ta takaita zirga-zirgar jama'a a ciki da wajen birnin Nairobi da Mumbasa da da kuma wasu karin birane guda biyu da yankin bakin ruwa.

  19. An tsawaita dokar hana taruwar jama'a a Ghana

    Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya tsawaita dokar hana taruwar jama'a har zuwa karshen watan Mayu a dai-dai lokacin da kasar ke ci gaba da samun karuwar masu korona.

    Makarantu na ci gaba da zama akulle haka ma wuraren ibadu da taruka da kuma kan iyakokin kasar.

    Ghana dai na da mutum 4,700 da ke dauke da cutar ta korona inda mutum 22 suka mutu.

    Yayin wani jawabi ta gidan talbijin na kasar, Shugaba Nana Akufor ya sanar da tsawaita dokar a ranar Lahadi.

  20. Cutar korona ta sake bulla birnin Wuhan

    An sake samun wasu mutane masu dauke da cutar korona a birnin Wuhan, birnin da cutar ta fara barkewa a can da lardin Jilin na kasar China.

    Birnin ya samu masu dauke da cutar guda biyar a yau Litinin, bayan tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar ranar Lahadi tun 3 ga watan Afrilu.

    Hukumomi sun ce mutanen guda biyar da ke dauke da cutar dukkansu na gida daya ne.

    Kasar China dai na ci gaba da sassauta dokar dokokin kulle a 'yan makonnin da suka gabata kuma ana samun raguwar masu dauke da cutar.

    Sai dai masana harkar lafiya na jan hankali cewa da zarar an saki mutane sakaka akwia yiwuwar samun sabbin masu dauke da cutar a karo na biyu