Jihohin arewa hudu da ke kan gaba a yawan masu cutar korona
Duk da cewa cutar korona ta soma bulla ne a jihohin da ke kudancin Najeriya kafin ta shiga arewacin kasar, amma dai a yanzu jihohin arewa su ne ke kara samun yawaitar masu dauke da cutar idan ka cire jihar Legas.
Cikin 'yan kwanaki kadan, masu cutar korona jihohi hudu da ke arewa suna da mutum fiye da dubu daya da aka tabbatar su na fama da cutar covid-19.
Jihohin su ne Kano da Bauchi da Borno da kuma Katsina.
Izuwa ranar Asabar da daddare - akwai masu cutar korona 576 a jihar Kano, sai kuma 161 a jihar Bauchi, da wasu 159 a jihar Borno sai kuma jihar Katsina mai mutum 156.
A bisa jerin jadawalin masu cutar a fadin Najeriya, jihar Kano ce ta biyu a yayin da jihar Legas ne kadai ke gabanta.