Rufewa
Masu bibiyarmu a nan muka kawo karshen wannan shirin na kawo muku bayanai kai tsaye a yau. Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu. Mun gode. A kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya game da cutar korona da ma wasu labarai da suka shafi rayuwarku.
Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Masu bibiyarmu a nan muka kawo karshen wannan shirin na kawo muku bayanai kai tsaye a yau. Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu. Mun gode. A kwana lafiya.
Hukumar Kostom a Najeriya ta kare matsayinta a game da shinkafar da aka tura jihar Oyo a kwanakin baya.
Gwamnatin jihar Oyo tace shinkafar da gwamnatin tarayya ta umarci hukumar kwastom ta tura ma ta bata da kyau. To sai dai hukumar yaki da fasa kwauri tace babu gaskiya a cikin wannan zargi.
Kwantirolan hukumar na shiyyar tashar jiragen ruwa ta Apapa ya shaida wa BBC cewa zargin ba gaskiya ba ne domin shugabannin jihar da kansu suka duba kayan kafin su dauka.
“Me ya sa bas u ce ba ta da kyau ba sai yanzu.”
Ya kuma kara da cewa ko da gwamnatin ta mayar musu da shinkafar kamar yadda suka fad aba za su karba ba.
Ya kara da cewa “me ya sa sai bayan kwana hudu sannan su ce za su dawo mana da ita. Ba za mu karba.”
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kadamar da wani tsari na sayar da takunkumin rufe fuska milyan goma a farashi mai rahusa.
A kasuwa dai ana sayar da takunkumin rufe fuskar ne kan dala sittin na sefa, amma kuma gwamnatin za ta sayar da shi ne a kan sefa dala ashirin ga ‘yan kasar.
Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne domin ci gaba da yaki da cutar korona a fadin kasar baki daya.
Jamhuriyar Nijer dai tana da mutum 770 masu dauke da cutar korona, inda mutum 38 suka mutu.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta aike da wasu jami’an ta na kar ta kwana domin kaiwa gwamnatin kano dauki na yakar cutar korona virus a jahar.
A wata sanarwa da hukumar ta lafiya ta fitar ta ce ta yanke wannan shawara daukar wannan matakin ne dan ganin an inganta yaki da cutar korona a Kano.
Wannan mataki dai na hukumar lafiya ta duniya na zuwa ne dai a dai-dai lokaicn da ma’aikatar lafiya dake jahar ta bayar da sanarwar mutuwar mutum biyar da ke dauke da cutar ta korona virus,sannan adadin wadan da suka kamu da cutar ya kai sama da dari hudu.
WHO din dai ta yi gargadin cewa mutum 190,000 zasu rasa rayukansu a nahiyar Afrika sanadin cutar korona muddin ba a kara kaimi wajen daukar matakan dakile bazuwar cutar ba.
Hukumar ta ce adadin wadanda zasu kamu da cutar ya fi yawan asibitocin da ake da su a a nahiyar Afrika bakidaya.
Rahotanni daga Amurka na cewa an yi wa shugaba Donald Trump gwajin cutar korona.
Matakin ya biyo bayan gano wani jami'in soja da ke taimaka masa ya kamu da ita.
Sakamakon gwajin da aka yi wa Mr Trump din ya nuna cewa ba ya dauke da cutar.
Wani mai magana da yawunsa ya ce yana cikin koshin lafiya, kana gwajin da aka yi wa mataimakinsa ma ya nuna ba ya dauke da korona.
Mun san kun sha ji ana fadar alamomin cutar korona, amma kun taba jin su a jikinku? Wadanne ne suke nuna kamar mun kamu da cutar?
Latsa hoton da ke ƙasa domin kallon abin da Abdulbaki Jari ya tattaro game da alamun.
Babu tabbacin ko za a kyale 'yan kallo su shiga filayen wasanni idan an ci gaba da gasar Bundesliga ta Jamus nan gaba a wannan watan, amma wata kungiya ta kudiri aniyar hakan.
Borussia Monchengladbach ta umarci magoya bayanta da su kawo hotunansu manya-manya domin a saka a kan kujerun zamansu na filin wasan.
Zuwa yanzu hoto 4,500 aka ajiye da kuma wasu 12,000 da ke jira a saka nasu - har da wasu magoya bayan da ba sa kusa a cikin masu aiko da hotunan.
Magoya bayan suna biyan yuro 19 (kusan naira 3,700) domin buga hotonsu a filin wasan kuma za a yi ayyukan agaji ne da kudin.
Ranar Asabar 16 ga watan nan za a ci gaba da Bundesliga amma ba tare da 'yan kallo ba.
Babbar kotun Senegal ta hana a mayar da wasu gawarwakin 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje, wadanda cutar korona ta kashe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Gwamnatin kasar da ke yammacin Afirika ce ta yanke hukuncin kada a mayar mata da mutanen, saboda kauce wa yaduwar cutar.
Sai dai makusantan mamatan sun nemi juya wa hukuncin baya, suna cewa hakan shiga 'yancinsu ne na addini, in ji AFP.
Kasar da mafi yawan mutanenta Musulmai ne, na da masu dauke da korona 1,500 kuma tuni 13 suka mutu.
Tawagar Gwamnatin Tarayyara Najeriya da aka tura domin bincika mace-macen da aka samu a Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar ta ce ba ta samu wata hujja da ke tabbatar da ƙaruwar mutuwa a jihar ba.
Shugaban tawagar, Dr Mahmoud ya ce mutum 92 ne suka mutu cikin kwana takwas, abin da ya ce hakan ba baƙon abu ba ne.
An tura likitocin biyar ne zuwa garin Hadeja bayan samun rahotannin ƙaruwa a yawan mutanen da suka rasu a 'yan kwanakin nan.
Sai dai tawagar ba ta ƙaryata ikirarin ko mace-macen na da alaƙa da cutar korona ba.
A gefe guda kuma, shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya reshen Jigawa, Dr Nura Basirka ya ce suna zargin ma'aikatan lafiya 16 sun kamu da cutar a Asibitin Kwararru na Rasheed Shekoni da ke jihar.
Ba kasaafai ake gudanar da gwaji kan gawar mutane ba a jihohin arewacin Najeriya saboda dalilai na addini - kasancewar Musulunci ya tanadi a binne wanda ya rasu ba tare da bata lokaci ba.
Ya zuwa daren Laraba, mutum 39 ne suka harbu da cutar korona a Jihar Jigawa, a cewar alkaluman hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya.
Masu taimaka wa Gwamnan Jihar Legas guda 10 sun kamu da cutar korona.
Kwamishinan lafiyar jihar ne ya tabbatar da hakan.
Mutanen guda 10 yanzu haka suna samun kulawa ta musamman a cibiyar killace masu dauke da cutar korona.
Hakan ya biyo gudanar da gwaji da aka yi ga dukkanin ma’aikatan gidan gwamnatin jihar.
Jihar Legas ce ke kan gaba a yawan masu dauke da cutar korona a Najeriya, inda take da mutum 1,308 - kaso daya cikin uku na yawan masu cutar a Najeriya.
Mutane 13 ne suka mutu yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti a jihar Andhra Paradesh da ke Indiya, sakamakon shakar iskar gas da suka yi, wadda ta fito daga wata cibiyar samar da sinadarai.
Tuni aka sallami wasu daga cikin su, yayin da wasu kuma ke cikin mawuyacin hali.
An rika kwashe mutanen daga gidajensu da ke makwabtaka da cibiyar a tsakar dare, bayan da suka rika yanke jiki suna faduwa.
Sinadarin da ya tsiyaya wani nau'in gas ne da ake kira styrene, mai dan ruwa ruwa haka, da ka iya sanya mutum tashin zuciya da jiri, da kuma matsanancin bugun zuciya.
Kamfanin wanda na wasu yan Koriya ta Kudu ne, ya ba da sanarwar shawo kan lamarin tare da alkawarin gudanar da bincike don gano yadda hakan ya faru.
Asusun ba da lamuni na duniya ya amince zai bai wa Uganda aron kudi $491m, domin taimaka wa tattalin arzikin kasar wajen fama da cutar korona.
Cibiyar ba da lamuni ta duniya ta ce raunin da tattalin arzikin kasar ke fuskanta saboda korona ya janyo gagarumin koma baya ga kudaden shiga da kuma yadda gwamnatin kasar ke kashe kudadenta.
Cibiyar da ke Washington ta ce kudin za su taimaka wajen samar da cibiyoyin lafiya da kuma farfado da tattalin arzikin kasar, kuma za su iya sanya wasu kasashen duniyar kara ba ta wani taimakon.
Bankin Lamunin ya gano yadda tattalin arzikin kasar Uganda ke cikin matsala saboda wannan annoba, da kuma yadda manyan hanyoyin shigar kudin kasar kamar wuraren yawon bude ido da harkokin zirga-zirga da gine-gine da masana'antu da kuma bangaren noma ke fuskantar hadari.
Yayin da Bankin ya rage kudin ruwan da yake karba daga harkokin kasuwanci, ita kuma gwamnatin Kampala na kara daukar wasu hanyoyin taimaka wa kamfanoni a kasar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya, INEC ta tura motoci domin tallafa wa Jihar Sokoto a yakin da take yi da annobar korona.
Hukumar ta wallafa hotunan jerin motocin a shafinta na Twitter, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ofishin kwamitin yaki da cutar da ke jihar.
Jihar Sokoto ta tabbatar da mutum 85 da suka harbu da cutar korona da kuma takwas da suka mutu, sai kuma mutum biyu da suka warke.
Gwamnatin Najeriya ta ce an samu sauyi game da lokaci da kuma jirgin da zai kwashe 'yan Najeriya daga New Jersey ta Amurka zuwa gida.
Ma'aikatar yada labarai ta kasar ta ce za a yi aikin ne ranar Asabar, 9 ga watan Mayu sabanin 10 ga wata da ta sanar tun farko, sannan wadanda suka riga suka sayi tikiti a jirgin Ethiopian Airlines ET 509 za a mayar da su jirgin ET 8509.
Mutum 270 za a diba a wannan karon sannan jirgin zai tashi ne da karfe 7:15 agogon Amurka daga filin jirgin Newark Liberty International Airport NJ.
Ma'aikatar ta umarci 'yan Najeriya mazauna Amurka da su hanzarta sayen tikitinsu a shafin kamfanin Ethiopian Airlines tare da tura mata da kwafinsa hadi da adireshi da lambar wayar wakilansu a Najeriya.
'Yan Najeriya a kasashen waje sun yi ta kiran a kawo musu agaji bisa halin kadaici da suka tsinci kansu ciki, yayin da kasashen ke cikin dokar kulle domin dakile yaduwar cutar korona.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin biyan kudin shigo da kayayyakin aikin lafiya zuwa Najeriya tare da harajinsu na tsawon wata shida.
Sanarwar da fadar shugaban ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce kayayyakin na cikin jerin wadanda hukumar hana fasa kwauri ta duniya ta bayar da shawarar a saya kuma umarnin zai fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Mayu.
Sai dai an cire abubuwan da ake iya kerawa a Najeriya daga cikin wadanda za a yi safararsu zuwa cikin kasar, a cewar Ministan Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed.
"Kayan da ake iya kerawa a cikin gida kamar kyallaye da takunkumin fuska da sinadarin peroxide da sirinji - mai allura ko maras allura, an cire su daga jerin abubuwan," in ji ta.
A ranar Talata kungiyar likitoci ta Najeriya reshen Jihar Kanota tabbatar wa BBC da mutuwar likita daya a jihar, yayin da 34 da sauran ma'aikatan lafiyasuka kamu da cutar ta korona.
Ma'aikatan lafiya kusan 100 ne suka harbu da cutar korona a Najeriya sannan kuma kungiyoyinsu sun yi ta kokawa game da rashin isassun kayan aikin gwaji da ma na kula da masu dauke da cutar.
Gasar Bundesliga ta Jamus za ta ci gaba ba tare da 'yan kallo ba a ranar Asabar 16 ga watan Mayu - ita ce gasar lig ta farko a Nahiyar Turai da za ta ci gaba tun bayan saka dokar kulle.
Daya daga cikin manyan wasannin da za a buga a ranar farko har da wasan hamayya tsakanin Schalke 04 da Borussia Dortmund.
Bayern Munich mai rike da kofin wadda kuma ke ta daya a saman teburi da maki hudu, za ta ziyarci Union Berlin a ranar Lahadi.
Akasarin kungiyoyin na da wasa tara kafin kammala gasar, yayin da ake sa ran kammala ta a 27-28 ga watan Yuni.
Gwamnatin Kenya ta ce za ta fara daukar nauyin wadanda aka killace sakamakon zarginsu da harbuwa da cutar korona.
Ta yi wannan yunkurin ne domin karfafa wa mutane gwiwar fitowa fili domin a yi musu gwajin cutar, yayin da mutanen suke jin tsoron yin gwajin saboda kada a same su da ita.
Tun barkewar cutar, mutane da yawa sun makale a cibiyoyin killacewar duk da cewa lokacin da ya kamata su bari ya yi amma saboda ba za su iya biyan kudin da aka kashe wurin kula da su ba.
Akasarin cibiyoyin gwamnati da ake killace wadanda ake zargin sun kamu da cutar suna cajar akalla dala 20 (fiye da naira 7,000) a kowace rana.
Hakan ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a 'yan makonnin nan, inda wasu suka rika barazanar dirowa ta taga daga dogayen gine-ginen cibiyoyin.
Har yanzu akwai karancin fitowar mutane domin yin gwajin a unguwannin marasa karfi na birnin Nairobi da Mombasa - yankunan da cutar ta fi yin kamari.
Kusan Amurkawa miliyan 3.2 ne suka bayyana kansu a matsayin marasa aikin yi a makon da ya gabata kadai.
Wannan ya sa adadin ya kai miliyan 33 tun daga tsakiyar watan Maris, lokacin da cutar korona ta tilasta saka dokokin kulle a kasar.
Sai dai rahoton Sashen Ayyukan Yi na makon nan ya yi kasa da na makon da ya gabata, wanda ya zarta miliyan 3.8.
Adadin yana raguwa a 'yan makonnin nan, sai dai wani mai sharhi ya ce har yanzu yana da yawa ko da kuwa an kwatanta shi da rikicin tattalin arziki na shekarar 2008.
A ranar Juma'a za a bayyana alkaluman watan Afrilu.
Shugaban Bankin St Louis US Federal Reserve, James Bullard, ya fada wa gidan talabijin na CNBC cewa rahoton "zai zama mafi muni a tarihin Amurka".
Shahararriyar mawakiyar nan ta Amurka, Madonna, ta ce ta yi fama da cutar korona lokacin da ta yi tafiya wasu kasashen duniya.
A sakon da ta wallafa ranar Laraba a Instagram, ta ce ta harbu da cutar ne lokacin da ta yi balaguro na kasashen duniya mai suna Madame X.
Sai dai ta ce yanzu haka lafiyarta kalau amma dai gwajin da aka yi mata a baya ya nuna cewa tana da garkuwar jikin ta Covid-19.
"Idan gwaji ya gano cewa kana garkuwar jikin ta hakan yana nufin ka taba KAMUWA da cutar kuma na yi fama da rashin lafiya a kusan karshen balaguron da na yi zuwa Paris mako bakwai da suka wuce tare da sauran 'yan rakiya ta amma a lokacin mun yi tsammani mura ce mai zafi ta kama mu," in ji sakon da mawakiyar ta wallafa a Instagram, tana mai karawa da cewa yanzu dukkansu sun samu sauki kuma lafiyar lau.
Madonna ta katse balaguron da take yi bayan gwamnatin Faransa ta haramta gudanar da dukkan tarukan jama'a.
Mawakiyar, mai shekara 61, ta bayar da tallafin $1m domin samar da riga-kafin cutar korona.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta da na rundunar hadin gwiwar kasashe ta MNJTF sun kashe 'yan kungiyar ISWAP 48 a wani hari da suka kai ta sama kan sansanin kungiyar da ke Dumba ranar Talata.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Alhamis, hedikwatar sojojin da ke Abuja babban birnin Najeriya ta ce sauran dakarun da suka kai harin sun hada da rundunar sojojin sama da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole.
Sai dai rundunar ba ta bayyana ko an kashe wasu daga cikin dakarunta ba ko kuma sun ji rauni yayin harin da aka kai a kusa da Tafkin Chadi.
Kazalika ta ce ta kai harin ne bisa rahotannin sirri da ta samu cewa 'yan kungiyar sun taru da niyyar kai hare-hare a makwabtan garuruwa, inda nan take jiragenta suka kai kai musu hari kuma suka ɗaiɗaita su.
Har wa yau, rundunar ta ce ta bi sahun dakarun kungiyar da suka kai wa sojojinta hari a kusa da garin Diffa na Nijar sannan ta kashe da dama daga cikinsu a wani matsuguninsu da aka yi wa lakabi da Location Charlie.