Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Zulum, ya tsawaita dokar kullen da aka sanya a jihar.
A jawabin da ya yi wa mazauna jihar ranar Laraba da maraince, Gwamna Zulum, ya ce an tsawaita dokar kullen ne da mako daya.
Ya ce tun da farko an sanya dokar ne domin dakile yaduwar cutar korona, yana mai cewa ko da yake matakin ba shi da dadi amma ya zama wajibi.
"Ina tsawaita dokar kulle da mako daya amma za a sassauta dokar gobe Alhamis, 7 ga wata da Juma'a, 8 ga wata da kuma Litinin, 11 ga watan Mayu, 2020 inda za a fito daga karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma domin mutane su samu damar yin harkokin kasuwanci da bude kasuwanni yadda iyalai za su samu damar sayen abinci," in ji Gwamna Zulum.
Ya kara da cewa za su yi nazari kan matakin ranar 31 ga watan Mayu sannan kwamitin da ke aiki don dakile yaduwar cutar korona zai sanar da sabbin matakai na gaba.
Mutum 106 ne suka kamu da cutar korona a jihar ta Borno ya zuwa ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2020.