Cutar korona ka iya ajalin Amurkawa 100,000 - Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargadin cewa akwia yiwuwar samun mutum 100,000 da za su mutu sakamakon cutar korona.
Mista Trump ya fadi hakan ne a lokacin da yake wani jawabi inda ya kuma musanta cewa gwamnatinsa na jan kafa wajen yakar cutar.
Fiye da mutum 67,000 ne dai cutar korona ta yi ajali a Amurka.
To saidai Mista Trump ya bayyana irin karfin gwiwar da yake da hsi dangane da samun rigakafin cutar a cikin watanni 12 ko 18.