Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ma'aikatan lafiya 14 sun kamu da cutar korona a Katsina

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Awwal Ahmad Janyau and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa

    A nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku na yau a wannan shafi. Ku kasance tare da mu ranar Talata domin samu sabbin labarai. Amma kuna iya duba kasa don karanta kabaran da muka wallafa, sannan ku duba karin labarai a babban shafinmu na bbchausa.com da ma shafukanmu na sada zumunta.

  2. Ma'aikatan lafiya 14 sun kamu da cutar korona a Katsina

    Akalla ma'akatan lafiya 14 ne suka kamu da cutar korona a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

    Jaridar ThisDay, wacce ta ambato gwamnan jihar Aminu Bello Masari yana tabbatar da hakan a hirar da ya yi da manema labarai ranar Litinin, ta kara da cewa ma'aikatan sun harbu da cutar ne lokacin kula da masu dauke da korona.

    Ya kara da cewa 10 daga cikinsu ma'akatan Federal Medical Centre, Katsina ne, yayin da hudu kuma ma'aikatan asibitoci masu zaman kansu ne.

    Gwamna Masari ya ce an samu karin mutum 37 da suka kamu da cutar korona a jihar, inda jumulla ake da mutum 75 da suka harbu da cutar a jihar.

  3. Kasashen duniya za su tara $8bn don samo riga-kafin cutar korona

    Kasashen duniya sun sha alwashin bayar da tallafin fiye da $8bn domin taimakawa wajen samar da riga-kafin cutar korona da ma gudanar da bincike kan maganin cutar.

    Kasashe 40 da kuma kungiyoyin bayar da tallafi sun gudanar da taro ta hanyar intane wannan kungiyar tarayyar turai ta gudanar.

    Shugabar Hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce kudin zai zama wata hanya ta samun hadin kan duniya a yunkurin fatattakar kungiyar.

    Ta ce hakan ya nuna cewa da gaske duniya tana mutunta darajar dan adam, ko da yake ta yi gargadin cewa akwai bukatar karin daukar matakai nan da kwanaki masu zuwa.

  4. Coronavirus: Yadda na sha fama da cutar - Muhammad Atiku Abubakar

    Muhammad Atiku, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Atiku Abubakar, ya bayyana wa BBC halin da ya shiga lokacin da kamu da cutar korona.

  5. Tururi ba ya maganin cutar korona

    Masana a harkar lafiya sun ce ba gaskiya ba ne tururin ruwan zafi zai iya maganin cutar korona kamar yadda shugaban Tanzania ya yi ikirari.

    Shugaban kasar ya nemi mutane da su rika shakar tururin ruwan zafi domin idan ya shiga jiki da zafi zai iya kashe kwayar cutar korona.

    Masana na gargadin cewa shakar tutuin zai iya yin lahani ga huhu.

    Ga bayanin dan jarida mai nsa ido a kan coronavirus Abdulbaki jari.

  6. Sojojin Najeriya 'sun kashe mayakan Boko Haram 134'

    Rundunar tsaron Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan Boko Haram 134 a farmakin da ta kai musu a arewa maso gabashin kasar.

    A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar ta kara da cewa ta kama manyan masu bai wa kungiyar Boko Haram bayanai 16.

    Ta ce mayakan na Boko Haram sun taru ne a wani wuri da bisa kuskure suka yi tsammani tudun-mun-tsira ne inda dakarun sojin sama suka yi musu ruwan wuta kuma suka yi musu ta'adi mai yawa.

    "A daya daa cikin wadannan hare-hare na atilari da aka kaddamar tsakanin raar 1 zuwa 2 ga watan Mayu, dakarun KANTANA JIMLAN, sun lalata motocin da ake haba bindigogi 7 na Boko Haram sannan suka kashe mayakan Boko Haram 78, a cewar rundunar.

    Ta kara da cewa dakarunta sun kashe karin 'yan Boko Haram 56 a yankin Damboa.

    "Kamar yadda bayanan sirrinmu suka nuna, kadan ne daga cikin 'yan ta'addar suka tsere daga wurin da raunuka, kuma da wahala su rayu. A wani labari mai kama da wannan, 16 daga cikin masu bai wa Boko Haram bayanai sun fada tarkon dakarunmu ciki mako biyu da suka wuce," a cewar sanarwar.

  7. An dakatar da shugabar dakin gwajin cutar korona daga aiki

    An dakatar da daraktar dakin gwajin cutar korona daga aiki a Tanzania har sai an kammala bincike a kansa.

    An dakatar da daraktar ce kwana guda bayan shugaban kasar John Magufuli ya bayyana shakku kan kayan aikin da dakin gwajin yake amfani da su wajen gwada masu cutar korona.

    A jawabin da ya gabatar kai-tsaye daga garinsu Chato da ke arewa maso yammacin Tanzania jiya, Mr Magufuli ya bayyana cewa cikin sirri ya bayar da umarnin yin gwaji kan samfur na dabbobi, kuma dakin gwaji ya bayar da sakamakon gwajin inda ya nuna na mutane ne har ma da shekarunsu.

    A cewarsa, sakamakon da dakin binciken ya fitar ya nuna cewa wasu daga cikinsu suna dauke da cutar korona yayin da wasu kuma ba sa dauke da ita.

  8. An naɗa sabon Shehun Bama

    Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya naɗa sabon Shehun Bama tare da sharaɗin cewa dole ya koma Bama cikin mutanensa maimakon Maiduguri.

    Sanarwar da kakakin gwamnatin Borno Isa Gusau ya fitar ta ce Umar Ibn Shehu Kyari Ibn Umar Elkanemi babban ɗan Shehun da ya rasu a makon da ya gabata aka naɗa a matsayin sabon Shehun Bama.

    Sakataren gwamnatin jiha Alh. Usman Jidda Shuwa ne ya gabatar da takardar naɗin ga sabon sarkin a madadin gwamna.

    Kuma ya shaida ma sa cewa, “gwamna ya umurci ka zauna a Bama, don kasancewa tare da jama’a, rawar da za ka taka matsayinka na jagora na da matukar muhimmanci ga kafuwar shugabanci a Bama.”

    Sakataren gwamnan ya ce an zaɓe shi ne bisa shawarwarin masu nada sarki a masarautar Bama.

    A ranar 27 ga Afrilun 2020 Allah Ya yi wa Shehun Bama Kyari Ibn Umar Elkanemi rasuwa.

  9. Ma'aikatan jinya a Kenya sun yi barazanar shiga yajin aiki

    Kenyan nurses have threatened to strike over a coronavirus risk allowance.

    Ma'aikatan jinya a Kenya sun yi barazanar zuwa yajin aiki kan kudaden alawus na kasadar da suke wajen aikin annobar korona.

    shugaban ma'aikatan sun ba gwamnati da wa'adin mako biyu, inda suka yi gargadin cewa za su dauki matakai idan ba a cimma bukatunsu ba.

    Wasu daga cikin bukatun da shugabannin ma'aikatan ke son gwamnati ta yi la'akari da su sun hada da daukar mambobin kungiyar aiki na dindin da kuma karin ci gaba ga ma'aikatan.

    Peterson Wachira shugaban kungiyar KUCO ya shaida wa BBC cewa mutum bakwai daga cikin mambobinsu sun kamu da cutr korona.

  10. An maido wa Najeriya dala miliyan 311 na Abacha

    Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya ce gwamnati ta karbi sama da dala miliyan 311 daga Amurka daga cikin kudaden da ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Sani Abacha ya sace.

    A wata sanarwa da maitaimaka masa kan yada labarai Dakta Umar Jibril Gwandu ya fitar ranar Litinin, ya ce kudin ruwa ya sa kudaden sun karu daga dala miliyan $308 zuwa dala miliyan $311 daga watan Fabrairun 2020 da aka ajiye su a babban bankin Najeriya zuwa 28 ga Afrilu.

    Sanarwar ta ce tun 2014 gwamnatin Najeriya ta fara bin matakai na dawo da kudaden da ake kira “Abacha III.”

    Malami ya ce za a yi amfani da kudaden wajen kammala ayyuka a sassan Najeriya da suka hada da hanyar Legas zuwa Ibadan da hanyar Abuja zuwa Kano da kuma gadar Niger.

    Ana dai zargin marigayi Sani Abacha da sace kimanin dala biliyan 5 a lokacin mulkinsa daga shekarar 1993 zuwa 1998 lokacin da ya rasu.

    Tun a shekarar 1999, aka soma batun kudaden da ake zargin Janar Abacha ya sace kuma hukumomi a Switzerland sun dawo wa gwamnatin Najeriya da wasu daga cikin kudaden.

  11. Madagascar za ta fara gwajin maganin korona da ganyen tazargade

    Shugaban Madagascar ya sanar da cewa kasarsa za ta fara gwajin maganin rigakafi da ruwan ganyen tazargade domin warkar da cutar korona.

    Andry Rajoelina ya ce a mako mai zuwa za a fara gwajin.

    Ya bukaci al'ummar kasar su shuka itacen tazargade.

    Shugaba Rajoelina ya ce yana tattaunawa da masana kimiya a Amurka domin taimakawa wajen binciken.

    Shugaban kuma ya ce yana kokarin tabbatar da maganin daga Hukumar Lafiya ta Duniya.

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, cikin wata sanarwa da ta aike wa BBC ta ce ba ta bada shawarar wani ya yi gaban kasan ya sha magani a matsayin maganin cutar korona.

    Tuni aka tura ruwan maganin zuwa wasu kashen Afirka da suka hada da Guinea-Bissau da Equatorial Guinea yayin da shugaban Tanzania John Magufuli ya ce zai aika da jirgi zuwa Madagascar domin karbar maganin

    Har yanzu dai ba a gano maganin cutar korona ba

  12. Kotun ƙolin Amurka za ta saurari shari'a ta waya

    Annobar korona ta tilasta wa kotun ƙolin Amurka rungumar sabbin sauye sauye.

    Tsawon mako biyu masu zuwa, kotun ƙolin za ta saurari bahasi ta wayar salula a karon farko a tarihi.

    Za a watsa sautin bahasin kai-tsaye ta intanet.

    Lauyoyi za su gabatar da bayani daga gida - ko da yake lauyoyin gwamnati za su yi aiki ne daga ofishin babban lauyan gwamnati.

    Kuma kamar yadda aka saba za su sanya kayan aikin lauya a lokacin sauraren shari'a.

    Ana sa ran gudanar shari'o'i da dama, ciki har da batun zargin badaƙalar kuɗi da ake yi wa shugaba Trump.

  13. Walwala ta dawo a Italiya

    Ƴan Italiya miliyan huɗu da rabi sun koma aiki tun kafa dokar kulle a kasar wata biyu da suka gabata.

    A Milan, inda cutar ta fi yaɗuwa, mutane da dama ne suka yi dandazo a tashar jirgin ƙasa,amma akwai ƙarancin mutane a motocin sufuri.

    Wasu ƴan kasar sun fita a wuraren shaƙatawa da aka buɗe. An kuma ba mutane damar ziyartar ƴan uwa amma ba zuwa wurin abokanai ba.

    Sai dai Firaminista Giuseppe Conte ya buƙaci al’ummar ƙasar su kiyaye matakan kariya kada ƙasar ta sake komawa gidan jiya.

    Mutum kusan 29,000 cutar korona ta kashe a Italiya, ƙasa ta biyu da cutar ta fi yi wa illa bayan Amurka.

  14. Ana taron samar da rigakafin cutar korona

    Shugabannin kasashen duniya sun fara aiki tare a yau, domin ganin sun tattara biliyoyin kudi don neman rigakafi da kuma maganin cutar korona.

    Shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der layn ce za ta jagoranci wannan yunkuri na samar da kudaden, wadda ta ce manufar ita ce samar da maganin cutar da kowa zai iya siya kuma ya isa zuwa kowanne sako na fadin duniya.

    Burtaniya da Japan da Saudiyya da wasu kasashen na cikin wadanda za su ba da wannan tallafin, wanda ake yunkurin tara sama da dala biliyan takwas.

  15. Dangote ya bayar da gudunmowar cibiyar gwaji ta tafi-da-gidanka

    Gidauniyar Dangote ta samar da wata cibiyar gwajin cutar corona ta tafi-da-gidanka a jihar Kano wadda za ta iya yi wa mutune har 400 gwaji a rana.

    A jiya Lahadi dai ne aka mika wannan cibiyar da sauran kayayyakin ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a asibitin Muhammadu Buhari da ke Giginyu bayan kaddamar da ita.

    Wannan kari ne kan wurin killace masu dauke da cutar korona mai gado 600 da mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka ya bai wa jihar tasa.

    To yayin da ake ci gaba da samun mace-mace da wasu ke alakantawa da cutar korona a Jihar Kanon, ayarin da shugaban kasa ya tura don yin bincike da kuma kai wa jihar dauki ya ce har yanzu yana kan tantance bayanan da yake tattarawa kan mace-macen.

  16. Kaso 40 na 'yan Najeriya matalauta ne - NBS

    Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce kaso 40 na 'yan kasar na fama da talauci.

    Kamfanin dillancin Labarai na Reuters ya rawaito cewa hukumar wadda ta wallafa alkaluman a ranar Litinin ta ce alkaluman talauci da ta tattara daga watan Satumbar 2018 zuwa Oktoba 2019 sun nuna 'yan kasar na zama ne kasa da naira 137,430 a shekara.

    Hakan dai na nufin a cikin mutum 10 mutum hudu matalauta ne.

    Alkaluman dai ba su kunshi yanayin da al'ummar jihar Bornon suke ciki ba, jihar da rikicin Boko Haram ya daidaita.

  17. Coronavirus:An sallami wadanda suka halarci jana'izar Abba Kyari

    Hukumomin lafiya a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja sun sallami dukkanin mutanen da aka killace bayan hallartar jana'izar shugaban ma'aikata a fadar Shugaban kasar marigayi Abba Kyari wanda ya rasu sakamakon cutar Corana.

    Wata sanarwa, da sakataren lafiya na hukumar birnin Dr. Muhammad Kawu ya fitar ta ce hakan ya biyo bayan da kammala kwanakki 14 a killace ba tare da nuna alamun cutar ba.

    Makonni biyu kenan da yi wa marigayi Abba Kyari jana'iza inda aka ga wasu mahalarta jana'izar suna cire kayan kariya da suka sanya suna wurgarwa, a cikin wani bidiyo da ya yi yawo a kafafen sada zumunta.

  18. Gwamnatin jihar Nassarawa ta fara mayar da almajirai jihohinsu na asali

    Gwamnatin jihar Nasarawa ta bi sahun wasu jihohin arewacin Najeriya wajen mayar da almajirai jihohinsu na asali a wani mataki na dakile yaduwar cutar korona.

    Almajiran kimanin 800 ne jahar ta tasa keyarsu zuwa jihohinsu a jiya Lahadi wadanda ta ce sune kashin farko na dubban almajiran da za ta mayar.

    A cewar mai magana da yawun gwamnan jihar Malam Yakubu Lamai a bisa wani bincike da gwamnati ta gudanar akwai almajirai fiye da dubu ashirin a jihar.

    A baya-bayan nan ne dai gwamnatin jihar Kano ta mayar da daruruwan almajirai zuwa jihohinsu na asali.

    To sai dai gwamnan jihar Kaduna ya ce fiye da 30 daga cikin almajiran da jihar Kanon ta mayar musu na dauke da cutar korona.

  19. Kasashe da dama a nahiyar Afrika sun fara sassuata dokar hana fita da suka kakaba a kokarinsu na shawo kan annobar korona a nahiyar.

    Akwai akalla mutum dubu 45 da aka tabbatar suna dauke da cutar a nahiyar.

    An sake bude manyan Katina da kasuwanni a Abuja da Legas na wasu ‘yan sa’o’ia kallum, yayin da mahukunta a Najeriya ke kokarin takaita illar wannan annoba a kasar.

    A Ruwanda an sanya dokar hana zirga-zirga da daddare, amma wasu wuraren kasuwancin kamarsu Otel da wuraren cin abinci za su kasance a bude.

    Hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun ce adadin masu dauke da cutar a gidan yarin soji da ke Kinshasa ya ninka ya zuwa yanzu.

  20. Shin ko akwai shaidar kirkirar kwayar cutar korona daga dakin gwaji?

    A jiya ne Dr Maria Van Kerkhove, ta kwamitin na musamman na yaki da cutar korona a Hukumar Lafiya ta Duniya, ta shaida wa BBC cewa shaida ta nuna kwayar cutar korona ba mutum ne ya kirkire ta ba, cuta ce daga Allah.

    Ana dai ta rade-radi da zargin cewa an sako annobar ne daga wani dakin gwaji da ke birnin Wuhan a kasar China.

    Tuni dai kasar ta China ta sha musanta zarge-zargen.

    Yayin wani jawabi ga manema labarai , Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce akwai gamsassun shaidu da ke nuna an sako cutar ne daga wani dakin gwaji a birnin Wuhan.

    Wani rubutu a mujallar Washington Post da aka yi watan da ya gabata shi ma ya bayyana cewa ofishin jakadancin Amurka na nuna damuwa a kan daya daga cikin dakunan gwaji na birnin na Wuhan.

    Sai dai jaridar ta amince cewa babu wata kwakkwarar shaidar da ke nuna an saki cutar korona ne daga dakin gwajin.