An kori masu sharar a filin jirgin sama na Kenya an barsu kara zube
Wani bidiyon masu shara a filin jirgin sama na Kenya da ake zargin an kore su daga aiki ranar Talata ya janyo cece-kuce a intanet.
Ma'aikatan sun ce sun je aiki a ranar da daddare a filin jirgi na Jomo Kenyatta da ke Nairobi babban birnin kasar, amma sa'o'i hudu bayan nan an umarce su da su ba da katin shaidarsu na tsaro kafin a koresu daga cikin ginin filin jirgin.
Babu wani karin bayani da aka yi musu game da korar ta su, an umarce su ne kawai da su tafi gida.
Yayin da ake fama da dokar hana fita, wadda aka sanya domin yaki da cutar korona a kasar, sun zauna tsahon dare cikin sanyi a wajen.
Masu sharar wadanda suka ce kamfanin share-share na Colnet ne ya dauke su aiki, sun nemi gwamnati ta shiga wannan batu.
BBC ta nemi jin ta bakin kamfanin na Colnet sai dai ya ce zai fitar da sanarwa kan batun anjima a yau.
A cikin bidiyon da aka sa a Tiwita daya daga cikin masu sharar na bayanin yadda ba ta iya samun kula da yaranta.