Karshen rahotannin kenan a wannan shafi
Jama'a karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu hadu gobe idan Allah ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye da 206,000 suka mutu.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Jama'a karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu hadu gobe idan Allah ya kai mu.
Gwamnatin jihar Legas ta ce gawarwaki da ke jibge a dakunan ajiye gawarwaki sun taru sosai sakamakon dokar hana fita da aka saka da zummar dakile annobar cutar korona a jihar.
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga duk wadanda suka san akwai gawarwakin ‘yan uwansu da su dauke su domin yi musu jana’iza.
Gwamnan ya kara da cewa 'yan uwan mamatan za su iya fita domin yin jana'iza idan har za su bi dokokin bayar da tazara da kuma guje wa taron mutanen da ba su wuce 20 ba.
An ceto wata 'yar Najeriya da aka sanya hotonta a shafin Facebook cewa ana neman mai sayenta a kasar Lebanon, kwanaki kalilan bayan hukumomin kasar ta Lebanon sun kama wani mutum da ake zargi da yunkurin sayar da matar.
Tallan matar ya janyo korafe-korafe da dama a shafukan intanet a Najeriya.
Hukumomin Najeriya sun ce ga alama dokar kulle da gwamnatin Lebanon ta kafa domin yaki da cutar korona ta saukaka gano matar da kuma mutumin da ake zargi da shirin sayar da ita.
Asusun bayar da lamuni na International Monetary Fund (IMF) ya amince da da bai wa Najeriya tallafin gaggawa na dala biliyan 3.4 domin yaki da annobar korona.
Shugabar asusun Kristalina Georgieva ta ce wannan shi ne adadi mafi yawa da suka bai wa wata kasa a matsayin tallafin yaki da cutar korona.
A wata sanarwa da IMF ta wallafa a shafinta na intanet, an sahale wa Najeriya tallafin ne a karkashin shirin gaggwa na tallafa wa yaki da annobar korona mai suna Rapid Financing Instrument (RFI).
Wannan tallafi na zuwa ne bayan Majalisar Dattawan Najeriya ta amince wa Shugaba Muhammadu Buhari ya karbo rancen kudi naira biliyan 850.
Majalisar ta amince da bukatar ne a zaman da ta yi ranar Talata bayan ta dawo daga hutun cutar korona.
Shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta amince da bukatarsa ta samun rancen daga kasuwar kudi ta cikin gida domin bai wa gwamnatinsa damar aiwatar da kasafin kudin 2020.
Gwamnan Jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya ya ce jihar ta sallami mutum biyu da suka harbu da cutar korona.
Jumillar adadin wadanda suka kamu da cutar a Jihar Delta shida ne ya zuwa karfe 12:39 na ranar 28 ga watan Afrilu, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya.
Gwamna Ifeanyi Arthur Okowa ya ja hankalin mazauna jihar da su ci gaba da bin umarnin gwamnati domin yaki da cutar.
Adadin wadanda suka kamu da cutar korona a Saudiyya ya zarta 20,000 a ranar Talata bayan an samu mutum 1,266 da suka kamu da cutar, a cewar rahoton jaridar Saudi Gazette.
Wasu mutum takwas sun mutu a cikin sa'a 24 ta gabata, abin da ya sa jumillarsu ya zama 152.
Kashi 23% na sabbin wadanda suka kamun 'yan Saudiyya ne kamar yadda kamfaninin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito mai magana da yawun ma'aikatar lafiya Dr. Muhammad Al-Abdel Ali yana bayyanawa.
Ya ce yanzu haka akwai mutum 17,141 da ke dauke da cutar.
Ba za a kammala gasar Faransa ta Lique 1 da 2 ta bana ba, bayan da gwamnati ta dakatar da dukkan wasanni har da wanda babu 'yan kallo har karshen Satumba.
Firai Minista, Edouard Philippe ya ce dukkan wasannin kakar 2019-20 an soke su, bayan da yake sanar da shirin da Faransa ke yi na janye dokar hana fita daga 11 ga watan Mayu.
Mahukuntan kwallon kafar Faransa sun so a ci gaba da gasar Faransa ranar 17 ga watan Yuni a kuma karkare ranar 25 ga watan Yuli.
Mai ba da shawara kan harkokin lafiya ga fadar mulkin Amurka ta White House, Dr Anthony Fauci, ya ce yana da yakinin cewa cutar Korona za ta sake dawowa nan gaba a wannan shekara.
Da yake jawabi ga kungiyar masana tattalin arziki ta Washington, Dr Fauci ya yi gargadin cewa Amurka na iya fuskantar mummunan yanayi game da cutar a lokacin kaka da kuma hunturu matsawar ba a aiwatar da matakan kariya da aka amince da su ba.
Ya ce cutar korona za ta ci gaba da kasancewa a duniya ba tare da ta je ko'ina ba, a don haka ya rage ga kasashe su yi abin da ya dace.
Amurka ce dai kasar da ta fi fama da cutar a duniya inda mutum miliyan 1,002,498 suka kamu, yayin da fiye da 56,000 suka mutu.
Hukumar Birnin Tarayya Najeriya, Abuja (FCTA) ta ce har yanzu umarnin rufe makarantu yana nan daram a birnin "har sai baba ta gani", ba kamar yadda wasu masu makarantu ke yadawa ba.
Hukumar ta ce ta samu bayani game da wasu rahotanni da wasu shugabannin makarantu masu zaman kansu a birnin ke shaida wa iyayen yara cewa za a ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2019/2020.
"Sakatariyar Ilimi tana kara jaddadawa cewa umarnin rufe makarantu da aka bayar tiun farkon annobar korona cewa ya yi 'sai baba ta gani', abin da yake nufin babu wasu ayyukan karatu har sai an bayar da umarnin yin hakan," a cewar FCTA.
A sanarwar da hukumar ta fitar a yau Talata ta ce za a bayar da cikakken tsarin yadda za a hade karashen zango na biyu cikin na uku.
"Saba wa wannan umarni zai iya kawo rikici a tsarin zangon karatu na biyu, wanda zai iya hadewa da na uku," in ji hukumar.
'Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun dawo bakin aiki a yau Talata bayan hutun mako biyar da suka yi.
Kuma daga gani za ku fahimci cewa al'amura sun sauya - kowanne dan majalisa sanye da takunkumin rufe fuska.
Ga kuma tazara da suka bai wa juna.
Mahaifin Farfesa Abdallah Uba Adamu, wanda shi ne Shugaban Jami'ar karatu daga gida ta National Open University of Nigeria, ya rasu a garin Kano.
Dr Uba Adamu ya rasu ne a ranar Litinin bayan wata gajeriyar rashin lafiya - yana da shekara 85.
Mataimaki na musamman ga Farfesa Abdallah, Abdurrahman Abdullahi ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar tasa.
An yi jana'izarsa ranar Talata a gidansa da ke Unguwar Nassarawa GRA.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kira Shugaba Buhari na Najeriya a yau Talata domin tattaunawa kan yaki da annobar korona.
Mai taimaka wa Shugaba Buhari a kan kafafen sada zumunta Tolu Ugunlesi ne ya bayyana hakan, inda ya ce Trump ya yi alwashin tallafa wa Najeirya.
Annobar na ci gaba da daidaita tattalin arzikin kasashen duniya, abin da ya sa kasashe mataluta ke neman tallafi ruwa a jallo domin ganin bayan cutar.
Ko a jiya Litinin sai da biloniyan dan kasuwar China Jack Ma ya aike wa da Nahiyar Afirka tallafin kayan yaki da cutar da suka hada na'urar ventilator 300 da takunkumin rufe fuska dubu 500 da kayan kare kai 2,000.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta ceto mutum 15 da aka yi garkuwa da su da kuma gano matatun man fetur na bayan fage a Jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Rundunar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Talata, inda ta ce dakarunta sun kama mutum uku tare da kwace makamansu uku.
Sannan an gano matatun mai 48 wadanda suke aiki ba bisa kai'ida ba.
Kazalika an gano tankin karkashin kasa na ajiyar man fetur guda 28 da kuma kananan jiragen ruwa 18.
Firaministan Faransa Édouard Philippe ya ce dokar kulle da gwamnatinsa ta saka a kasar ta taimaka wurin ceton ran mutum 62,000 a cikin wata guda.
Mista Philippe ya bayyana hakan ne yayin da yake zayyana shirin gwamnati na sassauta dokar nan da 11 ga watan Mayu. Nan gaba majalisar dokokin kasar za ta jefa kuri'a a kan shirin.
Kusan mutum 23,300 ne suka mutu sakamakon cutar korona a Faransa, yayin da aka tabbatar dubu 165,842 sun kamu da ita.
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta yi sakaci ba wurin neman shawarar 'yan majalisa a matakin da take dauka na dakile yaduwar annobar korona.
Femi Gbajabiamila ya yi wannan kira ne a yayin da yake jagorantar zaman majalisar a yau Talata bayan komawa hutu da suka yi, inda ya kara da cewa hakan zai kawo cikas ne kawai a ci gaban kasa.
"Idan tallafin gwamnatin tarayya bai isa ga wadanda suka dace ba, mu ne na farko da ake kawo wa kuka kuma dole ne mu yi musu bayanin dalilan da ya sa ba su cancanci tallafin ba ko kuma abin da ya sa aka share su," in ji Femi Gbajabiamila.
"Wajibi ne gwamnati ta guje wa fadawa kuskure ta hanyar mantuwa a irin wannan yanayi domin kuwa hakan zai kawo tsaiko ne wurin aiwatar da abin da aka sa a gaba da ke da matukar mahimmanci ga ci gaban kasarmu."
Kakakin majalisar ya kuma yi kira ga gwamnatin Buhari da ta yi amfani da bayanai daga 'yan majalisar domin raba kayan tallafin rage radadin matakan dakile annobar korona.
Kazalika ya ce suna fatan yin kudirin doka kan shirin tallafin gwamnatin tarayya na National Social Investments Programmes a zamansu na gaba sannan su amince da bukatar da Buhari ya aike musu game da shirin tallafi karo na biyu domin jama'a su amfana.
Hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce za a dawo da yin gwajin cutar korona a asibitin Malam Aminu Kano bayan rufe dakin gwajin.
Shugaban hukumar NCDC Dr Chikwe Ihekwaeazu wanda ya fitar da sanarwar a Twitter ya ce a gobe Laraba za a bude cibiyar gwaji ta biyu a Jami'ar Bayero da ke Kano.
Wasu bayanai dai sun ce an dakatar da gwajin ne a Kano saboda rashin kayan aiki na yin gwajin gano masu dauke da cutar korona.
An dauki kwanaki kusan hdu, hukumar NCDC ba ta fitar da bayana ba kan cutar korona a Kano, duk da yawan mace-macen da aka samu a jihar da ake alakantawa da cutar korona.
Tawagar kwararrun likitoci sun shiga jihar Kano da ke arewacin Najeriya domin taimakawa jihar kan halin da take ciki.
A cikin mako guda mutane da dama ne suka mutu a kusan dukkanin unguwannin birnin Kano.
Dakta Sani Gwarzo ya shaida wa BBC cewa kwararrun likitoci da dama ne suka shiga Kano domin taimakawa jihar wajen shawo kan matsalolin da jihar ke fuskanta da kuma dakile yaduwar cutar korona.
Ya ce a yanzu haka suna kewayawa a wuraren da aka yi tanadi domin killace masu fama da cutar korona da kuma cibiyar gwaji da sauran wuraren kula da lafiya.
Wani dan majalisar wakilai daga Kano ya shaidawa BBC cewa, wasu karin likitocin suna hanyar shiga Kano, kuma mafi yawancinsu 'yan asalin jihar Kano ne.
Wannan na zuwa bayan a jawanbinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai aika da tawaga domin gudanar da bincike.
Shugaban ya kuma sanar da rufe jihar na tsawon mako biyu domin dakile yaduwar korona.
Archbishop a birnin Douala na Kamaru ya musanta rahotannin da ke cewa ya samar da maganin cutar korona amma ya ce "ya dade yana bincike."
A makon da ya gabata ne kafofin yada labarai a Kamaru suka ce Samuel Kleda yana bayar da maganin cutar korona kyauta na wani "ganyen bishiya da ya ce ya sani"
Archbishop Kleda ya shaida wa kafar talabijin ta Equinox a Kamaru cewa "la'akari da alamomin cutar korona daga mutanen da suka kamu, na yi amfani da wani ganyen itace ga wasu masu dauke da cutar kuma kuma sun samu sauki."
Sai dai ya yi gargadin cewa bai ce ya "samar da maganin cutar korona ba. ban fadi haka ba." in ji shi.
Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin kaucewa yin gaban kai na shan wani maganin da ba a tabbatar da ingancinsa ba.
Baya ga Afirka ta kudu, kasar Kamaru ce ke da yawan masu dauke da cutar korona a kasashen da ke kudu da sahara inda mutum 1,705 ke dauke da cutar, yayin da 58 suka mutu.
Gwamnatin Nasarawa ta tabbatar da bullar cutar korona a jihar.
Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya ce wata matashiya ce ke dauke da cutar wacce ta fito daga Kano a makon da ya gabata duk da matakan hana fita da gwamnatin ta dauka.
Ya ce an killace matar a asibitin killace masu korona ta Dalhatu Araf a Lafia inda ta ke karbar magani.
Sannan gwamnan ya ce an killace 'yan uwanta bayan gwaji ya tabbatar da tana daukeda korona inda aka dauki samfurinsu zuwa Abuja domin gwaji.
Hukumar da ke kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cutar korona za ta haifar da karuwar juna biyu da ba a yi shiri ba.
Hukumar ta yi hasashen cewa idan har aka yi wata shida cikin dokar hana fita, kusan mata miliyan 47 a kasashe masu karamin karfi ba za su samu kai wa ga hanyoyin da suka saba ba na matakan hana daukar ciki.
Hukumar ta ce a za a iya samun juna biyu sama da miliyan bakwai saboda kulle da al’ummar duniya suke ciki.
Ta kuma yi gargadi kan karuwar rikici tsakanin ma’aurata da za a iya samu sama da milian 30 a tsawon wannan lokaci.