Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Wasu mutum 10 sun warke daga cutar korona a Jihar Legas

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye 167,000 suka mutu.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Covid-19: 'Jami'an tsaron Rwanda suna yi wa mutane fyade'

      • Marubuci, Mary Harper
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Edita a Afrika, BBC World Service

    Kungiyar kare hakkin dan adam ta zargi jami'an tsaron Rwanda da laifin kisa, da fyade da kuma kama mutane tun lokacin da aka kakaba dokar hana fita.

    Kungiyar Human Rights Watch ta ce an harbe akalla mutum biyu a kudancin lardin Nyanza.

    Ta kara da cewa an kulle mutanen da ake zargi da karyar dokar hana fitan a filayen wasa, sannan wasu mutane sanye da kakin soji sun yi wa mata fyade.

    Kazalika an kulle 'yan jaridar da suka bayar da labaran zargin yi wa matan fyade.

    Rundunar sojin Rwanda ta ce ta soma bincike kan zarge-zargen, kuma ta kulle mutum biyar da ake zargi da hannu a zarge-zargen.

  2. Coronavirus: Za a tilasta wa masu dauke da cutar zuwa wurin kallace su a Abuja

    Hukumar Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ta ce za ta tilasta wa masu dauke da cutar korona, wadanda suka yi ki zuwa cibiyar killace masu cutar tafiya cibiyar.

    "Bayan samun labari daga wurin kwamitin yaki da cutar covid-19 cewa mutanen da ke dauke da cutar sun gwammace su zauna a gida a kula da lafiyarsu maimakon kai su cibiyar killace masu dauke da cutar, ministan Abuja ya nuna rashin jin dadinsa.Ya ce za a yi amfani da dka wurin tilasta musu tafiya cibiyar kula da masu dauke da cutar," in ji wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma'a.

    Sanarwar ta kara da cewa ci gaba da zaman mutanen a gidajensu ka iya zama barazana ga kiwon lafiyar iyalansu.

  3. Maganin cutar korona na farko ya gaza samar da waraka

    Wani magani da aka yi gwajinsa da ake tasammanin zai zama maganin cutar korona, ya samu nakasu.

    An yi ta fatan maganin na Remdesivir zai zama mafita ga cutar korona.

    To amma wani gwaji da aka yi a kasar China ya nuna maganin ya gaza cimma manufa kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.

    Maganin bai hana kwayar cutar zagaye a cikin jinin mai dauke da cutar ba, in ji WHO.

    Kamfanin Gilead Sciences na Amurka wanda yake goyon bayan maganin ya ce hukumar Lafiya ta Duniya ta sauya ma'anar maganin.

  4. An tura tawaga ta musamman domin tunkarar cutar korona a Kano

    Cibiyar da ke hana bazuwar cutuka a Najeriya, NCDC ta aike da wata tawagar kwararru 17 zuwa birnin Kano domin taimaka wa jihar yaki da cutar korona.

    Bakwai daga cikin 'yan tawagar sun fito daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

    Babban jami'i a Kwamiti na Musamman kan annobar korona na Najeriya, Dr Aliyu Isah ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da BBC.

    Wannan dai na zuwa kwanaki biyu bayan da cibiyar da ke yin gwajin cutar korona a Kano ta ce ta rufe sakamakon rashin kayan aiki.

    Sai dai Dr Aliyu Isa ya ce sun aike wa dacibiyar kayan aiki, illa dai harbuwa da cutar korona da jami'an masu yin gwajin suka yi ne da kuma yi wa dakin gwajin feshi ne dalilan da suka sa aka dage yin gwaje-gwajen.

    Sakamakon dakatar da gwaje-gwajen a birnin na Kano, ya sa kwana biyu a jere hukumar NCDC da ma'aikatar lafiyar jihar ta Kano ba su fitar da alkaluman masu dauke da cutar ta korona daga jihar ba.

    Tuni dai gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nemi daukin gwamnatin tarayya, inda ya ce al'amarin ya fi karfi gwamnatin jiha.

    Gwamnatin Tarayyar dai ta bai wa jihar Legas tallafin kudi har naira bilyan 10.

  5. An sassauta dokar hana fita a Egypt saboda Ramadan

    Firai Ministan Egypt, Mostafa Madbouly ya sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga da daddare saboda watan Ramadan.

    Badbouly ya ce yanzu dokar za ta rinka farawa ne da karfe 9 na dare ba kamar yadda take a baya ba, inda take farawa da karfe 8 na dare.

    Hakan na nufin za a kyale masu saye-da sayarwa musamman gidajen cin abinci domin bai wa jama'a damar buda baki.

    To sai dai har yanzu ba a yarda a rinka yin sallar jam'i ba, inda aka rurrufe masallatai. Har wa yau, an haramta haduwar jama'a.

    Yanzu dai kasar ta Egypt na da masu dauke da cutar korona 3,893 inda 287 suka rasu.

  6. An caccaki Trump kan yi wa masu korona allura da maganin wanke datti

    Masana harkar magunguna sun caccaki shugaba Trump na Amurka, bayan ya nemi a rinka yi wa masu korona allura da ruwan maganin wanke datti.

    Har wa yau, wani likita ya yi watsi da shawarar da mista Trump ya bayar ta amfani da haske wajen warkar da masu dauke da cutar.

    An dai ce ruwan maganin wanke datti ka iya zama guba ga jikin dan adam.

    Masanan sun ce yin amfani da ruwan maganin a wajen jikin dan adam ma illa ne idanu da fata da ma hanyoyin numfashi.

  7. Coronavirus: Za a wajabta sanya takunkumin fuska a Afirka ta Kudu

    Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce daga wata mai zuwa kasar za ta soma sassauta dokar hana fita na mako biyar da ta sanya.

    A wani jawabi da ya gabatar ta talabiji, Mista Ramaphosa ya ce daga karshen watan Afirilu, za a koma da wasu hada-hadar tattalin arziki, sai dai za a yi hakan ne cikin yanayi na takatsantsan.

    Iyakokin kasar za su kasance a rufe ga masu shiga daga ketare, sannan za a iya safarar muhimman kayayakin amfani tsakanin yankunan kasar.

    Mista Ramaphosa ya kuma kara da cewa dole kowanne dan kasa ya yi amfani da takunkumin fuska idan zai fito daga gidansa.

    Sannan ya ce za su soma gwaji ga kowa nan gaba a wani mataki na dakile annobar.

    Mutum dubu 4 suka kamu da cutar a kasar, inda 75 suka mutu

  8. Coronavirus: Indonesia za ta rufe iyakokinta

    Indonesia za ta rufe filayen jiragen sama da haramta tashin jiragen na wucin-gadi domin hana mutane shiga ko fita daga kasar.

    Dokar za ta soma aiki ne daga yau Juma'a har zuwa karshen watan Yuni.

    Kazalika za a takaita zirga-zirga ta iyakokin kasa da na sama da ruwa da jiragen kasa.

    Sai dai dokar ba za ta shafi manyan jami'ai ba, bakin gwamnati ko kungiyoyin kasa da kasa sannan jirgin dakon kaya zai cigaba da aiki.

    Wannan na zuwa ne kwanaki bayanShugaba Joko Widodo ya sanar da cewa kasar ba za ta gudanar da al'adar nan ta Mudik ba, wadda mutane ke tururuwar komawa garuruwansu a karshen watan Azumin Ramadan.

  9. Coronavirus: Hargitsi ya kunno kai a Venezuela kan dokar kulle

    An samu hargitsi a Venezuela bayan mutane sun karya dokar killace kai a jihohin kasar da dama, yayin wata zanga-zanga kan rashin abinci da karancin man fetur da aka gudanar.

    An kashe mutum guda da jikkata wasu shida a arangama da 'yan sanda a jihar Bolivar, bayan daruruwan mutane sun fasa wani kanti tare da wawushe kayan da ke ciki.

    A sauran jihohi da dama, direbobi sun yi zanga-zangar karancin man fetur.

    Hukumar lafiya ta WHO ta bayyana Veneznuela a matsayin kasar da ke fuskantar gagarumin hadari a lokaci wannan annoba, yayin da ta shiga shekara ta shida tana fama da matsalolin hauhawar farashi da koma bayan tattalin arziki

  10. Wani bincike ya nuna zafin rana na kashe kwayar cutar korona

    Wani sabon bincike da gwamnati Trump ke yadawa ya ce yana ganin hasken rana zai iya taimakawa wajen maganin Coronavirus.

    Shugaban kimiya a ma'aikatar da ke kula da harkokin ciki gida, Bill Bryan, ya shaida wa maneman labarai a Fadar White House cewa zafin rana na rage wa cutar tasiri a jikin dan Adam.

    Ya ce yayin da yanayin zafi ke karuwa da huci ko babu hasken ranar cutar na mutuwa a cikin gaggawa sama da yadda ake tunani.

    Sai dai har yanzu wannan bincike ba a bayyana shi karara ga al'umma ba ko danganta shi da misalai ba.

    Mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya ce bincike zai taimaka wa Amurka wajen tunkarar annobar a lokacin bazara.

  11. Coronavirus: An samu mai cutar na farko a jihar Plateau

    Wata sanarwa da gwamnatin jihar Plateau da ke arewa maso tsakiyar Najeriya ta fitar, ta nuna cewa jihar ta samu mai cutar korona na farko.

    Sanarwar wadda aka fitar a shafin Twitter, ta nemi 'yan jihar da su kwantar da hankalinsu kasancewar suna daukar matakin da ya kamata wajen ganin cutar ba ta bazu ba.

    ALkaluman da hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa an samu mutum na farko daga jihar ta Plateau.

    A daren Juma'a ne dai dokar kulle da jihar ta sa ta kawo karshe, amma kuma gwamna Lalong ya ce za a dan sarara har zuwa ranar Litinin 27 ga watan Afrilu inda dokar kullen za ta fara babu kakkautawa.

  12. Coronavirus: Yadda musulmi suka fara azumin Ramadan a sassan duniya

  13. Coronavirus: An umarci masu azumi su ci abinci mai yawan lokacin sahur da buda baki

    Milyoyin al'ummar Musulmi a sassan duniya sun soma azumin watan Ramadan, wanda a bana ya riske musulmi cikin wani yanayi na annoba.

    Azumi wajibi ne ga duk wani musulmi baligi mai cikakken lafiya inda ake kame baki daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

    Sai dai likitoci sun ce azumi mai tsayi na rage karfin garkuwar jiki don haka sun shawarci mutane su ci abinci da kyau da shan ruwa mai yawa a lokutan buda baki da sahur.

    Sannan marasa lafiya, ko wadanda suka harbu da annobar korona kar su dauki azumin.

    Kasashen Musulmi da dama sun rufe masallatai, yayin da wasu suka dan sassauta dokar hana fita saboda watan Ramadana.

  14. Budewa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yaya muka ji da darurar annobar korona? Allah ya ba mu wucewa lafiya. Yaya kuma azumin Ramadana ga wadanda suke yi? Allah ya karba. Da fatan yau ma za ku ci gaba da kasancewa da shafin bbchausa.com domin kawo muku labarai da bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a sassan duniya. Mun gode.