Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Wasu mutum 10 sun warke daga cutar korona a Jihar Legas

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, inda mutum fiye da milyan biyu da dubu dari shida suka kamu sannan fiye 167,000 suka mutu.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Rahotanni a wannan shafin sun zo karshe

    Jama'a mun kawo karshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.

    Umar Mikail ke cewa mu hadu gobe idan Allah ya kai mu.

    Da fatan za mu kwana lafiya.

  2. Faransa ta haramta sayar da abubuwa masu sinadarin nicotine a intanet

    Hukumomi a Faransa sun haramta sayar da abubuwa masu dauke da sinadarin Nicotine saboda masu siya su boye, bayan wani bincike ya ce sinadarin zai iya kare mutane daga kamuwa daga cutar korona.

    Wannan hani ya hadar da cingan din da ke dauke da Nicotine, wanda ake yi domin hana mutane shaye-shaye.

    Wannan mataki na zuwa ne bayan wani bincike da wani asibiti a birnin Paris ya yi ya nuna mafi yawan masu shan sigari ba su fiya kwanciya a asibiti ba saboda korona.

    Yanzu asibitin na son ya rika amfani da robar da ake likawa a hannu mai dauke da sinadarin a shagunan sayar da magani a matsayin gwaji.

    Amma masu bincike na kara jaddada cewa shan sigari "na da mummunan hadari ga lafiyar dan Adam".

  3. Wasu mutum 10 sun warke daga cutar korona a Legas

    Gwamnatin Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta sallami wasu mutum 10 da ta ce sun yi jinyar cutar korona a cibiyoyin killace masu cutar uku na jihar.

    Ma'aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar da hakan a yammacin Juma'a, inda ta ce gwaji har sau biyu ya nuna ba sa dauke da cutar.

    Ta kara da cewa uku daga cikinsu mata ne sannan wasu uku 'yan kasashen waje ne - Indiya da Philippines.

    Jumillar wadanda aka tabbatar sun warke daga cutar a jihar yanzu sun zama 117, a cewar ma'aikatar lafiyar.

    Ta ce ya zuwa tsakar ranar Juma'a, mutum 455 ne suke dauke da cutar a yanzu sannan wasu 18 sun mutu.

  4. Cutar korona ta kashe tagwaye a Birtaniya

    Wasu 'yan biyu a Burtaniya sun mutu kwana uku a tsakani bayan gwaji ya nuna suna dauke da cutar korona, kamar yadda 'yar uwarsu ta bayyana.

    Katy Davis mai shekara 37 ta mutu ranar Talata a babban asibitin birnin Southampton. Sai 'yar uwar tagwaitakarta Emma wadda tsohuwar ma'aikaciyar jinya ce, ta mutu da safiyar Juma'a, in ji 'yar uwarsu Zoe.

    "Suna yawan cewa yadda suka zo duniya tare haka za su koma tare," In ji Zoe.

  5. An sha ruwa ido ya bude...

    Musulmai da dama a fadin duniya sun sha ruwa a ranar farko ta azumin watan Ramadana.

    Abin tambayar shi ne, yaya aka kai azumin - ganin yadda aka yi shi a cikin dokar zaman dabaro?

    "Wannan azumin daban ne da ragowar (wadanda aka yi a baya), saboda haka dole ne a samu sauyin abubuwa" a cewar Dr Umar Bawa, malami a sashen koyar da addinin Musulunci a Jami'ar Bayero ta Kano.

  6. Mu tsare kanmu da kuma al'umma daga korona – Rahama Sadau

    Tauraruwar fina-finan Hausa na Kannywood, Rahama Sadau ta shawarci 'yan Najeriya da "mu tsare kanmu da kuma al'umma" baki daya daga cutar korona ta hanyar wanke hannu da sabulu na akalla dakika 20.

    Sadau ta bayyana ne a wani bidiyo da hukumar NCDC ta shirya domin wayar da kan al'umma kan hadarin cutar da kuma yadda za su kare kansu.

    Tauraruwar ta ce ta san jama'a sun tsorata da bullar cutar "saboda karancin bayani na yadda za mu killace kanmu," kodayake akwai hanyoyi da dama na kare kai daga cutar.

    "Ku sani wanke hannu yana da matukar mahimmanci domin kuwa kashi 80% na yadda ake kamuwa da cutar (korona) daga musabaha ne," in ji Rahama.

    "A wanke hannu da ruwa da sabulu akalla na dakika 20."

    Taurarin fina-finai da na barkwanci da mawaka duk sun sha kiraye-kirayen wayar da kai a kasashen duniya game da cutar, wadda ta halaka sama da mutum dubu 290 a duniya kuma fiye da miliyan biyu da dubu 700 suka kamu.

  7. An soke gasar kwallon Holland kuma babu zakara

    An soke gasar kwallon kafa ta kasar Holland ba tare da fayyace kungiyar da ta lashe gasar ba.

    Sannan kuma babu kungiyoyi da za su nitse kasa.

    Matakin ya biyo bayan hukuncin gwamnati na haramta duk wani gagarumin buki saboda cutar Korona har sai zuwa 1 ga watan Satumba.

    Hukumar da ke kula da gasar ta kasar Holland ta ce babu yadda za a yi a kammala gasa a kakar 2019 zuwa 2020.

  8. Cutar korona cikin dakika 60

    A ci gaba da kawo muku yadda take wakana game da cutar korona cikin dakika 60 tare da Abdulbaki Jari, a yau mun duba ikirarin da Shugaban Amurka Trump ya yi.

    Trump ya ce za a iya yi wa mutum allura da maganin kashe kwayoyin cuta da zummar maganin korona.

    Ku latsa hoton da ke sama ku ji ko gaskiya shugaban yake fada.

  9. Jihar Rivers ta yi wa 'yan gidan yari 62 afuwa saboda korona

    Alkalin Alkalai na Jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, Mai Shari'a Adama Iyayi Lamikanra ya sallami mace daya da maza 61 daga gidan yari domin rage cunkoso a gidajen yarin jihar saboda annobar korona.

    Daga cikin wadanda aka sallama din akwai 46 da aka yanke wa hukunci da kuma 16 da ke jiran shari'a a gidajen yarin Fatakwal, babban birnin jihar, da Degema da Ahoada.

    Yayin da yake yi musu afuwar, Mai Shari'a Lamikamra ya umarce su da su kasance masu bin doka kuma su guje wa sake aikata laifin da zai sa su koma bursin.

    Jihar mai arzikin man fetur na da mutum uku ya zuwa yanzu da suka kamu da cutar ta korona, yayin da aka sallami mutum daya.

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta fara yin irin wannan afuwa ga 'yan gidan yarin tun a watan Maris a yunkurinta na takaita yaduwar cutar, wadda aka tabbatar ta harbi mutum 981 ya zuwa daren ranar Alhamis.

    Mutum 31 daga cikinsu sun mutu, yayin da aka sallami 197 bayan sun warke, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a kasar.

  10. Trump: 'Wasa nake game da allurar maganin wanke datti'

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce maganar da ya yi ta cewa maganin kashe kwayoyin cutuka wato disinfectants zai yi maganin cutar korona "ba'a ce yake yi".

    Yayin wani taron saka hannu kan tallafin annobar korona a ranar Juma'a, Trump ya ce "yana tsokanar 'yan jarida ne kawai don ya ga mai zai faru".

    Amma ya kara da cewa goga maganin a hannu "zai yi tasiri sosai".

  11. Mutum dubu 50 cutar korona ta kashe a Amurka zuwa yanzu

    Yawan wadanda cutar korona ta kashe ya haura 50,000 a Amurka kamar yadda bayanai daga Jami'ar Johns Hopkins suka nuna.

    Cikin sa'a 24 da suka gabata kawai mutum 3,000 ne suka mutu, sannan zuwa yanzu mutum 870,000 ne suka kamu da cutar.

    Sai dai har yanzu kasashen Turai sun fi Amurka yawan wadanda suka rasa rayukansu bisa ga alkaluman baya-bayan nan, kamar yadda hukumomi suka hakikance.

    Wannan mummunan labari na zuwa ne yayin da wasu jihohi ke kokarin bude harkokin kasuwanci bayan dokar hana fita da aka saka.

  12. An bude cibiyar gwajin korona ta zamani a Jihar Ogun

    Gwamnatin Jihar Ogun da ke kudancin Najeriya ta kafa cibiyar gwajin cutar korona wadda ba sai ma'aikatan lafiya sun hadu da wanda za su gwada ba domin bai wa ma'akatan kariya daga harbuwa da cutar.

    Gwamnan Jihar Dr. Dapo Abiodun ne ya bayyana kafa cibiyar irinta ta farko a Najeriya, wadda mutum zai matsa jikin gilashi kuma ma'aikacin lafiya ya dauki samfurin jikinsa ba tare da sun hadu da juna ba.

    Gwamnan ya ce an yi haka ne kacokam domin kara bai wa ma'aikatan lafiya kariya, kuma tuni mutane da dama suka bayar da samfurin nasu domin gwajin, a cewarsa.

    "Mataimakiyata Noimot Salako-Oyedele da kuma Kwamishinar Lafiya Dr. Tomi Coker ne suka jagoranci bude cibiyar sannan kuma kwararru za su yi aikin yin feshi," kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  13. Abin da ke faruwa zuwa yanzu...

    Ga wadanda suka shigo shafin namu yanzu, ga abubuwan da suka faru na baya-bayan nan:

    • Cibiyar da ke hana bazuwar cutuka a Najeriya, NCDC ta aike da wata tawagar kwararru 17 zuwa birnin Kano domin taimaka wa jihar yaki da cutar korona. Bakwai daga cikin 'yan tawagar sun fito daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.
    • Saudiyya ta bayar da rahoton samun mutum 1,172 da suka harbu da cutar korona a cikin awa 24 da ta gabata sannan wasu shida suka rasu, wanda ya kawo jumillar adadin wadanda suka kamu zuwa 15,102. Wadanda suka mutu kuma 127
    • Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce bai kamata Musulmi su dauki annobar korona a matsayin uzurin kin yin azumin watan Ramadana ba. Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce yana taya dukkanin Musulmin duniya murnar shiga watan mai tsarki.
    • Musulamai a fadin duniya sun fara Azumin Ramadana, amma ganin yadda aka kulle masallatai sannan aka saka dokokin bayar da tazara a mafi yawan kasashe, azumin bana zai yi wuya sosai
    • Shugaban Amurka Donald Trump na shan suka daga masana harkar lafiya kan kalamansa na cewa a yi wa mutane allura da maganin wanke datti
    • Kasar Spaniya ta bayar da rahoton adadi mafi karanci na wadanda suka mutu a kasar sakamakon cutar korona. Mutum 367 ne suka mutu a cikin awa 24 da ta shude
  14. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum 684 sun mutu a Burtaniya

    Mutum 684 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar korona a Birtaniya (Ingila, Scotland, Wales, Northern Ireland) cikin awa 24 da ta gabata, a cewar Sashen Lafiya.

    Lissafin ya kama ne ya zuwa ranar Alhamis karfe 5:00 na yamma.

    A gefe guda kuma, mutum 18,401 ne aka yi wa gwajin cutar kuma an gano 5,386 suna dauke da ita.

    A hannu guda kuma kasar Saudiyya ta bayar da rahoton samun mutum 1,172 da suka harbu da cutar korona a cikin awa 24 da ta gabata, wanda ya kawo jumillar adadin zuwa 15,102.

  15. Goodluck Jonathan ya taya Musulmi murnar azumin Ramadan

    Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bukaci musulmin Najeriya da su addu'o'in neman zaman lafiya da dorewar Najeriya da kuma kariya daga annoba.

    Tsohon shugaban na Najeriya wanda ya wallafa wannan sako a shafinsa na Facebook, ya ce yana fatan musulmi za su yi amfani da watan azumin na Ramadan domin samun karin kusanci da ubangiji.

    Daga karshe kuma mista Jonathan ya yi addu'ar Allah ubangiji ya karbi ibadun musulmi.

  16. Karin mutum 1,172 sun kamu da cutar korona a Saudiyya

    Kasar Saudiyya ta bayar da rahoton samun mutum 1,172 da suka harbu da cutar korona a cikin awa 24 da ta gabata, wanda ya kawo jumillar adadin zuwa 15,102.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma'akatar lafiyar kasar tana cewa wasu 124 sun warke daga cutar, yayin da karin mutum shida suka mutu.

    Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa jumillar wadanda suka mutu sun kai 2,049, yayin da wadanda suka mutu suka kai 127.

  17. Labarai da dumi-dumi, An mika bukatar gwajin korona ta intanet sau 5,000 cikin minti biyu a Birtaniya

    Gwamnatin Birtaniya ta ce sau 5,000 aka nemi gwajin cutar korona a cikin minti biyu kacal bayan an bude wani shafin intanet na musamman domin mutane su mika bukatar neman gwajin daga gidajensu ga hukumomi.

    Shaifin wanda yake bai wa ma'aikatan da ya zama dole su yi aiki damar neman gwajin cutar, an rufe shi sa'a biyu bayan bude shi.

    Gwamnati ta ce za a habaka yin gwajin na gida-gida da aka bukata daga shafin zuwa 18,000 a kullum daga mako mai kamawa.

    Birtaniya ta tsara yi wa mutum dubu 100 gwajin cutar a kowacce rana nan da karshen watan Afrilu.

  18. Bai kamata cutar korona ta hana Musulmi yin azumi ba - Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce bai kamata Musulmi su dauki annobar korona a matsayin uzurin kin yin azumin watan Ramadana ba.

    Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce yana taya dukkanin Musulmin duniya murnar shiga watan mai tsarki.

    Sai dai Buhari ya gargadi masu azumin da su takaita al'adun cakuduwa da aka saba lokacin azumin watan Ramadana kamar yayin sahur ko kuma buda-baki.

    Ya ce mutane su rinka cin abinci da gudanar da salloli a daidaiku ko kuma tare da iyalansu a gidajnsu.

  19. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum 587 sun mutu a Ingila

    Cutar korona ta sake yin ajalin wasu mutum 587 a Ingila, wanda ya kawo jumillar adadin wadanda suka mutu a asibitoci zuwa 17,373, a cewar hukumar lafiyar kasar NHS.

    Shekarun marasa lafiyar sun kama ne daga 40 zuwa 102, 34 daga cikinsu ba su da wasu cutukan na daban da ke damunsu bayan korona.

  20. An kara samun mutuwar mutum 64 a Scotland

    Babbar Ministar Scotland, Nicola Sturgeon ta ce karin wasu mutum 64 sun mutu a asibiti, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu a kasar zuwa 1,184.

    Sturgeon ta ce wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Scotland ya zuwa yanzu sun kai 9,697, inda aka samu karin mutum 288 a rana kafin haka.