Adadin masu cutar korona a Najeriya ya kai 782 - NCDC
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce an samu karin mutum 117 da suka sake kamuwa da cutar korona cikin sa'a 24 da ta wuce a kasar.
Don haka adadin masu fama da cutar a kasar ya kai 782 a daren Talata, kimanin wata biyu da bullar cutar Najeriya.
Fiye da rabi na sabbin alkaluman wadanda suka kamu, suna cikin jihar Legas a cewar alkaluman hukumar NCDC. Sai Abuja mai mutum 29, inda jihar Kano ta biye musu da mutum 14.