Coronavirus: Gidajen jaridu a Najeriya na neman 'durkushewa'
A Najeriya yayin da ake cikin mako na uku bayan da gwamnatin kasar ta sanya dokar hana zirga-zirga sanadin cutar korona, gidajen rediyo masu zaman kansu a arewacin kasar na fuskantar barazanar durkushewa.
Yanzu haka dai kungiyar masu gidajen rediyon a kasar ta fara neman agaji don kauce wa matsalolin da ka iya jefa 'ya'yanta cikin halin ha'ula'i.
Shugaban kungiyar, kuma mamallakin Liberty da ke Abuja, Tijjani Ramalan ya shaida wa BBC cewa "mu a nan Najeriya babbar hanyar samun kudin shigarmu ita ce samun tallace-tallace amma kamfanonin da ke ba mu tallar sun shaida mana cewa ba za su iya ci gaba da mu'amala da mu ba saboda cutar korona."
Ya kara da cewa "yanzu ba ma iya biyan ma'aikatanmu kuma bashi ya yi mana yawa. Muna kiran gwamnati da ta taimaka mana da rance daga asusu na musamman na tallafa wa kamfanoni irinsu domin tayar da komada."