Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Burtaniya za ta fara gwajin riga-kafin cutar korona

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Awwal Ahmad Janyau

  1. WHO: Ba kirkirar cutar korona aka yi ba a China

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce hujjoji sun nuna cewa cutar korona ta samo asali ne daga dabbobi, tare da yin watsi da rahotannin da ke cewa kirkirar cutar aka yi a China.

    A makon da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa za ta diba ikirarin da ake cewa kwatar cutar korona an kirkire ta ne a dakin bincike a Wuhan inda aka fara samun bullar cutar a karshen 2019.

    WHO ta yi watsi da ikirarin a ranar Talata, inda mai magana da yawunta, Fadela Chaib ta ce hujjoji sun nuna ba kirkirar cutar aka yi ba.

    "Mai yiyuwa ne, watakila cutar ta samo asali ne daga dabbobi," kamar yadda ta shaida wa taron manema labarai a Geneva.

    Sai dai ta ce ba a gano yadda dabbobi suka yada wa mutane cutar ba.

  2. Labarai da dumi-dumi, Wadanda suka kamu da korona sun zarta miliyan 2.5

    Sama da mutum miliyan biyu da rabi yanzu suka kamu da cutar korona a duniya.

    Yanzu mutum 2,501,156, suka kamu da cutar a duniya, kamar yadda alkalumman jami'ar Johns Hopkins da ke bin diddigin cutar a duniya ya nuna

    Adadin wadanda suka mutu sun 171,810 kawo yanzu.

  3. Birtaniya za ta fara gwajin rigakafin cutar korona

    Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa a ranar Alhamis za ta fara gwajin rigakafin cutar korona ga mutane.

    Sakararen lafiya na kasar Matt Hancock, ya ce ya ware sama da dala miliyan 50 domin aikin a jami’ar Oxford da kuma kwalejin Imperial a Landan.

    Ya ce amfanin kasancewa kasa ta farko a duniya da ta samar da rigakafi babban abu ne da za a iya sadaukar da komi akansa.

    Hukumomin Birtaniya sun kara bayar da rahoton mutum 852 da suk mutu a asibitotin Birtaniya, inda yanzu jimillar wadanda cutar korona ta kashe suka kai sma da mutum dubu goma sha bakwai.

  4. An ci tarar wadanda suka je biki a Ghana

    Wata kotu a Ghana ta ci tarar wasu mutane shida jumullar dala dubu 12, kwatankwacin sama da naira miliyan hudu da rabi, saboda samunsu da laifin saba dokar kulle, da taron jama'a.

    Mutanen sun halarci liyafar, ranar haihuwa ne, ranar Asabar da ta wuce a wata unguwa da ke wajen babban birnin kasar, Accra.

    Gwamnatin Ghanar, ta haramta taruka ko haduwar mutane a karkashin dokar kullen da ta sa, ta tsawon sati uku, domin hana bazuwar kwayar cutar Korona, dokar da aka dan sassauta a jiya Litinin.

    Sama da mutane dubu daya ne dai hukumomin kasar suka tabbatar sun kamu da cutar ta Korona, inda tara kuma suka rasu.

  5. Cutar korona na kara yaduwa a Makkah da Madina

    Ma'aikatar lafiya a Saudiyya ta ce mutum 1,147 sun kamu da cutar korona a rana daya, inda yanzu adadin yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai 11,631 a kasar.

    Kamfanin dillacin labaran SPA ya ce an samu karuwar cutar a 'yan kwanakin da suka gabata sakamakon karuwar gwaji da ake yi, kamar yadda kakakin ma'aikatar lafiya na kasar ya bayyana a wani taron manema labarai.

    Kawo yanzu mutum 109 aka tabbatar da cutar korona ta kashe a Saudiyya. Mutum 1,640 suka warke zuwa yanzu.

    A Makkah cutar ta fi yaduwa inda mutum 305 suka kamu, sai Madinah inda 299 suka kamu sai kuma 171 a Jeddah, 148 a Riyadh.

    Ministan lafiya na Saudiyya Dr. Tawfiq Al-Rabiah ya yi gargadin cewa yawan masu cutar za su kai sama da 200,000 cikin makwanni.

  6. Yadda za a koma yin shari’a a kotu ta intanet a Najeriya

    Ma’aikatar shari’a a Najeriya ta bayyana yadda za ta aiwatar da nazarinta da ta ke yi na komawa ga tsarin yin shari’a ta hanyar intanet bayan cutar korona ta dakatar da harakokin shari’a a kasar.

    Ministan sharia Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa ganin yadda lamurra suka sauya sanadiyyar takaita zirga-zirga saboda bazuwar cutar korona ya sa suka nemi wannan mafita.

    Ya ce mutane suna da shari’o a kotu, kuma akwai bukatar a diba hakkokinsu amma wannan damar ta kubuce saboda yanayin da aka samu kai, ba tare da yin tunanin za a shiga wanna hali ba.

    "Ina sanar da ku cewa mun yanke hukunci da bin bahasin matsalolin da ke da nasaba da shari’a ta hanyar amfani da intanet da kafofin talabijin.”

    "Bukata ta kama da rokon masu sauraren shari’a su hakura da hakkinsu na hutu na shekara shekara don biyan bukatun hakkokin jama’a bisa yanayin da aka shiga.” in ji ministan na shari’a.

    Ya kuma ce abin da suke kokarin cimma ya kasance ba a tauye wa masu hakki, hakkokinsa ba na ganin cewa kotu ta zauna a kan kari ta dauki mataki na bin sawun shari’a duk da halin da ake ciki.

    Ya ce akwai kwamiti da ke nazari kan bukatar, idan ya kammala za su sanar da lokacin da za a fara aiki da sabon tsarin na yin shari’a ta intanet.

  7. Wanne tasiri karyewar farashin man fetur zai yi ga Najeriya?

    Farashin man fetur ya yi faduwar da bai taba yin irinta ba a cikin shekaru sakamakon annobar korona, lamarin da ya kara tayar da hankalin kasashen duniya.

    Farashin danyen mai nau'in West Texas Intermediate na Amurka a ranar Litinin ya yi karyewar da ya zama tamkar ana neman kai da shi karon farko a tarihi.

    Haka ma farashin danyen mai a Turai da sauran kasashen duniya ya fadi da kashi 8.9% inda ake sayar da man kan $25 duk ganga.

    Yawan man fetur shi ne ya janyo faduwar farashinsa kamar yadda ta taba faruwa a 2015 inda farashin ya yi matukar faduwa A halin yanzu dai akwai man da yawa a kasuwa, yayin da farashin ke faduwa saboda barkewar annobar coronavirus.

    Farashin ya yi kasa fiye da farashin da Najeriya ta yi hasashe a cikin kasafin kudinta na bana.

    Najeriya na dogaro ne da arzikin man fetur, kimanin kashi 90% na kudaden shigarta ke fitowa daga man da take sayarwa.

    Faduwar farashin ne ya tilatstawa gwamnatin Najeriya sake tsara kasafin kudinta, inda a watan Maris gwamnatin Najeriya ta yi wa kasafin kudinta kwaskwarima saboda barazanar cutar korona.

    Farfesa Mustapha Muktar masanin tattalin arziki a Jami'ar Bayero Kano, ya ce yadda farashin man ke faduwa, gwamnatin Najeriya ba za ta iya aiwatar da kasafin kudin bana ba.

    "Idan an sayar da mai yakan dauki lokaci kafin kudinsa ya dawo, nan gaba kasashen masu fetur za su shiga mugun mawuyacin hali saboda kudaden da suke samu ya ragu," in ji masanin.

    "Kudin da za a saya a kasuwar duniya ba zai kai kudin da aka hako shi ba," a cewarsa.

    Ya kuma ce faduwar farashin zai yi tasiri sosai ga sauran fannonin tattalin arziki inda wasu ma za su durkushe, saboda arzikin mai ne ke samar da kudaden shiga da ke yunkura sauran fannonin.

    "Idan farashin ya ci gaba da faduwa sauran fannonin ma za su durkushe," in ji shi.

  8. Nijar ta daure mutum 10 kan cutar korona

    An daure mutum 10 a Jamhuriyyar Nijar bayan zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi kan adawa da dokar hana fita don gudun yaduwar cutar korona.

    Matasa da dama ne suka fito suk rufe hanya a birnin Yamai.

    'Yan sandan a Yamai sun ce sun cafke mutum sama da mutum 100. Kuma jami'ai sun ce an kama wasu saman babura suna raba jarkunan fetir inda kum aka kone gidajen mutane da dama.

    A ranar Lahadi 'yan sanda sun tarwatsa wani gungun mutane da suke shirin gudanar da sallar jam'i.

  9. Labarai da dumi-dumi, Mai tsaron lafiyar Shugaba Buhari ya rasu

    Daya daga cikin masu tsaron lafiyar Shugaba Buhari na Najeriya ya rasu.

    Mai bai taimakawa Shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a Twitter ranar Talata.

    Ya ce ya dade yana fama da ciwon suga.

  10. An haramta sallar jam'i a masallatai a Nasarawa

    Gwamnatin jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ita ma ta dauki wasu matakai na hana yaduwar cutar korona, ciki har da haramta sallar jam`i a dukkan masallatai da sauran harkokin ibadah da na rayuwa da suka shafi hada taron jama`a.

    Malam Yakubu Lamai kakakin gwamnan jihar Nasarawa, wanda ya tabbatar wa BBC matakin, ya ce ya kuma shafi duk wani taron ibadah na mabiya addinin kirista.

    Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja, har yanzu ba a samu bullar cutar korona ba a jihar. Gwamnatin jihar kuma ta ce tana daukar duk matakan da suka dace ne domin dakile bullar cutar a jihar.

    Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar Talata a Twitter ta ce ta killace wasu mutanen da suka fito daga jihohin Legas da Kano da ke fama da cutar.

  11. Yawan masu cutar korona sun kusan kai miliyan 2.5

    Yanzu kusan mutum miliyan biyu da rabi suka kamu da cutar korona a kasashe 185, yayin da cutar ke ci gaba bazuwa.

    Akalla mutum 170 cutar ta kashe.

    Yanzu mutum 2,494,915 aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a fadin duniya, yayin da cutar ta kashe jimillar mutum 171,152, kamar yadda alkalumman jami'ar Johns Hopkins da ke bin diddigin cutar suka nuna a ranar 21 ga Afirlu.

    Cutar ta sarkewar numfashi, ta fara bulla a garin Wuhan a China a karshen 2019. Kuma yanzu cutar ta fi yawa a Amurka, yayin da take ci gaba da yaduwa.

  12. Boris Johnson zai tattauna da Sarauniya

    Ana sa ran Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai tattauna da Sarauniyar Ingila a cikin wannan makon.

    Tattaunawar da za su yi ta wayar tarho ita ce ta farko tsakanin Boris Johnson da Sarauniya tsawon mako uku da Firaministan ke jinya.

    Ana kuma sa ran Firaministan zai tattauna da shugaba Trump na Amurka idan an jima.

    Fadar gwamnatin Birtaiya ta ce tattaunawar dama ce ta samun karin bayani kan matakan da ake dauka kan cutar korona tsakanin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki.

    Har yanzu Boris Johnson na farfadowa a wani gidan gwamnati a Chequers, ba tare gudanar da ayyukan gwamnati ba.

  13. Cutar korona za ta ninka yawan masu fama da yunwa a duniya

    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa annobar cutar korona za ta ninka yawan mutanen da ke fuskantar masananciyar yunwa a duniya.

    Hasashen hukumar ya ce an kara samun mutum miliyan 130 da ke fama da yunwa a duniya inda adadin ya karu zuwa mutum miliyan 265 a 2020 daga miliyan 135 a 2019 sakamakon tasirin annobar cutar korona ga tattalin arzikin duniya.

    Gargadin na WFP na zuwa a yayin da wasu alkalumma ke bayana matsalar abinci da ake fuskanta a sassan duniya

  14. Coronavirus: Yadda ake tsangwamar 'yan Afrika a China

    A yanzu haka ana killace 'yan Afrika ba tare da son ransu ba a wasu wuraren a China ko da kuwa gwaji ya nuna ba sa dauke da cutar korona.

  15. Coronavirus: Asibitoci masu zaman kansu sun dakatar da aiki a Legas

    Wani asibiti mai zaman kansa a birnin Legas na Najeriya ya dakatar da aiki sakamakon mu'amila da masu cutar korona.

    Asibitin mai suna St Nicholas, a wata sanarwa, ya ce za ta dakatar da ayyukanta har na tsawon mako biyu.

    Darektan asibitin ya ce za a wanke harabar asibitin sannan a rufe shi har zuwa tsawon lokacin da gwamnati ta amince.

    An sanar da marasa lafiya da su tuntubi likitocin asibitin ta hanyar waya ko intanet.

    Kafafen watsa labarai na birnin na Legas sun rawaito cewa akwai karin asibitoci masu zaman kansu guda biyar da su ma sun rufe sakamakon cutar ta korona.

    Jihar Legas dai na da mutum 376 da ke dauke da cutar korona, inda ko a makon da ya gabata wani likita mazaunin birnin ya mutu a wani asibiti mai zaman kansa.

  16. Coronavirus: An hana tururuwar jama'a a Ramadan a Indonesia

    Shugaban kasar Indonesia ya sa dokar hana cincirindon musulmi domin bukukuwan sallah da ake yi a karshen watan Ramadana da manufar dakile yaduwar cutar korona.

    To sai dai masu fashin baki na ganin ya hakan ya zo a makare.

    Kimanin mutum milyan guda ne ake kyautata zaton sun fice daga birnin Jakarta zuwa kauyukansu daf da fara azumin watan Ramadan.

    Da dama 'yan kasar na tinanin cewa ba abu ne maiyiwuwa ba a ce ba za su koma kauyukansu ba a lokacin watan Ramadan inda a nan za su yi bukukuwan sallah karama.

    A lokacin sallar karama dai jama'a sanye da sabon tufafi kan cika filayen kwallo da wuraren farkin da kuma wuraren shakatawa domin gudanar da sallar idi.

    To sai dai masana lafiya na fargabar hakan ka iya jefa mutane cikin wani hali kasancewar babu wuraren gwaji da ma asibitoci a kauyukan da suke.

  17. Ka da a yi garaje wajen cire dokar hana zirga-zirga - WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta gargadi kasashen da ke shirin janye dokokin kulle da na hana zirga-zirga da su yi kaffa-kaffa.

    WHO ta ce janye dokar kulle cikin gaggawa ka iya mayar da hannun agogo baya.

    "A jira har a samar da rigakafin cutar ko kuma wani jinjinan maganin cutar to za a iya samun fifa-iya-koma baya."

    Kasashe kamar Japan da Singapore sun samu karin mutanen da ke dauke da cutar, al'amarin da ya sa ake ganin cutar ta sake yin kome.

  18. Ko cutar korona ka iya zama alkairi ga India?

    Jim kadan bayan da kasar India ta sa dokar hana fita a watan da ya gabata lokacin da ta rufe duk harkokin sufuri domin dakile bazuwar cutar korona, samman kasar mai cike da hazo sakamakon gurbatar iska ta washe sannan iska ta yi wasai

    Tuni dai 'yan kasar suka fara watsa hotuna wurare da a baya suka yi duhu, amma yanzu sun washe.

  19. Cutar korona ta bulla a gidan yarin Younde

    Hukumomi a birnin Younde na Kamaru sun tabbatar da samun masu cutar korona 13 a gidan yarin birnin mai suna Kondegui, kamar yadda jaridar Journal du Cameroon ta intanet ta rawaito.

    Gidan yarin dai wanda ya kamata ya dauki mutum 1000 na da cunkoso inda yake da fursunoni 4,000.

    Jaridar ta Journal du Cameroon ta ce, fursunonin sun shaida cewa sun samu mutanen da suka mutu saboda cutar korona.

    Jagoran masu adawar kasar, Maurice Kamto ya ja hankalin hukumomin kasar da su saki fursunonin da ke gidajen yarin kasar domin rage cunkoso.

    To sai dai a hannu daya kuma shugaba Paul Biya ya bayar da gudunmowar kayan kariya da suka hada da takunkumin kariya na dala miliyan 3.3 ga gundumomin kasar 360, kamar yadda jaridar ta ce.

  20. 'Ba cutar korona ba ce kawai ke kashe jama'a a Burtaniya ba'

    Mace-mace a Ingila da yankin Wales sun karu fiye da yadda aka zata, inda alkaluman suka wuce na shekaru 20 da suka gabata.

    Ofishin Burtaniya mai fitar da kididdiga ya ce an samu mace-mace 18,500 a makon farko na watan Afrilu.

    An dai alakanta mutuwar mutum fiye da 6,200 ga annobar korona, inda kaso daya cikin shida na mutanen suka mutu ba a asibiti ba.

    To sai dai mace-macen maras alaka da korona sun karu, abin da ya sa ake alakanta su da dokar hana fita da ke tasiri a kan jama'a.