Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Dole gwamnonin Arewa su tallafa wa 'yan cirani a Lagos'
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail
An kama mutanen da suka yi yunkurin sanya wa jami'an tsaro coronavirus
Ma'aikatar cikin gidan Tunisia ta ce ta kama mutum biyu, ciki har da wanda ake zargi da ikirarin yin jihadi, saboda zargin kitsa shafawa jami'an tsaro cutar korona.
Ma'aikatar ta ce mutumin da ake zargi da jihadin - wanda aka saka daga gidan yari kwana baya - ya yi yunkurin zuga mutanen da ke da cutar korona domin su yi atishawa a kusa da 'yan sanda da jami'an tsaro.
Daya mutumin ya ce an gaya masa ya rika yin tari da atishawa a ko'ina da gangan amma wasu mutane sun kai kararsa wurin 'yan sanda.
Yanzu dai za a yi masa gwajin cutar korona domin sanin ko yana da ita ko kuwa karya yake yi.
Yadda gobara ta kashe wani mutum a kasuwar Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi da ke Najeriya, Bala Mohammed, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar wani mutum sakamakon gobarar da ta tashi a Muda Lawal, kasuwa mafi girma a jihar.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis.
A sakon da Gwamna Bala Mohammed ya wallafa a Twitter, bayyana cewa: "Muna matukar jimanin wannan rasuwa, kuma muna addu'a Allah ya kade faruwar irin wannan a gaba sannan muna taya iyalansa alhini."
Ba wannan ne karon farko da kasuwanni ke gobara a jihar ba, abin da ake dangantawa da wutar lantarki.
Covid-19: Kano ta zama fayau
Hotunan da wakilinmu na Kano, Khalifa Shehu Dokaji, ya dauko mana da safiyar Juma'a sun nuna birnin fayau.
Hakan ya faru ne sakamakon dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya don dakile cutar korona, wacce ta soma aiki a daren Alhamis.
Mutum 21 ne suka kamu da cutar ta korona a Kano, inda ta yi ajalin mutum daya.
Hira ta musamman da likita kan covid-19 a BBC Hausa Facebook
Ku kasance da mu kai-tsaye da misalin karfe 11 na safe a agogon Najeriya da Nijar domin kallon hira ta musamman da kwararren likita, Dr Nasiru Sani-Gwarzo, kan cutar korona a shafinmu na Facebook.
Covid-19: An sauke gwamnan da ya dage sai an yi sallar jam'i
Firai Ministan Sudan Abdalla Hamdok ya sauke gwamnan babban birnin kasar, Khartoum, bayan ya bijire wa dokar hana yin sallar jam'i wadda gwamnati ta yi domin dakile yaduwar cutar korona.
Janar Ahmed Abdun Hammad Mohammed ya ki aiwatar da matakin da aka dauka na haramta yin sallah a masallatai da kuma ibada a coci-coci wacce za ta soma aiki ranar Asabar.
Tun da fari, ranar Alhamis 'yan sanda sun fesa barkono-tsohuwa kan masu goyon bayan hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir. Suna zanga-zangar adawa da matakin da gwamnatin rikon kwarya ta dauka na gudanar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.
Za a raba kayan gwajin covid-19 miliyan daya a Afirka
Hukumar yaki da cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta sanar cewa za ta kaddamar da shirin raba kayan gwajin cutar korona miliyan daya domin cike "wagegen gibin" da aka samu na rashin gwajin cutar a baya.
Shugaban hukumar John Nkengasong ya ce akwai karancin yadda ake gudanar da gwajin cutar a Afirka.
Ya kara da cewa kungiyar Tarayyar Afirka (AU) za ta raba kayan gwajin daga mako mai zuwa domin tallafa wa kasashen da ba su da halin yin gwajin.
Dr Nkengasong ya ce Najeriya, kasar da ta fi kowacce kasa yawan al'umma, ba ta da kayan gwajin cutar korona da yawa - Najeriya dai tana da yawan al'umma fiye da miliyan dari 200 amma ya zuwa yanzu ta gudanar da gwajin cutar korona a kan mutanen da basu wuce 6,000 ba, yayin da Habasha, wacce ke da yawan al'umma fiye da miliyan 100, ta gwada mutum 5,000 zuwa yanzu.
"Daga yanzu zuwa wata uku ko shida, watakila muna bukatar gwada mutum miliyan 15, sai dai kamar yadda 'yan magana kan ce da babu gwara ba dadi," in ji shi.
Barka da Juma'a
Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da safiyar Juma'a.
Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.
Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.