Covid-19: Mutum 83 sun warke a Ghana
Hukumomi a Ghana sun ce mutum 83 sun warke daga cutar korona.
A cewar hukumar lafiyar kasar, utum 17 na jiran sakamakon gwajin da aka yi musu wanda ake sa ran zai tabbatar su ma sun warke daga cutar.
Ana yin gwaji sau biyu zuwa uku kan mutanen da ke fama da cutar kafin a tabbatar sun warke.
Ya zuwa ranar Alhamis, an tabbatar mutum 642 suna dauke da cutar inda ta yi ajalin mutum takwas.