Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya ranar 16/04/2020

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen kawo muku bayanan irin wainar da ake toyawa a sassan duniya dangane da annobar korona. Da fatan za ku kasance da mu gobe da safe inda shirin zai dawo muku. Amma kafin nan ku ci gaba da karanta labaranmu da ke shafin BBC Hausa.com da kafafen sada zumunta na Facebook da Twitter da Instagram. Sai da safe.

  2. Coronavirus: Dalilin da ya sa Sweden ba ta kulle jama'a ba

    Firai Ministan Sweden, Stefan Löfven ya kare matakin gwamnatinsa na kin kafa dokar hana zirga-zirga don yaki da cutar korona.

    Mr Lofven ya ce salon da ake amfani da shi na kyale makarantu da kasuwanni ci gaba da harkokinsu yayin da ake nesa-nesa da juna na aiki.

    Ya fada wa manema labarai cewa kasar Sweden ba ta gaza ba.

    Wakiliyar BBC ta ce dokokin Sweden ba su bai wa ministoci damar daukar wasu matakai ba tare da amincewar majalisa ba, amma a yanzu bayan doguwar tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa, an amince da wata sabuwar doka da ta bai wa gwamnati ikon daukar mataki a yayin annobar.

  3. Coronavirus: An tsawaita dokar hana zirga-zirga a Burtaniya

    Gwamnatin Birtaniya ta ce dokokin da aka kafa don hana yaduwar cutar korona za su ci gaba da kasancewa har nan da makwanni uku.

    Sakataren harkokin wajen kasar Domic Raab, ya ce duk da cewa akwai alamun dokokin na taimakawa wajen rage yaduwar cutar, duk wani canji da za a yi a yanzu ka iya kawo barazanar karuwar yaduwarta.

    Ya ce yayin da gwamnati ke nazartar yadda al'amura ke kasancewa a sauran kasashen duniya,a nasu bangaren za su dauki matakin da ya dace ne dai-dai da halin da ake ciki a kasar.

    A ranar Alhamis din nan ne aka bayar da rahoton mutuwar jimillar mutane dubu goma sha takwas tun bayar barkewar cutar a kasar.

  4. Cutar korona na raguwa a birnin New York - Andrew Cumo

    Gwamnan jihar New York inda cutar korona tafi kamari a Amurka, ya sanar da raguwar mutanen da ake kwantarwa a asibiti da sashen bayar da kulawar gaggawa.

    Andrew Cumo, ya ce samun raguwar a yau, ya nuna cewa hukumomi za su iya shawo kan cutar baki daya.

    Ya kara da cewa “a baya ba mu da tabbacin za mu iya, mun yi tacewa za mu iya ba tare da mun san hakan ba, amma a yanzu, mun san cewa za mu shawo kan cutar korona.”

    To sai dai duk da haka, ya ce jihar na bukatar taimakon gwamnatin Amurka don kara yawan cibiyoyin gwaji da kuma samar da karin mutanen da ke bincike don gano wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu.

  5. Coronavirus: Za a fara gurfanar da masu motsa jiki gaban kuliya a Abuja

    Daga gobe Juma'a. za a fara kama da gurfanar da masu motsa jiki da safe a birnin Abuja.

    Jaridar Premium Times ta rawaito jami'in da ke jagorantar kwamiti na musamman kan aiwatar da takaita zirga-zirga a birnin, Ikharo Attah yana fadin cewa "muna da kotun tafi da gidanka akalla guda biyar da za mu gurfanar da masu laifi nan take."

    Mista Attah ya kara da cewa "ya zuwa karfe daya na yammar Alhamis, mun samu masu laifi guda 20 sannan biyu ba su amshi laifin da ake tuhumar su da shi ba."

  6. An ci tarar mai gari saboda karya dokar takaita zirga-zirga

    An ci tarar wani mai gari a jihar Victoria ta kasar Australia bisa karya dokokin takaita zirga-zirga bayan daukar hotonsa yana kwankwadar barasa.

    An dai kama Tony Herbert, wanda shi ne mai garin Warmambool bayan daukar sa a hoto rike da kwalabar giya yana yin marisa.

    Wani abin takaici shi ne 'yan sa'o'i kadan kafin kama mai gari, an ji shi yana jan hankalin jama'a da su kasance a cikin gidajensu.

    A ranar Alhamis din nan ne 'yan sandan jihar ta Victoria suka ci tarar Mista Herbert har dala 1,652 saboda kin mutunta dokar takaita zirga-zirga da kuma bayar da tazara da gwamnati ta tasa domin dakile bazuwar cutar korona.

  7. Zakuna sun maye gurbin mutane a wani titin Afirka ta Kudu

    Nan gaba kadan dabbobi za su fahimci cewa annobar cutar korona ta kawar da mutane daga ban kasa sakamakon dokar hana zirga-zirga kuma tuni zakuna suka fahimci hakan Afirka ta Kudu, inda suka fara shakatawa a kan tituna.

    Richard Sowry na gidan namun dajin Kruger National Park ya fita ran-gadi a lokacin da ya ci karo da zakunan a ranar Laraba suna baccin rana a kan titin da ya saba cika da zirga-zirgar jama'a musamman 'yan yawon bude ido.

    Gidan namun dajin na Kruger ya kasance a garkame tun ranar 25 ga watan Maris saboda dokar hana fita domin yaki da cutar korona.

    Akasari sai da dare ne ake ganin manyan namun dawa kamar su zaki idan masu ran-gadi sun fito bakin aiki.

  8. Rasha ta dage bikin nasara a Yakin Duniya na biyu saboda cutar korona

    Shugaban Russia, Vladimir Putin ya sanar da dage ranar bikin nasarar da kasar ta samu a yakin duniya na biyu da za a ranar 9 ga watan Mayu a dandalin taro na Moscow Red Square.

    Shekara 75 kenan da nasarar da daular Soviet ta samu a kan gwamnatin Nazi ta Jamus a 1954.

    Rasha dai ta kara samun karin mutum 3,448 da ke dauke da cutar korona ranar Alhamis, inda adadin masu cutar ya zama 27,938.

    An samu mutum 232 da suka mutu sakamakon cutar, inda ake tsammanin mamatan sun fi haka.

  9. Annobar korona: Wasu mutum 753 sun mutu a Faransa

    Faransa ta bayar da rahoton mutuwar mutum 753 a cikin sa'a 24 da suka gabata - jumullar wadanda suka mutu a kasar sun zama 17,920.

    Yanzu kasar ta zama ta hudu da ke da mafi yawan wadanda suka mutu a duniya sakamakon cutar korona.

    Jerome Salomon, shugaban hukumar lafiya ya ce jumullar mutanen da ke sashen kulawar gagggawa sun ragu a kwana na takwas a jere zuwa 6,248 - mafi karanci tun daga 1 ga watan Afrilu.

    Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 108,847 bayan ya karu a kan 106,206 da aka bayyana a jiya.

  10. Daga kasar Ghana...

    Ministan Yada Labarai na kasar Ghana, Kojo Oppong Nkrumah ya yi taron manema labarai, inda ya bayar da karin bayani kan matakan yaki da cutar korona a kasar.

    Ga wasu daga cikin abubuwan da ya fada:

    • Zuwa yanzu an yi wa mutum 50,719 gwajin cutar korona a Ghana kuma 641 ne aka gano suna dauke da cutar - kashi 1.3 kenan cikin 100
    • Mutum 83 ne suka warke daga cutar
    • Bayar da wutan lantarki kyauta na watannin Afrilu da Mayu da Yuni zai sa gwamnati ta kashe GH₵ biliyan daya, inda ake sa ran mutum miliyan 4.8 za su amfana
    • Wadanda suka sayi katin wuta kafin bayar da sanarwar za su sha wutar kudinsu a watannin gaba
    • Wadanda aka yanke musu layi ba za su sha wutar ba har sai an mayar da su
    • Hukumar kwallon kafar Ghana (GFA) ta bayar da tallafin wuri mai cin gado 250 ga gwamnati domin yin amfani da shi a matsayin wurin killace marasa lafiya
    • Gwamnati tana taimaka wa wadanda suka bayar da gidajensu domin yin amfani da su wurin ayyukan harkokin lafiya
  11. Coronavirus: 'Sauro ba ya yada cutar a tsakanin al'umma'

  12. Coronavirus: An sallami mutum biyar, uku sun mutu a Legas

    Ma'aikatar Lafiya ta jihar Legas ta sanar da karin mutum uku da suka mutu sakamakon cutar korona.

    Ma'aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa yanzu haka mutum 10 kenan suka mutu a jihar.

    Mamatan dai dukkaninsu maza ne masu shekaru 51 da 52 da kuma 62.

    Har wa yau, ma'aikatar ta kuma sanar da warkewar karin mutum biyar wadanda aka sallama bayan sake yi musu gwaji har sau biyu, inda sakamakon ya nuna ba sa dauke da kwayar cutar.

    Wadanda suka warke din dai sun kunshi mata 3 da maza 2.

    Yanzu haka mutum 90 ne kenan suka warke daga cutar a Legas.

  13. Coronavirus: Yadda aka lalata makarantu fiye da 200 a Afirka ta Kudu

    Kusan makarantu 200 ne aka lalata a fadin Afirka ta kudu, ta hanyar banka musu wuta ko kuma balla kofofinsu.

    Hakan dai ya faru ne a tsawon makonni ukun da suka gabata lokacin da gwamnatin kasar ta sanya dokar hana fita a fadin kasar domin dakile yaduwar cutur korona makonni 3 da suka gabata.

    Mafi yawan makarantun da ta'asar ta shafa dai na lardin Gauteng da ke zaman cibiyar tattalin arzikin kasar.

  14. Kasashen G-5 na Sahel sun yi taro kan cutar korona

    Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G-5 ta Sahel sun gudanar da wani taro ta hanyar bidiyo, domin tattauna matsalolin tsaro da kuma yanayin da kasashen ke ciki game da cutar korona.

    Haka kuma ministocin sun yi nazari a zaman da sukka yi jiya, Laraba, kan maganar kasancewa tsintsiya madaurinki guda, wajen yakar masu ikirarin jihadi a yankin na Sahel.

    Kasashen guda biyar na G-5 su ne Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma jamhuriyar Nijer.

  15. Coronavirus: EU na fuskantar matsin lamba kan gaza agaza wa Italiya

    Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce ya kamata tarayyar ta nemi ahuwar Italiya saboda gaza ba ta tallafin da ya kamata tun farkon barkewar cutar korona.

    Misis Von der leyen ta ce fadin gaskiya da kuma amince wa da ita, muhimmin abu ne a yaki da cutar korona.

    Ta ce gaskiya ne, kasashe da dama, ba su kai agaji yayin da Italiya ke tsaka da bukatar dauki ba tun a farko, a kan wannan ba shakka tarayyar turai na neman afuwa.

    Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Italiya ta yaba da wadannan kalamai da ta kira gaskiya tsagwaronta.

    Kasar ce ta farko da tasirin annobar ya fi shafa sosai, kana yawan mutanen da suka mutu a cikinta sun fi na Amurka.

  16. Mutum uku sun warke daga covid-19 a jihar Bauchi

    Mutum uku sun warke daga cutar korona a jihar Bauchi, a cewar gwamnan jihar Bala Mohammed.

    A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter yau Alhamis, gwamnan ya ce tuni aka sallame su daga cibiyar killace masu korona bisa amincewar hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya.

    Ya zuwa karfe 11:20 na daren Laraba, NCDC ta ce mutum shida ne suka kamu da cutar a Bauchi.

    Da wannan sanarwa ta gwamna, mutum uku ne kenan suka rage masu dauke da cutar ya zuwa lokacin da ya wallafa sanarwar.

  17. 'Najeriya ta tanadi jiragen mayar da 'yan kasarta gida'

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta tanadi jirgi biyu na musamman domin aikin debo 'yan kasar da suka makale a kasashen duniya daban-daban sakamakon annobar cutar korona.

    Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyema ne ya bayyana haka a yau Alhamis a wurin taron manema labarai da kwamitin shugaban kasa kan cutar korona yake yi kullum a Abuja.

    Ya ce: "Saboda yawan wadanda ke bukatar su dawo gida Najeriya da kuma karancin wuraren killace mutane, za a yi jigilar ne rukuni-rukuni."

    Ministan ya ce sun tattara adadin 'yan Najeriyar da ke son komawa gida ta hanyar ofisoshin jakadancinta na kasashe.

    A jiya Laraba wani dan Najeriya mazaunin Dubai da bai yarda a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa suna matukar bukatar su koma gida saboda halin da suke ciki na dokar hana fita da take aiki a birnin.

  18. 'Jami'an tsaron Najeriya sun kashe mutum 18 a lokacin cutar korona'

    Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Najeriya ta ce jami'an tsaron kasar sun kashe akalla mutane 18, yayin aiwatar da dokar hana zirga-zirga da aka kakakaba a wasu jihohi don yaki da cutar Korona.

    Wannan adadi dai ya zarce na mutanen da ita kanta cutar ta kashe a kasar baki daya, da ya tsaya a mutum 12.

    Hukumar ta ce ta samu korafe-korafe fiye da 100 da ke da alaka da take hakki, ciki kuwa harda wadanda ta ce sun shafi kisan jama'a.

    A Najeriya dai hukumomi sun kakaba dokar hana zirga-zirga a manyan biranen kasar uku, ciki har da babban birnin kasar Abuja.

    Ko da a ranar Laraba sai da wani likita ya mutu saboda kamuwa da cutar a birnin Legas.

  19. Coronavirus: Russia za ta karbi agaji daga Amurka

    Fadar mulki ta Kremlin ta Russia ta ce za ta karbi tayin da shugaba Trump yayi mata na aika naurorin taimakawa numfashi don yaki da cutar Korona.

    Mai magana da yawun shugaban Russia Vladmir Putin ya ce shugaban ne da kansa ya amince cewa akwai bukatar a taimaki juna a wannan lokaci na annoba.

    Ya ce tun da ya zama dole, Russia za ta yi hakan, kasan cewa shugaba Putin ya yarda da kaddarar annobar Korona, wannnan babbar dama ce ga Russia ta taimaka wa jama'a.

    Shugaba Trump ya mika bukatar ne duk da tsamin dangantakar da ke akwai tsakanin Amurika da Russia.

    A farkon watannan ne wani jirgin saman Russia ya kai agajin naurorin taimakawa numfashi da sauran kayan aikin lafiya birnin New York, in da annobar tafi kamari a Amurika.

  20. Mutum miliyan 21 sun rasa aikinsu cikin mako hudu a Amurka

    Amurkawa miliyan 21 ne suka rasa ayyukansu a cikin mako hudu da suka gabata, kamar yadda sababbin alkaluma suka nuna. Wannan ne adadi mafi yawa sosai a tarihi.

    A cewar Ma'aikatar Kwadago, wadanda suka bayyana rasa ayyukansu a kasar sun kai miliyan 5.25 zuwa ranar 11 ga watan Afrilu.

    Adadin makon da ya gabata kuma ya kai na mutum miliyan 6.6.

    Akasarin kasar Amurka na cikin dokar hana fita sakamakon annobar cutar korona, abin da ya durkusar da tattalin arzikin kasar saboda dakatar da ma'aikata da masu kamfanoni suka yi.

    Akwai hasashen cewa rashin aikin yi zai iya kai wa kashi 20 cikin 100 a wannan watan.