Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faruwa a Najeriya da sassan duniya ranar 15/04/2020

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Usman Minjibir

  1. Sabbin alkaluman cutar korona a Birtaniya

    • Ingila: Alkaluman masu mutuwa sun karu da 651 inda adadin ya kai 11,656
    • Scotland: Mutum 962 ne aka rawaitio sun mutu tun bayan kamuwa da cutar korona. Kaso hudu na masu mutuwar tsaffi ne da ke gidan kula da tsaffin.
    • Wales: Kafafen watsa labaran yankin Wales sun ce an samu karin mutum 60 da suka mutu a cikin awanni 24, inda adadin wadanda suka mutu ya zama 463.
    • Northern Ireland: Da misalin karfe 11:30 na safiyar Laraba an samu karin mutum shida da suka mutu sakamakon cutar korona, inda adadin mamatan ya kai 140.
  2. An kaddamar da manhajar gano masu dauke da Covid-19 a Ghana

    Ghana ta kaddamar da wata manhajar wayoyin hannu da nufin taimaka wa hukumomi wajen gano mutanen da ake zaton sun kamu da cutar korona.

    Gwamnatin kasar ta ce manhajar za ta taimaka wajen sauya salon yaki da annobar, kuma kawo yanzu an yi amfani da manhajar wajen gano kusan mutum 100 da ake ji suna da cutar.

    Manhajar za ta ringa amfani da taswira ta hanyar GPS wajen bibiyar wuraren da mutum ya je, abin da zai ringa bai wa hukumomi damar gano ko mutum ya yi mu'amala da wanda aka tabbatar yana dauke da cutar.

    Za kuma a yi amfani da ita wajen gano ko mutanen da aka umarta su kebe kansu suna aiki da umarnin, duk da cewa ba a san irin hukuncin da za a yi wa wadanda ba su bi umarnin ba.

    Za a iya amfani da manhajar a yaruka biyar, amma da yake masu amfani da wayoyin tafi-da-gidanka na zamani basu wuce 35% ba, amfanin manhajar zai iya zama takaitacce.

    Ana nuna damuwa kan batun tsaron bayanan masu amfani a manhajar, sai dai ma'aikatar sadarwa ta ce ana tabbatar da kiyaye bayanan masu amfani da manhajar.

    Kawo yanzu Ghana ta yi wa mutum 37,000, sannan ta tabbatar da cewa mutum 636 sun kamu, sannan mutum takwas sun mutu.

    A bangare daya kuma Asusun Lamuni na Duniya, IMF, ya tallafa wa Ghana da kusan dala biliyan daya domin taimaka mata rage dawainiyar cutar.

    An sanya dokar hana fita a wasu sasssan Ghana da suka hada da babban birnin kasar Accra, sannan iyakokin kasar sun ci gaba da kasancewa a rufe.

  3. Coronavirus: Trump ya tayar da kura kan janye tallafin WHO

    Shugabannin kasashen duniya da manyan likitoci da jami'an Diplomasyya sun soki matakin shugaba Trump na janye tallafin da Amurka ke bai wa hukumar lafiya ta duniya WHO.

    Shugaban ya zargi WHO da sakaci wajen yaki da annobar, sai dai kasashen duniya da dama na cewa rike kudin yayin da ake cikin wannan hali ba shine mafita ba.

    Manyan kasashen duniya da basa ga-maciji da Amurka, wato Russia da China na cikin masu sukar.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Zhao Lijian ya ce kasar ta yi matukar damuwa da wannan mataki da Amurka ta dauka.

    A cewarsa: "Ba shakka zai janyo nakasu ga kokarin hukumar lafiya ta duniya, kana makarkashiya ce ga kokarin da kasashen duniya keyi na kawo karshen wannan annoba"

    Kafofin yada labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa da dama daga cikin jami'an gwamnatin Mr Trump basu goyi da bayan matakin da ya dauka ba.

  4. COVID-19: Yadda ake wanke hannu, Ku kalli wannan bidiyon na dakika 56 domin ganin yadda ake wanke hannaye.

  5. Coronavirus: Halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

    • Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum milyan 74 da ke yankin Larabawa ke fuskantar hatsarin kamuwa da cutar korona saboda ba su da wuraren wanke hannu.Kimanin mutum milyan 87 kuma ba su da ruwan sha a gidajensu al'amarin da ya tilasta musu dibar ruwan a wuraren da jama'a ke diban ruwa. Hakan kuwa inji hukumar ta Lafiya ta Duniya yana kara janyo musu kamuwa da cutuka.
    • Hukumomi a Qatar sun yi wa wasu 'yan cirani kawanya sannan suka tasa keyarsu bayan an shaida musu cewa za a yi musu gwajin cutar korona kamar yadda kungiyar Amnesty International ta shaida. Kungiyar dai ta tattauna da mutum 20 daga Nepal wadanda suka ce an tsare su tare da daruruwan wasu a watan Maris. Mutanen dai sun yi zargin cewa an tsare su a wuraren tsare jama'a har zuwa wasu 'yan kwanaki kafin a dora su a kan jirgi. Gwamnatin Qatar ta ce jami'an nata sun gano daidai kuwar mutanen da ke gudanar da al'amura ba bisa ka'ida ba.
    • Alkaluman masu mutuwa saboda cutar korona sun yi kasa a rana ta biyu a jere, inda suka kasance kasa da mutum 100 a kullum. Ma'aiaktar Lafiyar kasar ce ta ce mutum 94 sun mutu a awanni 24 da suka gabata inda yawan mamata a kasar ya zama 4,777.
  6. Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi

  7. Coronavirus: Duniya za ta shiga matsin tattalin arziki mai muni tun bayan shekara 90

    Tattalin arzikin duniya zai ragu da kasha uku cikin 100 a wannan shekarar yayin da na kasashe a fadin duniya ke raguwa cikin saurin da ba a taba ganin irinsa ba a baya-bayan nan, in ji Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF.

    IMF ya bayyana durkushewar tattalin arzikin a matsayin mafi muni tun matsin tattalin arziki da aka shiga a duniya a shekarun 1930, wato Great Depression.

    Asusun ya ce annobar ta jefa duniya cikin “rikicin da bai da tamka”.

    Sannan ya kara da cewa idan annobar ta dade ba a shawo kanta ba, gwamnatocin kasashe da manyan bakunan kasashe za su wahala kafin su farfado da tattalin arzikin.

    Gita Gopinath, babbar jami’a a bangaren tattalin arziki a IMF, ta ce matsin da aka shiga zai wawure dala tiriliyan tara daga arzikin da aka samar a duniya a shekara biyu masu zuwa.

  8. Bayanai na baya-bayan nan a Gabas Ta Tsakiya

    • Kusan mutum miliyan 74 ne a yankin da ake karancin ruwa a kasashen Larabawa suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar korona saboda ba su da hanyar samun ruwan da za su dinga wanke hannayensu da shi.
    • Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa kusan mutum miliyan 87 kuma ba su da ruwan sha a gidajensu, al'amarin da ke tursasa musu debo ruwa a wuraren cunkoson jama'a kuma hakan barazana ce ta kamuwa da cutar a gun su.
    • Hukumomi a Qatar sun sallami ma'aikta 'yan ci trani da dama bayan da suka shaida musu cewa za a yi musu gwajin Covid-19, a cewar kungiyar kare hakkin da adam ta Amnesty International. Kungiyar ta ce ta yi hira da mutum 20 'yan Nepal da suka ce an kore su a watan Maris tare da wasu mutum 100. Sun yi zargin cewa an tsare su a wasu cibiyoyi cikin yanayi marar kyau tsawon kwanaki, kafin daga bisani a sanya su a jirgi zuwa kasashensu. Qatar ta ce jami'anta sun gano ''mutane na yin abubuwan da aka haramta.''
    • A Iran kuwa, kwana biyu kenan a jere ana samun raguwa a yawan mutanen da ke mutuwa kullum zuwa kasa da 100. Ma'aikatar Lafiya ta ce mutum 94 sun mutu cikin sa'a 24 da suka gabata, abin da ya jawo yawan wadanda suka mutu ya kai 4,777
  9. Me coronavirus take yi wa jikin dan adam?

    A watan Disambar 2019 ne cutar korona ta fara bulla a China, amma zuwa yanzu kowace kasa a duniya na fama da annobar ta Covid-19.

    Ga mutane da dama, su kan yi rashin lafiya sama-sama ne, amma cutar kan kashe wasu kuma.

    To ta yaya cutar ke shiga jikin mutum, sannan ta yaya ake warkewa?

    Ku latsa nan don karanta amsoshin wasu tambayoyi da kuka aiko mana da kuma yadda ake warkewa daga cutar.

  10. COVID-19: Mutanen da suka mutu sun zarta 3,000 a Jamus

    Mutanen da suka mutu sanadin kamuwa da cutar korona sun zarta 3,000 a Jamus 3,000.

    Cibiyar yaki da cututtuka ta Robert Koch Institute da ke kasar ta ce mutum 285 daga cikinsu sun mutu ne a kwana daya da ya wuce, abin da ya sa alkaluman wadanda suka mutu suka kai 3,254.

    Ya zuwa yanzu an tabbatar mutum 127,584 na dauke da cutar korona a kasar, a cewar alkaluman baya bayan nan.

    Nan gaba ranar Laraba, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tattauna da shugabannin lardunan kasar a kan ko zai yiwu a sassauta wasu daga cikin matakan da aka dauka don dalike yaduwar cutar ta korona.

    Kasashe da dama a Turai ciki har da Austria da Denmark sun kyale dalibai su koma makaranta.

  11. Coronavirus: Yara sun koma makaranta a Denmark

    Kananan yara wadanda basu wuce shekaru 11 ba sun koma makarantun rainon yara da na firamare a duk fadin Denmark, a yayin da gwamnatin kasar ta kasance ta farko a Turai da ta sassauta dokar hana fita kan coronavirus.

    Fira Minista Mette Frederiksen ta yi maraba da yara 'yan makaranta lokacin da suka koma azuzuwansu a babban birnin kasar Copenhagen.

    Denmark na cikin kasashen Turai na farko-farko da suka sanya dokar zaman gida, inda aka rufe makarantu ranar 12 ga watan Maris.

    An samu raguwar masu kamuwa da cutar korona a kasar ko da yake masu suka suna ganin hakan na da hatsari.

  12. Gwamna zai raba wa talakawa giya a tallafin Covid-19

    Gwamnan Nairobi, babban birnin Kenya, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya sanar cewa zai raba wa talakawa giya a cikin kayan abincin da zai ba su bayan da gwamnati ta tilasta musu zaman gida domin dakile yaduwar cutar korona.

    Gwamna Mike Sonko ya bayar da sanarwar ce a taron manema labarai da ya gudanar ranar Talata kuma tun daga lokacin ne ake ta yama-didi da batu a shafukan sada zumunta bayan da ya ce "zan bayar kananan kwalaben giya samfurin Hennessy a cikin kayan abincin da zan bai wa mutanena".

    "Binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya da hukumomin lafiya da dama suka gudanar ya nuna cewa barasa tana taka rawa wajen kashe coronavirus da ma sauran cutukan da kwayar cuta ke haddasawa," in ji shi.

    Gidan talbijin na Citizen TV ta wallafa sakon Twitter na bidiyo wanda ya nuna gwamnan yana yin kalaman:

    Shafukan sada zumunta a Kenya sun yi ta zolayar gwamnan bisa kalaman nasa.

    Da ma dai Gwamna Sonko ya shahara wajen janyo ce-ce-ku-ce. A baya an zarge shi da safarar miyagun kwayoyi da halasta kudin haramun, ko da yake ya musanta.

    Hukumar gidan yarin kasar ta zarge shi da tserewa daga gidan yari mai matukar tsaro shekara 20 da suka gabata.

  13. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum biyar sun kamu da coronavirus a Kano

    Ma'aikatar Lafiya ta jihar Kano da ke Najeriya ta ce karin mutum biyar sun kamu da cutar korona a jihar.

    A sakon da ya wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ya zuwa karfe 10:25 na safiyar Laraba, adadin masu dauke da cutar a Kano ya kai tara.

  14. Me ya sa Trump ya dakatar da bai wa WHO tallafi?

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai dakatar da tallafin kudin da kasarsa take bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, saboda "ta gaza aiwatar da ayyukan da suka wajaba a kanta " a matakin da ta dauka na dakile cutar korona.

    Ya zargi Hukumar da yin rufa-rufa kan yaduwar cutar bayan ta bulla a China, sannan ya ce dole ne a dauki mataki a kanta.

    Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa "wannan ba lokaci ba ne" da ya kamata a dakatar da bai wa Hukumar Lafia ta Duniya kudin gudanar da ayyukanta.

    Mr Trump yana shan kakkausan suka kan yadda ya bullowa batun dakile cutar korona.

    Ya so ya rage kaifin sukar da ake yi masa cewa ya ja kafa sosai wajen daukar matakin dakile cutar korona inda ya ce a watan Janairu ya dauki matakin takaita masu shiga Amurka daga China.

    Ya zargi Hukumar Lafiya ta Duniya da zama 'yar amshin-shata ta China.

    Mr Trump ya shaida wa taron manema labarai a fadar White House ranar Talata cewa: "Ina umartar gwamnatina ta dakatar da bayar da tallafin kudin sai mun sake nazari kan rawar da Hukumar Lafiya ta duniya ta taka wurin yin rufa-rufa kan yaduwar cutar korona."

    Amurka ce kasar da ta fi bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya tallafi inda a shekarar 2019 ta ba ta tallafin fiye da $400m.

  15. Labarai da dumi-dumi, Mutum daya 'ya warke daga covid-19 a Kaduna'

    Gwamnatin Kaduna da ke Najeriya ta ce mutum daya cikin mutum shida da suka kamu da cutar korona ya daga cutar a jihar.

    Sakon da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnan jihar ranar Laraba ya ambato kwamishiniyar lafiya ta jihar Dr Amina Mohammed-Baloni tana cewa tuni aka sallami mutumin daga cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta jihar.

    Ta ce an sallami mutumin ne bayan a karo na biyu an yi masa gwajin cutar ranar Talata wanda sakamakonsa ya nuna ya warke daga cutar.

  16. Muhammad Babandede 'ya warke daga COVID-19'

    Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede ya gode wa mutanen da suka yi ta yi masa addu'a har ya samu sauki daga cutar korona.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Babandede ya ce sakamako na biyu na gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ya warke daga cutar.

    "Wannan nasara ce daga Allah, muna gode masa da ya ba mu dama muka shiga irin wannan hali wanda ya zarta ilimina da kuma aikin gwamnati," in ji shugaban na hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.

    Lokacin da cutar ta kama shi, ya sanar da cewa zai killace kansa na makonni biyu kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta umarta.

  17. Yadda ‘yan sandan Najeriya suka kama mace mai garkuwa da mutane

    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wata mace mai shekara 28 da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a jihohin arewacin kasar.

    A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Tatala, wanda kakakinta Frank Mba ya sanya wa hannu, rundunar ta ce matar mai suna Fatima Garba na cikin gungun masu garkuwa da mutane da suka addabi jihohin Sokoto, Kebbi da kuma Kaduna da ke arewacin kasar.

    “Fatima ta amince cewa ta kwashe shekara daya tana bai wa masu garkuwa a mutane makamai, inda ake biyanta kudade da dama kan kowanne makami idan an yi amfani da shi wajen yin garkuwa da mutane,” in ji Mr Mba.

    Rundunar ta yi ikirarin cewa wani saurayin Fatima ne ya shigar da ita sana’ar garkuwa da mutane.

    A cewar Mr Mba, jami’ansu sun kama sauran mutanen da ke gungun, wadanda suka hada da Samaila Usman, Mohammed Ibrahim, Mohammed Agali, Dahiru Bello, Shamsu Mohammed, Mohammed Usman, Umar Abdullahi, Buhari Abubakar da kuma Abubakar Garba.

    Ya ce sun kama makamai da dama daga wurinsu.

  18. Coronavirus ta kashe mutum sama da 125,000

    Alkaluma na baya bayan nan sun nuna cewa a fadin duniya mutum 126,539 ne suka mutu sanadin cutar korona, wacce take sarkafe numfashi.

    Amurka ita ce kasar da aka fi mutuwa inda cutar ta yi ajalin mutum 25,992, Italiya tana biye mata da mutum (21,067), Spaniya na da mutum(18,255), Faransa tana da mutum (15,729) , sai kuma Birtaniya inda mutum (12,107) suka mutu

    China, inda cutar ta samo asali, ta ce mutum 3,345 ne suka mutu sanadin cutar ta covid-19.

  19. Budewa

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da wannan lokaci.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Za ku san halin da ake ciki game da annobar coronavirus, wacce ta buwayi duniya.

    Kafin nan, muna kira a gare ku da ku ci gaba da bin shawarwarin manasa lafiya, kamar yawaita wanke hannayenku da yin nesa-nesa da juna da kuma kaurace wa shiga taron jama’a, da sauransu.