Rufewa
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen kawo muku bayanai kai tsaye dangane da halin da ake ciki a Najeriya da sassan duniya kan cutar korona. Da fatan za ku sake kasancewa da mu a gobe Alhamis. Allah ya ba mu alkairinsa.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Usman Minjibir
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen kawo muku bayanai kai tsaye dangane da halin da ake ciki a Najeriya da sassan duniya kan cutar korona. Da fatan za ku sake kasancewa da mu a gobe Alhamis. Allah ya ba mu alkairinsa.
Ministan birnin tarayya, Abuja, Malam Muhammad Bello ya sanar da cewa an sallami mutum uku daga inda ake killace da su bayan sun warke daga cutar korona.
Ministan wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter ya ce yanzu haka adadin mutanen da aka sallama a Abuja 23 ne a ranar 15 ga watan Afrilu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Asusun bada lamuni na duniya IMF ya sanar da cewa tattalin arzikin kasashen duniya zai yi mummunar tabarbarewar da ba a taba ganin irinta ba tun bayan 1930 sanadiyyar cutar Coronavirus.
A wani hasashe da ya gudanar kan tattalin arzikin 2020, asusun ya jaddada cewa kasashen Afrika da ke yankin kudu da hamadar sahara na daga cikin wadanda za su fi jin wannan radadi musamman Najeriya.
This comes as the fund approved debt relief for 19 African countries to get access to grants in order to mitigate the impact of Covid-19 pandemic
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da asusun na IMF ya amince da bai wa kasashen Afirka 19 bashi domin samun zarafin yakar cutar korona.

Asalin hoton, Getty Images
A cewar hukumar Lafiya ta Duniya kashi 13 cikin dari na wadanda ke dauke da cutar korona a kasar Masar ma’aikatan lafiya ne.
Likitoci na rokon gwamnatin kasar ta samar musu kayan aiki don kare lafiyarsu ta yadda za su dakile cutar a asibitocin da lamarin yafi kamari.
Masar wadda ita ce kasar Larabawa mafi yawan jama’a ta sanar da cewa kawo yanzu fiye da mutane dubu biyu ne cutar korona ta kama.
Hukumomin kasar dai sun hana fita da daddare a wani mataki na hana bazuwar cutar inda za ka iske tituna babu kowa amma kuma da safe sai ka ga ana ci gaba da hada-hada.
Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, G20, sun amince su dakatar da karbar basukan da suke bin kasashe matalauta domin ba su damar yaki da annobar korona.
Ministan kudi na Jamus Olaf Schols, ya kira matakin a matsayin sadaukarwa mai cike da tarihi.
Haka kuma kungiyar ta bukaci bangarori masu zaman kansu su dauki irin wannan mataki don taimaka wa kasashen.
To sai dai wannan wani dan jinkiri ne kawai na biyan kudin, amma za su kara neman a biya kudin nan da 2022 ko 2024.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Gebreyesos, ya bayyana rashin jin dadinsa, game da matakin shugaban Amurka na janye tallafin da kasarsa ke bai wa hukumar.
Ya ce hukumar za ta yi aiki kafada da kafada da sauran kasashen da ke aiki da ita domin cike gibin kudaden.
Mista Tedros ya ce "a shirye muke mu hidimta wa jama'ar duniya, sadaukarwa ita ce babbar ka'idar yaki da cutar Korona.
A ranar Talata ne dai shugaba Trump ya sanar da matakin dakatar da tallafin, bayan da ya zargi hukumar Lafiya ta Duniya WHO da hada baki da China wajen yin rufa-rufa a kan cutar.
Rundunar `yan sanda kasa da kasa ta ce ta yi nasarar dakile wani yunkurin wasu kamfanoni na bogi, wadanda suka so su damfari mahukunta a Jamus yuro miliyon daya da rabi a wata kwangila ta samar da kyallayen nan da ake kare baki da hanci.
Rundunar ta bayyana cewa `yan damfaran suna da alaka da Najeriya.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, `yan damfarar sun yi amfani ne da wani shafinsu na intanet da adireshinsu na email duka na bogi, wanda yake kama da na wani sanannen kamfanin gaske a kasar Spaniya, wanda ke yin kyallayen kare fuska da su.
Ganin yadda ake fama da karancin kayan aiki a bangaren kiwon lafiya a duniya sakamakon yakin da ake yi da annobar korona , sai `yan damfarar suka dinga yin kutse cikin adireshin email din kamfanin Spaniyan suna damfarar al`umma, inda suke shigar karya a shafin nasu, sannan su yi cinikin samar da kaya har da karbar kudin sumin tabi ko adibas.
Bincike dai ya gano cewa gabannin tare kudin, har `yan damfarar sun ware yuro 500,000 daga cikin kudin, an tura Burtaniya, wanda daga can za a tura wani asusun banki a Najeriya.
A halin da ake ciki dai kamar yadda sanarwar ke cewa an kama mutum biyu daga cikin wadanda ake zargi da yunkurin damfarar, sannan ana ci gaba da farautar ragowar.

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Faransa ta bayyana cewa yawan mutanen da suka mutu a kasar sun zama 17,167.
An samu karin mutum 500 kan 10,643 daga cikin wadanda suka mutu a asibiti a awanni 24 da suka gabata.
Sai dai yawan wadanda ake kwantarwa ta ragu a karon farko. Har wa yau, yawan mutanen da ke kwanciya a sashen kulawar gaggawa na ci gaba da raguwa.
Mutum 6,524 sun mutu a gidan kula da tsaffi.
Shugaban majalisar Tarayyar Afirka, Moussa Faki ya yi Alla-wadai da kudirin shugaba Donald Trump na Amurka na dakatar da tallafi ga Hukumar Lafiya ta Duniya.
Mista Faki wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya bayyana aniyar Trump da 'abin takaici', inda ya ce a yanzu ne jama'a suke bukatar hukumar a yakin da duniya ke yi da cutar korona.
Mista Trump dai ya ce hukumar ta Lafiya ta Duniya ta gaza wajen yaki da cutar korona.
Mista Faki ba shi ne mutum na farko da ya soki kudirin Donald Trump ba.
Attajirin nan mai kudin duniya, Bill Gates shi ma ya yi Alla-wadai da barazanar Mista Trump.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
A yau ne alkaluma suka nuna yawan masu dauke da cutar korona sun kai mutum milyan biyu a fadin duniya, inda Amurka kadai ke da mutum 600,000 kamar yadda jami'ar Johns Hopkins University ta fadi.
Ana hasashen cewa alkaluman ka iya karuwa duk da cewa kowacce kasa na da naa salon yin gwaje-gwajen cutar.
Wannan dai na zuwa 'yan sa'o'i kafin Tarayyar Afirka ta fitar da alkaluman masu dauke da cutar a nahiyar Afirka.
Tarayyar ta ce kawo yanzu akwai 'yan nahiyar fiye da dubu 16 da suka kamu da cutar ta korona.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce sun sallami mutum 16 daga cibiyar killace masu dauke da cutar Korona a Legas.
Gwamnan wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter ya ce mutanen sun kunshi maza guda 14 da mata guda 2.
Ya kara da cewa a cikin mutum 16 din, uku 'yan kasar waje ne da suka hada da dan Birtaniya da China da kuma Pollland.
Hakan na nufin adadin wadanda suka warke daga cutar sun kai 115.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Tarrayar Afrika ta ce mutum fiye da dubu 16 ne suka kamu da cutar korana a kasashen Afrika yayin da sama da 870 suka rasa rayukansu.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya bayar da sanarwar Amurka za ta dakatar da tallafin da kasarsa ke bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya, a kan zargin cewa ta gaza wajen aiwatar da alhakin da ya rataya a wuyanta na dakile bazuwar cutar korana da tasamo asali a kasar China.
A yau da safe ne yara 'yan makarantar firamare da sakandare suka koma makaranta, wata guda bayan rufe makarantun da kasar ta rufe sakamakon tsoron yaduwar cutar korona.
Sai dai an ce ba daliban ne za su koma makarantar a lokaci guda ba.
Kasar ta Denmark ta rarraba ranakun komawar, ta kuma kafa ka'idoji masu tsauri na bayar da tazara idan daliban suka koma daukar darussa a azuzuwa.
Akwai dai mutane kimanin dubu shidda da suka kamu da cutar corona a kasar, kuma kimanin dari uku ne suka mutu. Ga fassarar rahoton Richard Hamilton;

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin jiragen sama na Emirate ya soma yi wa matafiya gwajin cutar Korona.
Kamfanin ya sanar a shafukansa na sada zumunta cewa shi ne kamfanin zirga-zirga na farko a duniya da ya soma daukar irin wannan mataki.
Shi dai sakamakon gwajin kan fito ne bayan minti 10 da daukar samfurin jinin Fasinja.
Tuni ma aka soma yin irin wannan gwaji a filin sauka da tashin jiragen sama na hadaddiyar Daular Larabawa, in da ake yi wa matafiyan da kan tashi zuwa kasashen da ke da dokar mallakar takardar shaidar cewa mutum baya dauke da cutar.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akalla kaso 74 cikin dari na mutanen da ke rayuwa a kasashen Larabawa ba sa samun damar mallakar sinadaran wanke hannu abin da ka iya janyo musu barazanar kamuwa da cutar Korona.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce sun hadar da mutane miliyan 14 a Yemen, da miliyan goma a Masar, da akalla miliyan 31 a Sudan.
Rahoton ya kuma janyo hankalin mahukunta a kan cewa kusan mutane miliyan 90 a kasashen ba sa samun ruwan sha a gidajensu, abin da ke tilasta musu amfani da na waje, wanda kuma hakan ke zaman wata barazana ga lafiyarsu.

Asalin hoton, Nigeria Police
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi al'ummar kasar da cewa za ta dauki tsauraran matakai kan mutanen da ke shirya tafiye-tafiye da daddare, wadanda kuma ke ci gaba da karya dokar hana zirga-zirga da aka sa don hana yaduwar cutar korona.
Rundunar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta aike wa manema labarai ranar Laraba.
Sanarwar ta ce wannan gargadi ya zo ne bayan da rundunar ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa kungiyar masu motocin haya da ke zirga-zirga tsakanin jihohi na ci gaba da bujire wa dokar tafiye-tafiye suna ayyuka da daddare.
Sanarwar ta ce shugaban 'yan sanda ya bai wa kwamishinoninsa umarnin tabbatar da bin doka da oda kan takaita zirga-zirgar.
Shugaban 'yan sanda Mohammaed Adamu ya yi kira ga kungiyoyin masu motocin haya da su ja kunnen mambobinsu kan bin dokar gwamnatin tarayya, inda ya ce ''wadanda suka ki bin dokar za su gamu da fushin hukuma.''
A rana ta biyu a jere, adadin wadanda ke mutuwa saboda cutar Korona a Iran ya yi kasa da dari. Alkalumman baya-bayan nan da kakakin ma'aikatar lafiya na kasar ya bayar, sun nuna cewa mutane 94 cutar ta kashe a ranar Talata, abin da ke nuna cewa adadin wadanda suka mutu tun bayan barkewar cutar a kasar ya kai 4777 a kasar.
Kasar Iran na daya daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar a duniya, yayin da alkalumman da ba na hukumomi ba ke nuna cewa adadin wadanda suka mutum ya ma zarce dubu biyar.
A yanzu dai mahukunta a kasar na kokarin sassauta wasu daga cikin dokokin da suka kakaba, don bai wa harkokin kasuwancin da ba sa barazanar janyo karuwar cutar damar cigaba da harkokin su.
Kamar yadda muka ambata a baya, shugaba Trump na Amurka ya ce zai dakatar da bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya kudade gudanarwa bisa abin da ya bayyana da "almubazzarancin da ke wakana."
Kamar dai yadda ta tabbata an fara kai wa hukumar Lafiya ta Duniya ne rahoton bullar cutar korona a ranar 31 ga watan Disamban 2020.
Jadawalin abubuwan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kan korona: