Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Usman Minjibir

  1. Za a yi gwajin riga-kafin covid-19 a kan mutane

    Kafofin watsa labaran China sun rawaito cewa za a yi gwajin riga-kafin cutar korona guda biyu a jikin dan adam.

    Kwanan baya, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa ana gwada fiye da riga-kafin cutar korona 70 a fadin duniya, kuma uku daga cikinsu sun kai matakin gwada su a jikin dan adam.

    Biyu daga cikin ukun, an gwada su ne sa Amurka, yayin da na ukun aka gwada shi a China. Wadannan riga-kafi su ne na hudu da na biyar da suka kai matakin gwaji kan dan adam.

    Ruguguwar da ake yi na samar da riga-kafin cutar korona na nufin ana tsallake ka'idojin da al'adance ake dauka wajen samar da riga-kafin cututtuka.

    Sai dai kamar yadda wakilin BBC James Gallagher ya bayyana a farkon watan nan, samu riga-kafin cutar zai dauki lokaci.

    "Ko da wadannan gwaje-gwaje sun yi nasara, ba a tsammanin kamfanonin magunguna za su soma yin magunguna da yawa ba sai tsakiyar shekarar 2021," in ji shi.

  2. Shah Rukh Khan zai bai wa ma'aikatan lafiya gudunmawar kayan kariya

    Fitaccen tauraron fina-finan India, Shah Rukh Khan, ya ce zai bayar da kayan kariya 25,000 ga ma'aikatan lafiyar da ke fafutukar dakile yaduwar cutar korona a jihar Maharashtra da ke yammacin kasar.

    An yi ta watsa labarai kan tauraron mai shekara 54 watan jiya bayan ya sanar da daukar matakai daban-daban wadanda za su taimaka wajen dakile cutar a India, ciki har da bayar da abinci kyauta da kuma zai bayar da ofishinsa domin a yi amfani da shi wajen jinyar mutane da ska kamu da Covid-19.

    Shah Rukh Khan yana cikin shahararrun mutanen da ake girmamawa a India kuma ya fito a fina-finai fiye da 90.

    Mutum 339 ne suka mutu a India sanadin cutukan da ke da alaka da korona.

  3. Cutar korona: Bayani na baya bayan nan game da Turai

    Kasashen Italiya da Austria sun bar wasu kasuwanni sun bude amma ba baki daya ba, kwana guda bayan Spaniya ta bar ma'aikatan kere-kere sun koma bakin aiki.

    Da ma dai kasuwanni sayar da kayan abinci da kantunan sayar da magunguna a bude suke tun da aka samu bullar cutar

    Ga karin labarai kan hali da ake ciki a Turai:

    • A Italiya ana sake bude wasu shaguna, mako biyar bayan an sanya dokar hana fita: an bude katunan sayar da littattafai da na sayar da kayan jarirai. An bari a ci gaba da kera kwamfutoci da sarrafa takardu. Amma ana barin kasuwancin ne ta hanyar yin la'akari da yankunan da cutar ta fi sauki, sannan ana tsaurara matakai kan kiwon lafiya. A lardin Lombardy da ke arewacin kasar – wanda shi ne cibiyar yaduwar cutar a Italiya– kantuna na ci gaba da kasancewa a rufe. Yanzu adadin mutanen da suka mutu sanadin cutar korona a Italiya ya kai 20,465, adadi mafi girma a Turai, ko da yake adadin masu kamuwa da cutar yana raguwa.
    • Austria na cikin kasashen farko-farko a Turai da suka bi sahun Italiya wajen tsaurara dokar hana fita. Yanzu ta bar lambunan shakatawa da kantunan sayar da kayan kwamfuta da makamantansu su sake budewa. Amma ana bai wa mutane shawara su ci gaba da zama a gidajensu sannan an tilasta wa masu kantuna sanya takunkuman rufe fuska.
    • An samu karin masu dauke da Covid-19 a Rasha, a cewar jami'ai:sun ce mutum sama da 2,774 sun kamu da cutar a kwana daya. inda a jimilla ake da mutum 21,102 da suka harbu da cutar, yayin da mutum 170 suka mutu.
    • A kasar Serbia 'yan sanda sun kama wani mai kula da gidan lura da marasa galihu a birnin Nis, bayan sabbin mutum 140 sun kamu da cutar. An zargi mutumin da barin wasu mutae ka ziyara gidan lura da marasa galihun, inda suka karya dokar hana fita. Zai iya shan daurin shekara 12.
  4. COVID-19: An kama alkali da dan majalisa saboda karya doka

    An kama mutane da dama a kasar Kenya lokacin hutun Easter bayan an same su suna shan barasa a gidajen giya abin da ya ci karo da umarnin da gwamnati ta bayar na zaunawa a gida don dakile yaduwar cutar korona.

    Cikin mutanen da aka kama har da wani dan majalisar dokokin kasar, da alkalin kotun majistiret da 'yan sanda wadanda aka samu a waje suna shan giya.

    'Yan sanda ne suka kai samame a gidajen sayar da barasa da ke babban birni kasar, Nairobi, wadanda aka samu a bude duk da umarnin da aka bayar na rufe su.

    'Yan sandan sun ce sun kai samamen ne bayan an tsegunta musu abubuwan da ke faruwa a gidajen giyar inda suka kuma gargadi 'yan kasar cewa za su ci gaba da kai samame kan irin wadannan wurare.

    Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da mutum na tara ya mutu sanadin cutar ta korona, wacce ya zuwa yanzu ta harbi mutum 208 a kasar.

    Ministan lafiyar Kenya ya ce yanzu gwamnati tana da kayan aikin da za su iya yin gwaji kan mutum 1,000 kowacce rana a yunkurinta na gano masu dauke da cutar.

  5. Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi

  6. An dakatar da kwallon kafa a Burundi saboda covid-19

    Hukumar kwallon kafar Burundi ta dakatar da gasar da ake yi ta kwallon kafa, mako biyu bayan hukumomin lafiya sun tabbatar da bullar cutar korona a kasar.

    Tun da fari, hukumar ta ki dakatar da gasar tana mai cewa ta dauki matakan da za su kare 'yan wasan daga kamuwa da cutar.

    Yanzu dai Burundi ta tabbatar mutum biyar sun kamu da cutar korona.

    Hukumar ta ce bayan nazarin da ta yi ta gano cewa akwai yiwuwar su cimma wa'adin ranar 30 ga watan Mayu domin mika sunayen kungiyoyin da suka yi zarra a gasar ga hukumomin da ke gudanar da gasar kwallon kafa na duniya.

    Ta ce tana sake nazari kan kalandar wasanni kuma za a ci gaba da gasar kafin cikar wa'adin.

    Burundi ce kasar Afirka daya tilo da ke ci gaba da buga gasar kwallon kafa duk da cutar korona.

    Tana cikin kasashen Afirka na karshe da suka sanar da bullar cutar a kasashensu.

  7. Kwana uku a jere ba a samu sabbin masu cutar korona a Abuja ba

    Kwana uku kenan a jere ba a samu sabbin masu dauke da cutar korona a Babban Birnin Tarayyar Najeriya ba.

    Alkaluma na karshe da hukumar yaki da cututtuka a Najeriya, NCDC, ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa an samu sabbin mutum 20 da suka kamu da cutar a jihohin Lagos da Edo da Kano da Ogun da kuma Ondo.

    Gabanin sanarwar ta ranar Litinin, NCDC, ta fitar da sanarwa sau biyu wadanda suka nuna babu sabbin masu dauke da cutar ta korona a Abuja.

    Sai dai duk da haka, Abuja ce ta biyu a Najeriya cikin jihohin da ke fama da cutar korona inda take da mutum 56, yayin da jihar Lagos, wacce ita ce ta daya, take da mutum 189 da suka kamu da cutar ya zuwa ranar Litinin da maraice.

  8. Mutum sama da 450, 000 sun warke daga Coronavirus

    Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka da ke bibiyar yaduwar cutar korona ta ce mutum sama da 450, 000 sun warke daga cutar a duniya ya zuwa safiyar ranar Talata 14 ga watan Afrilu, 2020.

    Jami’ar ta kara da cewa mutum fiye da miliyan daya da dubu dari tara ne suka kamu da cutar, inda ta yi ajalin akalla mutum dubu dari daya da shara tara.

    Ga kasashe goma da suka fi fama da cutar ya zuwa safiyar Talata:

    Spaniya – 170, 099

    Italiya -159, 516

    Faransa – 137, 877

    Birtaniya – 89, 571

    Iran – 73, 303

    Belgium – 30, 589

  9. Barkanmu da warhaka

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka. Da fatan za ku kasance tare da mu domin sanin halin da ake ake ciki dangane da cutar korona, wacce ta addabi kasashen duniya.

    Baya ga batun wannan cuta, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma wasu sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.