Alkaluma daga Belgium sun nuna cewa adadin mutanen da ke mutuwa a kullum sakamakon coronavirus ya karu zuwa 303 ranar Litinin, inda jimulla ake da mutum 3,903 da suka mutu sanadinta.
Wadanda suka mutu sun hada da mutanen da ke gidan gajiyayu da aka zarga da kasancewa dauke da cutar, amma ba a yi musu gwaji ba.
Ko da yake za a iya ganin kamar wadanda suka mutu ba su da yawa idan aka kwatanta da sauran kasashen Turai, amma yawan jama'ar Belgium bai wuce miliyan 11.5. Jamus na da yawan jama'a miliyan 83, kuma mutum kusan 3,000 ne suka mutu sakamakon coronavirus. - don haka a alkalumance mutanen da suka mutu a Belgium ya kusa na Spain da Italiya.
Belgium ta tabbatar mutum 30,000 suka kamu da cutar.