Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Karin mutum 17 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Yadda sojojin Chadi 'suka kashe 'yan Boko Haram' 1,000

      • Marubuci, Mary Harper
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editar Afrika, BBC World Service

    Rundunar sojin Chadi ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 1,000 a wani samame da ta kai yankin Tafkin Chadi.

    Kakakin rundunar sojin Kanar Azem Agouna ya ce an kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu.

    Shugaba Idriss Déby ya ziyarci yankin Tafkin na Chadi. Ya ce babu dan kungiyar Boko Haram ko daya da ya rage a yankin.

    Ya yi takaici kan yadda ya ce an bar Chadi ita kadai take fatattakar mayakan na Boko Haram a fadin Tafkin na Chadi, wanda ke da iyaka da kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

    An kaddamar da farmakin ne bayan da a watan jiya sun kashe dakarun Chadi kusan 100 a harin da suka kai musu a yankin.

    Har yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin sojojin Chadin kuma Boko Haram bata ce komai ba.

  2. Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi

  3. Covid-19: Buhari ya taya Kiristoci murnar bikin Easter

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga Kiristoci su yi koyi da darasin da ke cikin ranar Easter duk da halin da duniya ke ciki na annobar covid-19.

    A sakon da ya fitar domin taya mabiya addinin Kirista murnar ranar ta Easter, Shugaban na Najeriya, ya ce: "Ina mai kira a gare ku da ku yi riko da dabi'u na kirki da da da'a da hakuri da sadaukarwa da kuma mika kai wadanda Yesu Almasihu ya nuna a rayuwarsa a doron kasa".

    "Bikin Easter na wannan shekarar ya zo ne a yayin da duniya ke fama da annobar Covid-19. Wannan abu ne da bai taba faruwa ba a tarihi, inda akasarin Kiristoci suka tsinci kansu wajen yin bikin Easter ba tare da shagulgula da taruwa a coci-coci ba," in ji Shugaba Buhari

    Ya nanata kiran da ya yi a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya ta kafar talbijin inda ya bukaci su dauki matakan kauce wa kamuwa da coronavirus, irin su yawaita wanke hannaye da kauce wa shiga tarukan jama'a da kuma toshe bakinsu da kyalle lokacin da za su yi atishawa da bai wa juna tazara da makamantansu.

  4. Coronavirus ta kashe mutum kusan dubu dari daya

    Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka da ke bin diddigin yaduwar annobar coronavirus, ta ce mutum 95, 745 sun mutu daga cutar a fadin duniya zuwa safiyar ranar Juma’a 10 ga watan Afrilu, 2020.

    Jami’ar ta kara da cewa an tabbatar mutum sama da miliyan daya da dubu dari shida sun kamu da coronavirus.

    Kazalika mutum fiye da 355, 000 sun warke daga covid-19.

    Ga kasashe goma da suka fi fama da cutar ya zuwa safiyar Juma’a:

    Spaniya – 153,222

    Italiya -143,626

    Faransa – 118, 785

    Iran – 66, 220

    Birtaniya – 65, 872

    Belgium – 24, 983

  5. Budewa

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Sashen Hausa na BBC ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan kasance tare da ku tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Kada ku manta cewa za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.