Karshen rahotannin kenan
Jama'a rahotannin namu sun zo karshe, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ne ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail
Jama'a rahotannin namu sun zo karshe, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ne ke cewa mu kwana lafiya.
Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a Najeriya ya karu zuwa 305 bayan wasu 17 sun harbu a yau Juma'a, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka.
Daga cikinsu, takwas a Jihar Legas suke - wadda yanzu take da 163 kuma mafi yawa a kasar.
Jihohin da aka samu sabbin wadanda suka kamu:
Lagos - 8
Katsina - 3
Abuja - 2
Neja - 1
Kaduna - 1
Anambra - 1
Ondo - 1
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ce daga yanzu dakarun kasar, wadanda suka taka rawa a yaki da masu ikirarin jihadi, ba za su sake shiga wani yaki da ta'addanci ba a wata kasa daban.
Wannan sanarwa tasa ta zo ne bayan rundunar sojojin kasar ta ce ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 1,000 a yankin Tafkin Chadi yayin wani samame, inda sojojin kasar 50 suka mutu.
Sanye da kakin soja yayin da yake yi wa manyan hafsoshin soja jawabi, Shugaba Deby ya ce dakarun kasarsa sun tafka asara mai yawa yayin yaki da masu ikirarin jihadi a yankin.
Shugaban ya zargi sauran kasashe da cewa ba sa taka rawar da ta kamata sannan ya ce sojojinsa ba za su sake shiga wata kasa ba.
Idan har matakin ya tabbata, za a samu babban gibi a yaki da kungiyin jihadi.
Akwai dakarun kasar Chadi - wadnda suka fi na makobtansu kwarewa a yankin - da aka tura su Najeriya da Jamhuriyar Nijar domin yakar Boko Haram.
Har wa yau, akwai su a kasashen G5 da ke aikin kare iyakokin kasashen yankin Sahel sannan suna cikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali.
Faransa ta bayar da rahoton mutuwar 987 sakamakon annobar coronavirus.
Jumullar adadin ya zama 13,197 a kasar baki daya.
Sai dai marasa lafiyar da ke dakin kulawar gaggawa sun ragu a rana ta biyu a jere, kamar yadda babban jami'in lafiya Jérôme Salomon ya fada wa manema labarai.
Mace-macen sun karu da mutum 554 zuwa 8,598 a asibitoci sannan wasu 433 suka karu zuwa 4,599 a gidaje, inda tsofaffi da masu larura ta musamman suka mutu.

Asalin hoton, Getty Images
Duniya na fuskantar barazanar "sake barkewar" annobar coronavirus idan kaashe suka yi saurin dage dokokin hana taruwar jama'a, a cewar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce abu ne mai matukar muhimmanci kasashe su tanadi hanyoyin dage dokokin cikin nutsuwa.
"WHO ma tana son ta ga an dage dokokin zaman gida kamar kowa," in ji Dr Tedros.
Ya kara da cewa: "A gefe guda kuma dage dokokin lokaci guda ka iya jawo sake barkewar cutar. Sake barkewarta zai iya zama mai hadari kamar yadda ta fara idan ba a dauki matakan da suka dace ba."

Asalin hoton, OPEC
Ministocin mai na kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya na gudanar da taronsu domin duba yadda za a rage radadi annobar coronavirus kan harkar man fetur a duniya.
Annobar dai ta sanya farashin danyen man fetur ya yi faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama.
Suna gudanar da taron ne ta na’ura domin gudun yada cutar.
Kasashen na G20 dai su ne suka fi amfani da man fetur a duniya saboda karfinsu na masana’antu amma annobar ta durkusar da harkokin masana’antu don haka man ya yi kwantai a kasuwar duniya kuma farashinsa ya fadi lamarin dake barazana ga tattalin arzikin duniya musamman na kasashe masu samar da man.
Sakatare Janar na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC Muhammad Sanusi Barkindo a jawabinsa ga taron, ya bukaci manyan kasashen da su taimaka a yunkurin da ake yi na samar da daidaito a kasuwar man.
Ya ce barazanar da ake fuskanta ta fi ta koma-bayan tattalin arzikin duniya da aka fuskanta a 2008. ‘Muna fuskantar matsalar da ba a taba ganin irinta ba’ inji Barkindo.

Asalin hoton, OPEC
Amma ya bayyana kawarin gwiwar cewa za a hada karfi da karfe domin dakile matsalar.
Shi ma Sakataren Makamashi na Amurka Dan Brouilletle wanda ke halartar taron ta na’ura, ya ce kasuwar mai a duniya ta fada mawuyacin hali matuka.
Ya ce annobar Coronavirus da kuma kwantan mai a kasuwa, sun hadu sun haifar da mummunan yanayi.
"Wannan lokaci ne ga dukkan kasashe su duba gaske, abin da kowacce zata iya yi domin gyara rashin daidaito da ke akwai a kasuwa tsakanin adadin man da ake samarwa da wanda ake bukata".
Ya ce dole kasashe su dauki matakan rage kwantan man a duniya.
Ana dai sa ran a karshen taron, manyan kashen za su bayyana irin matakan da za a dauka domin kyautata kasuwar man da kuma tallafa wa tattalin arzikin duniya.
Wannan taro na na G20 dai na gudana ne kwana daya bayan da kungiyar OPEC da kasar Russia suka cimma yarjeniyar rage adadin man da ake kai wa kasuwa da ganga muliyan goma a kowace rana da nufin farfado da farashin man a duniya, lamarin da Sakataren OPEC Muhammad Sanusi Barkindo ya bayyana a matsayin gagarumar nasara.
Adadin wadanda annobar Covid-19 ta kashe a fadin duniya ya kai 100,376, a cewar alkaluman Jami'ar Johns Hopkins.
Italiya ce ta fi yawan wadanda suka rasun, sai kuma Amurka da ke biye mata da kuma Sifaniya.
Muna kawo muku bayanai kai-tsaye a shafinmu na Facebook daga shugaban hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya.
Yana magana ne kan irin matakan da suke dauka na yaki da coronavirus a kasar.

Asalin hoton, Getty Images
An gargadi gwamnatoci a Najeriya musamman na jihohi da cewa lokaci bai yi ba na dage dokar hana tarukan bikin Easter da na sallar Juma'a a lokacin da ake faman yaki da annobar cutar Covid-19.
Wata kungiya mai sa ido kan harkokin lafiya a Najeriya mai suna Health Sector Reform Coalition (HSRC) ce ta yi wannan kira a ranar Juma'a, inda ta ce ta fuskanci wasu gwamnoni na dage dokar hana tarukan addini a kasar.
A sanarwar da ta fitar, gamayyar kungiyoyin sa-kai fiye da 100, ta ce duk da cewa tana mutunta al'amuran addini da kuma shugabannin addinai a Najeriya, "hujjojin da suka bayyana a yanzu ba su ba da damar yin irin wadannan taruka ba".
"Abin takaici, ba mu da wani zabi a irin wannan lokacin. Hujjojin kimiyya daga kasashe da suka ci gaba da masu tasowa sun nuna cewa kaurace wa taruka da bayar da tazara da wanke hannu da kuma kiyayewa yayin shakar numfashi ne hanya mafi kyau ta kauce wa harbuwa da Covid-19," in ji sanarwar.
Saboda haka ne kungiyar ta yi kira ga gwamnonin jihohi da su guji cire wadannan dokoki har sai hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta bayar da shawarar yin hakan.
Sannan ta shawarce su da su kara kaimi wurin raba kayan agajin rage radadin da dokar hana fitar ke haifarwa ga mutane.
Karin mutum uku sun kamu da cutar coronavirus a Jihar Katsina, a cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari.
Gwamnan ya ce mutum ukun da suka kamu iyalan likitan nan ne da ya mutu a garin Daura sakamakon cutar - matarsa daya da yara biyu.
Kazalika an saka dokar hana fita a garin na Daura.
Gwamna Masari ya ce: "Duk da cewa ana ci gaba da bin sawu da kuma gwada jinin mutane a Daura, an saka dokar hana fita a garin, wadda za ta fara aiki da karfe 7:00 na yammacin gobe [Asabar]."
Amma za a zabi wasu kantunan sayar da magunguna da kuma wurin cefanen kayan abinci uku-uku wadanda mutane za su rika zuwa cikin tsauraran matakan sa ido, a cewar gwamnan.
Har wa yau, gwamnatin Katsina za ta tallafa wa mutanen Daura a lokacin da wannan doka za ta yi aiki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Najeriya ta bayyana cewa ta bi sahun kasashn kungiyar OPEC masu arzikin man fetur wajen rage adadin man da take hakowa a kowacce rana domin taimakawa wajen habaka farashinsa a kasuwar duniya.
Karamin ministan man fetur a kasar, Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.
Ministan ya ce daga yanzu Najeriya za ta rika hako gangar mai miliyan 1.412 a kowacce rana da miliyan 1.495 da miliyan 1.579 a tsakanin watannin Mayu zuwa Yuni, Yuli zuwa Disamba da kuma Janairun 2021 zuwa Afrilun 2022.
Har wa yau, Najeriya ta bayyana fatanta cewa "idan abin ya dore" farashin man zai karu da akalla dala 15 a kan yadda yake a yanzu.
Bisa kiyasin hako danyen mai na Oktoban 2018, a yanzu Najeriya na hako ganga miliyan 1.829 a kowacce rana.
Wannan ragin ya biyo bayan yarjejeniyar da kasashen na OPEC tare da wasu kasashe masu arzikin fetur na rage ganga miliyan 10 na adadin da suke hakowa a kullum a yunkurinsu na farfado da darajar man.
Sai dai har yanzu yarjejeniyar ba ta kullu ba sakamakon jinkirin da kasar Mexico ta yi na saka hannu a kanta.
"Muna fatan idan wannan yarjejeniyar mai dumbin tarihi ta tabbata za a samu karuwar farashin mai da akalla dala 15 kan kowacce ganga a nan kusa," in ji Timipre Sylva.
Hukumar lafiya ta NHS a Ingila ta ce karin mutum 866 sun mutu sakamakon harbuwa da cutar Covid-19.
Wannan ya sa jumullar adadin wadanda suka mutu a Ingila ya zama 8,114.
Daga cikin wadanda aka bayyana mutuwar tasu a yau, 117 sun mutu ne ranar 9 ga Afrilu, 720 kuma daga 1 zuwa 8 ga watan Afrilu, sai kuma 29 da suka mutu a watan Maris.

Asalin hoton, Saudi Gazette
Saudiyya ta kara wa'adin da ta bai wa 'yan kasarta mazauna kasar waje da suke son komawa gida zuwa 14 ga watan Afrilu, a cewar wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.
"An dauki matakin ne bisa umarnin Sarki Salman da kuma Yarima Mai Jiran Gado na dawo da 'yan kasa gida da suke bukatar dawowa," in ji Ministan Harkokin Waje Yarima Faisal Bin Farhan, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Ita kuma ma'aikatar harkokin wajen ta wallafa a shafinta na Twitter cewa: "Wa'adin da aka saka na dawowar 'yan kasa gida an dage shi har zuwa 14 ga Afrilun 2020 da karfe 5:00 na yamma."
Mutum 3,287 ne suka harbu da annobar cutar coronavirus a Saudiyya bayan ta samu mutum 355 da suka kamu a ranar Alhamis.
Mutum 44 ne suka mutu sakamakon cutar.
Kwamishinan lafiya na Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya ya gargadi mazauna birnin su shirya domin karbar bakuncin ma'aikatan lafiya wadanda za su rika bin su gida-gida don yin tambayoyi kan alamomin coronavirus.
Ma'aikatan lafiyar za su "gudanar da tambayoyi kan alamomi irin su tari da mura da zazzabi", in ji Farfesa Akin Abayomi a sakon Twitter da gwamnatin Lagos ta wallafa.
Farfesa Abayomi ya ce za a gudanar da tambayoyin ne "a matsa kaimin da ake yi wajen gano masu dauke da Covid-19".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, murnar cika shekara 63 a duniya.
Sanarwar da Femi Adesina, kakakin shugaban kasar ya fitar ranar Juma'a, ta ambato Shugaba Buhari yana mai yin alfahari da hamshakin mai kudin na Afirka.
A cewarsa, “Alhaji Dangote yana yin abin da ya dace a lokacin da ake bukatar yin hakan, idan aka yi la'akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen yaki da cutar shan inna da Ebola da kuma Coronavirus da ake fama da ita yanzu, da ma sauran kalubalen da ke fuskantar Najeriya da ma nahiyar Afirka.”
Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya kara wa Dangote koshin lafiya da nasarori a rayuwarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Galibin labaran da ake bayarwa kan coronavirus ba masu dadin ji ba ne. Kowa yana sane da hakan. Don haka wannan labarin da za mu ba ku zai sanya ku murmushi.
Mutumin nan mai shekara 101 wanda ya kamu da coronavirus ya koma gidansa daga asibiti bayan ya warke sarai daga cutar.
Tun da fari an kwantar da Keith Watson, dan yankin Worcestershire, a asibit inda za a yi masa tiyata a kafarsa bayan ya fadi amma sai aka gano ya kamu da Covid-19 bayan yanayin jikinsa ya yi zafi.
"Ya zo domin a yi masa tiyata amma mun furgita bayan mun gano yana dauke da coronavirus," in ji surukursa, Jo Watson. "Mutum ne mai haba-haba."
Wani hotonsa tare da ma'aikatan asibitin Worcestershire da aka wallafa a shafin Facebook ya ja hankalin ma'abota shafukan zumunta inda aka rarraba shi sau fiye da 3,000.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta bude dakin gwajin cutar coronavirus a jihar Kano da ke arewacin kasar.
Malam Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban Najeriya kan shafukan zumunta na zamani ne ya tabbatar da wannan labarin a sakon da ya wallafa a Twitter ranar Juma'a.
"Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bude dakin gwajin covid-19 a asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano. Gwamnatin jihar ta ce nan gaba ba za a rika kai samfur na dukkan mutumin da ake zargi ya kamu da cutar Abuja ba domin kuwa dakin gwajin zai rika gudanar da wannan aiki yanzu," in ji Bashir.
Da ma dai akwai dakunan gwajin a Lagos da Abuja da Edo da Ibadan da Abakaliki da Osun.
NCDC ta ce tana aiki tukuru domin kammala dakunan gwaji a Sokoto da Fatakwal da Jos da Kaduna da kuma Maiduguri.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
An killace manyan birrai saboda fargabar kamuwa da coronavirus.
An dakatar da mutane daga zuwa kallon manyan birrai a Afirka, yayin da kuma aka rufe gidajen ajiye birrai da ke wurare daban-daban.
Ba a sani ba ko manyan birrai ka iya kamuwa da corovirus, amma ana fargabar cewa kusantar su ka iya shafa musu cutar.
An dauki sabbin matakan ne da zummar kare birran daga kamuwa da wannan cuta ta sarkewar numfashi.

Asalin hoton, Getty Images