Coronavirus: An samu raguwar mutuwa a Sifaniya
Mutum 674 ne suka mutu a Sifaniya a rana guda, wanda hakan ya kawo jumullar mace-macen da aka samu a kasar sakamakon coronavirus zuwa 12,4189.
Wannan adadin da aka samu a yau shi ne mafi karanci a wannan makon inda har aka samu raguwa da mutum 135 kan mutuwar da aka samu a ranar Asabar.
A jiya dai mutum 809 ne suka mutu a kasar.
Sifaniya na daga cikin kasashen da coronavirus ta fi addaba a fadin duniya.