Coronavirus: Akwai yiwuwar sakin fursunoni har 4,000 a Birtaniya
Hukumar kula da fursunoni ta Birtaniya ta bayyana cewa akwai yiwuwar sakin fursunoni kusan 4,000 a Ingila da kuma Wales saboda coronavirus.
Sai dai wadanda suka aikata muggan laifuka da kuma fyade ba su cikin jerin mutanen da za a saki a rukunin farko.
Ana sa ran fursunonin da wa'adin zamansu ya rage watanni biyu ko kuma kasa da haka za a saki.
Ana ganin cewa asibitoci za su shiga wani hali idan cutar coronavirus ta ci gaba da bazuwa a cikin fursuna.
A halin yanzu akwai fursunoni 88 da suka kamu da cutar wadanda ke a gidajen yari 29 a fadin kasar.
Akwai kuma kusan fursunoni 1,200 da ake gani sun killace kansu.
Kusan ma'aikatan gidan yari 8,000 ne ba su zuwa aiki sakamakon wannan cuta - kusan kashi daya bisa hudu na ma'aikatan gidan yari a kasar.