Karshen rahotannin kenan
Jama'a nan muka kawo karshen rahotannin.
Mu hadu da safe in Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita
Jama'a nan muka kawo karshen rahotannin.
Mu hadu da safe in Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, EPA
Daga cikin abubuwan da Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wurin taron manema labarai a yau Asabar :

Asalin hoton, @MKKyari
Kamfanin mai na NNPC ya ce ya tara tallafin kusan naira biliyan 21 da zai bai wa gwamnatin Najeriya domin yaki da annobar coronavirus.
Shugaban kamfanin Mele Kyari, wanda ya shaida wa BBC hakan ranar Asabar, ya ce sun tara kudin ne da hadin gwiwar kamfanoni abokan huldarsu.
Kazalika sun bai wa gwamnati asibiti guda biyu domin kula da marasa lafiya. Guda daya yana unguwar Utako da kuma wani a Maitama.

Asalin hoton, Getty Images
Hausawa kan ce likita bokan Turai! Duk da cewa cutar coronavirus sannaniya ce - ganin cewa an yi makamanciyarta a shekarun 2000 - cutar ta 2019 wadda aka yi wa lakabi da Covid-19 na kan wahalar da kwararru a harkar lafiya.
Daga cikin abubuwan da suka gaza ganowa game da cutar zuwa yanzu akwai:

Asalin hoton, Bauchi State Government
Tun daga ranar 27 ga watan Fabrairu da cutar coronavirus ta fara bulla a birnin Legas na Najeriya - bayan zuwan wani dan Italiya birnin - 'yan kasar ke ta kasa kunne domin jin wane ne zai kamu a gaba.
Wannan cuta ta coronavirus ta harbi shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin Najeriya da akalla gwamnoni guda uku na kasar da kuma shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriyar.
Ga wasu daga cikin kusoshin gwamnatin Najeriya da cutar ta harba.
Hukumomin lafiya a kasar Faransa sun ce mutum 441 ne suka mutu a cikin sa'a 24 da suka gabata, jumullar wadanda suka mutu a asibiti sun kai 5,532.
Adadin wadanda cutar ke kashewa ba ya karuwa daga yadda aka saba a baya-bayan nan. Hukumomi sun ce suna bayar da kulawa a gidajen gajiyayyu, inda adadin wadanda suka mutu a nan din ya kai 2,028.
Baki dayan wadanda suika mutu a kasar 7,560 ne. Daga cikin 28,143 da ake kulawa da su a asibiti, 6,838 suna sashen kulawar gaggawa.
Ita kuwa kasar Turkiyya ta ce mutum 501 ne suka mutu a kasar zuwa yanzu sannan kuma adadin wadanda suka harbu ya kusa 24,000.

Asalin hoton, Getty Images
Wadanda suka kamu da cutar coronavirus sun zarta 500 a Kamaru sannan takwas sun mutu sakamakon annobar.
Har yanzu Shugaba Paul Biya bai ce uffan ba ga 'yan kasa game da annobar.
Bayan hoton da ya dauka da wani jakada a watan da ya gabata da kuma wani sakon Twitter da ke shawartar 'yan kasa su yi biyayya ga umarnin likitoci, babu wani bayani daga shugaban mai shekara 87.
Paul Biya bai fiya fitowa bainar jama'a ba sannan an san shi da shafe lokaci mai tsawo a wani kasaitaccen otel a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Salon shugabancin da Paul Biya ke gudanarwa na rashin bayyana kai abin mamaki ne, musamman ga shugaban da ya shafe shekara 37 a kan mulki.
Madugun 'yan adawa Maurice Kamto ya bayyana shurun shugaban a matsayin "babban laifi".
Wani babban jami'i daga jam'iyyar shugaban kasa, Oswald Baboke ya ce hakan alama ce ta hangen nesa.

Asalin hoton, Nigerian Senate
Majalisar Wakilan Najeriya na shirin duba wani kudiri da zai sa a bai wa ‘yan kasar wutar lantarki a kyauta na tsawon wata biyu saboda annobar coronavirus.
Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya ce matakin zai janyo habbakar tattalin arziki ga talakawan kasar wadanda suka fuskanci kalubale saboda Covid-19.
Kudirin shi ne zai kasance mataki na biyu domin ba da tallafi ga talakawan Najeriya bayan da aka ayyana coronavirus a matsayin annoba a duniya.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne a tattaunawar da shugabannin majalisar dokokin kasar suka yi tare da Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed da kuma wasu jami’ai a fannin tattalin arzikin kasar.
Carrie Symonds, budurwar Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson, ta ce ta shafe kwanaki a gado da alamun cutar coronavirus.
Shi kansa Mista Johnson ya kamu da cutar a makon da ya gabata.
Mis Symonds ta kara da cewa ganin alamun cutar yayin da take dauke da ciki "abin damuwa" ne.
Italiya ta tabbatar da karin mutum 681 da suka mutu sakamakon coronavirus, abin da ya kai jumullar adadin zuwa 15,362 a kasar.
Adadin yana dan raguwa a cikin kwana takwas da suka gabata, wadanda ke harbuwa ma adadinsu ba ya karuwa sosai.
Mutum 2,886 ne suka kamu da cutar cikin awa 24 da suka gabata - jumullar wadanda ke dauke da ita a yanzu ya kai 88,274.
Mutum 20,996 ne suka warke, yayin da Italiya da Sifaniya ke da fiye da 124,000 na masu cutar.

Asalin hoton, REUTERS
Wani yaro dan shekara biyar na cikin wadanda suka rasu cikin awa 24 da suka gabata a Birtaniya sakamakon coronavirus, a cewar hukumomi.
Da ma dai yaron majinyaci ne, inda yake fama da wasu cutukan na daban.
Bayanan baya-bayan nan sun nuna cewa mutum 4,313 ne suka mutu a kasar sakamakon cutar bayan 708 sun mutu a rana guda.
Ministan Majalisar Zartarwa Michael Gove ya ce ana kera daruruwan na'urar ventilator - mai taimaka wa marasa lafiya yin numfashi - a kullum sannan kuma ana samo wasu daga kasashen waje.
Ana ta yin gargadi ga mutane da su zauna a gida duk da yanayi mai zafi da ake fama da shi a Birtaniya.
Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce yana samun sauki tun bayan da aka killace shi sakamakon kamuwa da coronavirus.
A wani sakon bidiyo da mahaifinsa ya wallafa a Twitter, ya ce lokacin da aka kai shi cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Gwagwalada a Abuja, ya shiga cikin fargaba da tashin hankali.
Mohammed ya bayyana labaran karya da ake yadawa kan masu dauke da coronavirus a matsayin "abin bacin rai".

Asalin hoton, @FMoCDENigeria
Ma'aikatar Sadarwa a Najeriya ta ce har yanzu ba a fara amfani da sabuwar fasahar intanet ta 5G ba, sabanin wasu ra'ayoyi da ke alakanta 5G din da cutar coronavirus a Najeriya.
Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ne ya jaddada hakan a wata sanarwa da ya saka wa hannu a ranar Asabar, inda ya kara da cewa har yanzu suna kan matakin gwaji da kuma duba tasirin fasahar ga lafiyar 'yan Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da mutane a sassan duniya suka fara zargin cewa fasahar 5G na da alaka da annobar cutar coronavirus, abin da ya sa suka fara lalatawa tare da cinna wa turakun layin intanet wuta.
Kazalika a Najeriya, jama'a na ta bayyana ra'ayoyin goyon baya da kuma suka - har ma da na ba'a - kan fasahar a shafin Twitter, inda aka rika tattauanawa da maudu'in #5GinNigeria.
"Bisa bayanan da ke kan teburina, hukumar National Frequency Management Council (NFMC) wadda ni ne shugabanta, ba ta bayar da izinin kafa fasahar 5G ba a Najeriya," in ji Isa Pantami.
Ya kara da cewa: "An tsinkayar da ofishina kan wasu bayanai da ke alakanta annobar coronavirus da fasahar 5G a Najeriya. Saboda haka nake so na fayyace cewa har yanzu ba a bayar da lasisin kafa 5G ba a Najeriya."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Mutane na lalata turakun samar da layin intanet sakamakon alakanta cutar coronavirus da ake yi da sabuwar fasahar nan ta 5G, duk da cewa hukumomi na cewa babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.
An cinna wa turakun wuta a Sparkhill, Birmingham a ranar Alhamis, sai kuma Melling da Merseyside a ranar Juma'a, duka a Birtaniya.
Kamfanin samar da layin waya a Birtaniya, Mobile UK ya ce alakanta coronavirus da 5G da ake yi "abin damuwa ne".
Gwamnati ta ce "babu wata hujja kwata-kwata ta alaka" tsakanin abubuwan biyu.
A ranar Juma'a, Facebook ya goge wani shafi da ya rika nuna wasu bidiyo da ke nuna yadda turakun 5G ke ci da wuta sannan ya rika ingiza mutane da su ci gaba da yin hakan.
Da take magana a wani sakon Twitter, ma'aikatar kafafen yada labarai na zamani da wasanni ta ce "tana sane da labarin da ake yadawa game da 5G a intanet".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Jami'an kashe gobara sun ce sun kashe wutar da take ci a wani turken 5G a unguwar Melling.
Jami'an na unguwar Midlands sun ce wutar ta kama wani turke ne mai tsawon kafa 70. Sai dai sun ce har yanzu ba su da tabbacin ko turken na 5G ne.
Jumullar wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya mutum 209 ne ba mutum 210 ba, kamar yadda hukumar NCDC ta gyara alkalumanta baya-bayan nan.


Asalin hoton, @LadanSalihu1

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya kara wa'adin rufe iyakokin kasar da makonni biyu da yunkurin kasar na dakile yaduwar Covid-19.
Iyakokin sun hada da na kan tudu da na ruwa da kuma filayen jiragen sama. Umarnin da shugaban ya bayar zai fara aiki ne da tsakar daren Lahadi.
A yanzu haka wasu sassa na Ghana kamar irin su Accra na rufe sakamakon dokar takaita zirga-zirga.
Hukumomi a kasar sun kara matsa kaimi wajen binciko wadanda suka yi mu'amula da masu dauke da cutar a kasar.
Kasar ta Ghana ta samu sama da mutum 200 da suka kamu da cutar inda mutum biyar suka mutu.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yabi kasashe masu tasowa ciki har da Najeriya inda ya ce kasar na taka rawar gani wajen dakile yaduwar coronavirus.
Ya bayyana cewa akwai matakai da Najeriyar ta dauka wanda a ganinsa wasu kasashen da suka ci gaba sun kasa daukar irin matakan.
Ya kuma bayyana cewa kasashe masu tasowa suna bukatar taimako matuka.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatan kamfanin jirgin sama na British Airways na zargin cewa sun kamu da coronavirus a makonni biyu da suka wuce bayan sun shafe sa'o'i da dama cikin jirgin sama.
Kungiyoyin da ke wakiltar ma'aikata da direbobin cikin jirgi na bukatar a dauki mataki domin kare ma'aikatan daga kamuwa da cutar.
Kamfanin jirgin sama na British Airways har yanzu na zuwa wurare kamar New York a Amurka, garin da coronavirus ta fi ta'azzara a fadin Amurka.
Kamfanin jirgin saman ya kafe kan cewa akwai kayayyakin kariya da aka tanadar ga ma'aikatan jirgin kuma akwai wasu matakai da aka dauka na bayar da tazara tsakanin fasinjoji da ma'aikatan cikin jirigi.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan shafe makonni uku a rufe, kasar Sifaniya ta bayyana cewa mutum 809 sun sake mutuwa a kasar a rana guda, jumullar wadanda suka mutu a kasar sun kai 11,744.
A halin yanzu, mutum 124,736 suka kamu da cutar a kasar, hakan ya zarta yawan wadanda cutar ta harba a Italiya.
Yawan mace-mace ya sauko kasa da 900 a karon farko cikin kwanaki uku a Sifaniya