Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce yana samun sauki tun bayan da aka killace shi sakamakon kamuwa da coronavirus.
A wani sakon bidiyo da mahaifinsa ya wallafa a Twitter, ya ce ko da yake lokacin da aka kai shi cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Gwagwalada a Abuja, babban birnin kasar ya fada cikin fargaba da tashin hankali, amma babu abin da ya fi bata masa rai fiye da labaran karya da ake yadawa kan irin su da ke dauke da coronavirus.
A cewarsa, an fi watsa irin wadannan labarai kan irin sa da suka fito daga gidajen 'yan siyasa.
Ya ce yana sa ran kammala wa'adinsa na zaman wurin killace masu dauke da cutar, yana mai cewa "yau ina kwana na 11 zuwa 12, ina fatan barin wurin nan ba da dadewa ba, watakila idan sakamakon gwaje-gwajen da za a yi min suka kasance masu armashi."
Ya jinjina wa ma'aikatan lafiya da ke kula da masu cutar, amma ya bukaci jama'a su ci gaba da daukar matakan kare kansu daga kamuwa da cutar.