Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus ta bulla a kasashen Afirka 26
Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Yadda wannan iftila'i ya shafi wasu
Wani a shafin Twitter ya wallafa bidiyon yadda wannan lamari ya shafi abokinsa inda gidan da yake da kuma motocin gidan duk sun lalace.
An ceto mutum 15
Jami'an Kungiyar Red Cross sun tabbatar wa BBC da cewa an samu nasarar ceto mutum 15 a halin yanzu daga wata makaranta da gininta ya ruguzo kuma suna asibiti ana duba lafiyarsu.
Yadda wasu ke tserewa suna barin yankin da abin ya faru
Tuni wasu da ke zaune a Unguwar Abule Ado suka fara gudun hijira sakamakon firgicin da suka shiga a safiyar yau.
Jami'an hukumar NSCDC sun hallara
Jami'an hukumur tsaro ta NSCDC sun isa wurin da lamarin ya faru.
A halin yanzu suna bincike da kuma duba yadda abubuwa suke kuma ana sa ran za su yi karin bayani.
Wasu mazauna wannan wuri sun shaida cewa akwai gwamman mutane da ba a ceto ba wadanda ke ciki wani hali.
An samu nasarar ceto wata mata da kuma wasu dalibai uku inda tuni aka wuce da su asibiti domin duba lafiyarsu.
Bidiyo: Ruwa ya kare a motar kashe gobara
Motar kashe gobara kenan za ta koma debo ruwa domin a ci gaba da kashe wuta
Bidiyo: Yadda jama'a ke zuwa gane wa idonsu abin da ya faru
'Bututun mai ya fashe a Legas'
Rahotanni daga jihar Legas na cewa an samu fashewar bututun mai a Unguwar Abule Ado a jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya
Gajimarin hayaki ya turnike sararin samaniya bayan afkuwar lamarin.
Wakilanmu da ke Legas din sun shaida mana cewa gidaje da dama ne suka rushe kuma yanzu haka babu cikakken bayani dangane da rayukan da suka salwanta sakamakon wannan iftila'i.
Tuni dai jami'an bayar da agajin gaggawa ciki har da kungiyar Red Cross International suka garzaya wurin domin bayar da agaji.
Farawa
Bayani kan maƙala - Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu barkanmu da wannan rana ta Lahadi, wannan shafin zai kawo muku rahotanni da kuma labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya, a ci gaba da kasancewa tare da mu.