Wada ya yi watsi da sakamakon zaben jihar Kogi

Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotanni kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da wasu makwabtansu a yau.

Rahoto kai-tsaye

  1. Rufewa

    A nan muka kawo karshen wannan shafi da ke kawo muku rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana a yau 18 ga watan Nuwamba.

    Ka da ku manta ku shiga cikin shafin sosai don karanta labarai kamar abin da Obasanjo ya ce kan Buhari da batutuwa kan zaben Kogi da Bayelsa.

    Halima Umar Saleh da Fauziyya Kabir Tukur ke cewa mu hadu gobe Talata idan Allah ya kai mu.

    Halima da Fauziyya
  2. Wada ya yi watsi da sakamakon zaben jihar Kogi

    Dan takarar gwamna a babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ya yi watsi da sakamakon zaben gwamna da aka gudanar ranar Asabar a jihar Kogi.

    A wata sanarwa da ya fitar, Injiniya Musa Wada ya ce da shi da magoya bayansa masu dimbin yawa a jihar ba su amince da sakamakon zaben 16 ga watan Nuwamba ba.

    Ya ce a ganinsa, ba zabe aka gudanar ba illa 'ayyana yaki kan al'umma'.

    Ya kuma zargi jami'an tsaro da hada kai da gwamnati wajen tsoratar da mutane da kashe masu kada kuri'a, inda ya ce mutanen da suka rasa rayukansu ba su gaza 9 ba.

    Ya ce tun da aka sanar da Yahaya Bello a matsayin wanda ya yi nasara, al'ummar jihar ke alhini.

    Injiniya Musa Wada ya ce zai bi hakkinsa a kotu kuma ya ce shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Mahmoud Yakubu da Sufeto janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu za su yi bayani a gaban Allah kan rawar da suka taka a zaben da ya ce mai cike da magudi.

    Injiniya Musa Wada

    Asalin hoton, FACEBOOK

  3. An kashe gomman mutane a Gummi a Zamfara

    Wasu 'yan bindiga sun far wa kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara da ke Najeriya, tare da hallaka gomman mutane, da kuma kona gidaje.

    Mazauna kauyen Karaye sun ce ba su taba ganin tahin hankali irin wannan ba.

    Sun ce 'yan bindigar sun zo a kan babura dauke da adduna, da bindigogi tare da yi wa kauyen kawanya, sun kuma kwashe sa'o'i da dama su na cin karensu ba bu babbaka.

    zamfara map
  4. Wani mutum ya ajiye zaki yana masa gadin gida a Legas

    Jami'an hukumar kula da muhalli a birnin Lagos, sun kai samame gidan wani mutum da ya ajiye zaki a matsayin maigadinsa.

    Kamar yadda rahotanni suka bayyana, jami'an sun je gidan ne a ranar Juma'a bayan mazauna unguwar sun kai korafin makwafcin nasu ya ajiye dabbar mai hadin gaske a gidansa.

    An dauke zakin daga gidan mutumin a ranar Litinin zuwa gidan namun daji da ke birnin.

    zaki
  5. Keke Napep sun daina zirga-zirga a Abuja

    A Najeriya yau fadin babban birnin taraya na Abuja da kewaye ya kasance babu Babura masu taya uku sabili da barazanar da jami’an tsaro suka yi wa drebobin ababan hawan.

    Tashoshi daban-daban ne inda masu Keke Nape ke daukar mutane suka kasance sai 'yan motocin tasi-tasi.

    Ko a makon da ya gabata masu baburen da ake kira keke-Napep sun gudanar da irin yajin aiki sabili da yunkurin hukumomin babban birnin Abuja na haramta gudanar da ayyukan nasu.

    Keke Napep

    Asalin hoton, Galaxy

  6. EU da Amurka sun nuna rashin jin dadinsu kan zaben Kogi da Bayelsa

    Zaben Kogi

    Hukumar Tarayyar Turai da gwamnatin Amurka sun nuna damuwarsu kan rahotannin tashe-tashen hankula da magudi da sayen kuri'u lokacin zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa a Najeriya.

    A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, masu sa idon sun ce sun yi matukar mamakin rikicin da tawagoginsu suka gani lokacin zaben.

    Cikin tawagogin akwai wakilan Tarayyar Turai da Amurka da kasashen Tarayyar Turai.

    Masu sa ido kan zabe sun nuna damuwarsu kan sayen kuri'u da abinda suka ce sahihan rahotanni kan sace akwatunan zabe.

    A kalla mutum uku aka kashe a zaben jihar Kogi kuma a cewar masu sa idon, wadanda aka kashe din sun hada da masu kada kuri'a da jami'an zabe.

  7. Ghana, Kwamitin da ke binciken zargin 'lalata da dalibai' na Ghana ya bayar da rahotonsa

    Kwamitin mai mambobi biyar, wanda Jami'ar Ghana ta kafa domin bincike kan zargin lalata da dalibai da malamai ke yi ya mika sakamakon bincikensa ga shugaban jami'ar Farfesa Ebenezer Oduro Owusu.

    Rahoton kwamitin ya biyo bayan dakatar da wasu malaman jami'ar biyu bisa zarginsu da lalata da dalibai, wanda sashen bincike na BBC Africa Eye ya bankado.

    University of Ghana Professor
    Bayanan hoto, Farfesa Gyampo na daya daga cikin malaman da aka nada yana neman ya yi lalata da wata daliba
  8. Faransa ta mayar wa Senegal kayan tarihin wani Malamin Islama

    Faransa da Senegal

    Asalin hoton, AFP

    Faransa ta mayar wa da Senegal wasu kayan tarihi wadanda mallakar wani sanannen malamin addinin Islama ne da ya yi zamani a karni na 19.

    Wannan dai wani yunkuri ne da Faransar ke yi na ganin ta mayar wa Senegal duk wani kayan tarihi da ta mallaka da kuma aka karbe a lokacin mulkin mallaka.

    Firai Minista Edouard Philippe ne ya mika wa Shugaba Macky Sall wani gariyo da kuma takobin katako da ke cikin kube.

    An gano cewa ainihin kayan yakin na tarihi mallakar Shugaba Umar Saidou Tall ne, wanda ya yaki mulkin mallaka da Faransa ta yi wa Senegal.

    Mista Phillipe ya ce wannan sharar fage ne kan abin da ya kira shirin mayar wa Senegal da kayanta da yanzu haka ke ajiye a gidan tarihin Faransa.

  9. Yahaya Bello ya lashe zaben gwamnan Kogi

    Yahaya

    Asalin hoton, Facebook

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ayyana Yahaya Bello na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi.

    Bello ya yi nasara ne da kuri'a 406,222.

    Sai dai bayan da aka kammala tattara sakamakon, baturen zabe ya bukaci wakilan jam'iyyu su sa hannu kan sakamakon na karshe amma wakilin jam'iyyar PDP ya ki sa hannu a sakamakon.

    PDP ta samu kuri'a 189,704 sannan SDP da ta samu kuri'a 9,482.

    Wakilin PDP ya ki sa hannu

    Asalin hoton, b

    Bayanan hoto, Wakilin PDP ya ki sa hannu
  10. Hotunan yadda ake tattara sakamakon zabe a jihar kogi

    Hotunan tattara sakamakon zaben jihar kogi
    Hotunan tattara sakamakon zaben jihar kogi
    Hotunan tattara sakamakon zaben jihar Kogi
    Hotunan tattara sakamakon zaben jihar kogi
  11. Da a Najeriya Yesu ya ke, ba zai iya kauda kai daga lamarin kasar ba- Obasanjo

    Olusegun Obasanjo

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce, da a ce Yesu al-masihu na Najeriya a wannan lokacin, ba zai iya kauda kai daga lamuran da ke faruwa a kasar ba.

    Jaridar Punch ta ruwaito tsohon shugaban da cewa haka a taron shekara-shekara na cocin Foursquare Gospel Church a Najeriya karo na 64, wanda aka gudanar a jihar Ogun.

    Obasanjo ya ce ganin halin da kasar ke ciki, ya kamata malaman addinai su rika fitowa suna magana kan abubuwan da suka addabi kasar, kamar yadda jaridar ta Punch ta ruwaito.

    Punch ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya bukaci babban malamin cocin da ya kai cocin mataki na gaba sannan sai ya yi hanzarin karawa da "Ban fa ce ka kai ta 'next level' ba."

    Obasanjo dai na shagube ne ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan takenta na "next level."

  12. Jami'a ta dakatar da daliban da suka yi wa wata daliba duka

    Jami'ar kimiyya ta Akure, FUTA da ke kudu maso yammacin Najeriya ta dakatar da wasu dalibai da suka yi wa wata daliba taron dangi suka yi mata dukan tsiya ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

    An yi ta ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan da wani bidiyo ya bayyana wasu dalibai na yi wa wata daliba wacce ta ke ajin farko dukan fitar hankali.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Kakakin makarantar Adegbenro Adebanjo ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a wajen makarantar.

    Adebanjo ya ce "A halin da ake ciki, mun dakatar da dalibai bakwai da ke da hannu a lamarin. Mun dakatar da karatunsu kuma bayan mun kammala bincike za su san makomarsu. Ba za mu amince da cin zarafi ba, babu wanda zai tsallake fushin hukuma a cikinsu."

    FUTA ta ki bayyana sunan daliban har sai sun gama bincikensu.

    Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Akure, Femi Joseph ya ce wani ya kira shi don kai kara kan lamarin kuma ya ba shi shawarar zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa.

    Rundunar ta ce idan lamarin ya faru ne a cikin makaranta dole ne ta bi ta hukumar makaranta kafin ta iya kama wani mai laoifi amma idan a wajen makaranta lamarin ya faru, to za su iya kama duk wani mai laifi kai tsaye.

    A halin yanzu, hukumar makarantar ta sallami dalibar da aka yi wa duka daga asibiti kuma ana ba ta shawarwari.

  13. An mayar da Hama Amadou gidan kaso a Nijar

    A ranar Litinin da safe ne madugun adawar jamhuriyar Nijar Hama Amadou, ya gabatar da kansa gaban alkalin da ya yanke masa hukuncin zaman kaso na shekara daya.

    Tuni dai aka mayar da shi gidan kaso na Flingue daga inda ya tafi magani bai dawo ba.

    Madugun adawar zai cike watani takwas din da suka rage masa.

    .

    Hama Amadou

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Labarai da rahotanni kai tsaye

    Masu bin shafinmu na BBC barkanku da war haka.

    Halima Umar Saleh da Fauziyya Kabir Tukur ne za su kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kmaru da Ghana a yau.

    Sai ku yi ta bin mu a wannan shafi don karin bayani.

  15. Buhari ya taya sabon gwamnan Bayelsa na APC murna

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bayelsa murnar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar dinna.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, shugaban ya ce wannan "nasara ce mai kayatarwa."

    A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da zabukan gwamna a Bayelsa da Kogi.

    Sannan hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ta sanar da cewa David Lyon na APC ne ya lashe zaben Bayelsa, amma ta ayyana cewa zaben Kogi bai kammala ba.

    Sannan shugaban ya yabi magoya bayan APC da 'yan jihar baki daya, ''wadanda suka kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali, duk da 'yan rikice-rikicen da aka samu a wasu wuraren.''

    Sanarwa ta kara da cewa shugaban ya yi Allah-wadai da asarar rayukan da aka samu a Bayelsa a lokacin zaben, ya kuma mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka mutun.

    "Tashin hankula a lokutan zabe na dakusar da kokarinmu na nuna wa duniya da al'umma mai tsaowa cewa mu mutane ne da ke iya zabar shugabanni cikin lumana," a cewar Buhari.

    Shugaba Buhari ya ce duk da cewa hukomar INEC da hukumimin tsaron kasar sun yi bakin kokarinsu don yin abin da kasa ta tanadar musu, to abin takaiic ne yadda aka dinga samun tashe-tashen hankula a wasu sassan jihar, "wadanda yawanci 'yan siyasar da idonsu ya rufe da son mulki ne suka dauki nauyin hakan."

    David Lyon

    Asalin hoton, APC Nigeria