Ana sayen kuri'u a Lokoja
Wakilin BBC a Lokoja babban birnin jihar Kogi Ibrahim Isa, ya ce ana zargin jam'iyyu da sayen kuri'u.
Ana zargin cewa jam'iyyar APC mai mulki na sayen kuri'un a kan Naira 5,000, yayin da ake zargin PDP da sayen kuri'un a kan Naira 1,000.
Ibrahim Isa ya ce ya shaida yadda ake sayen kuri'un a wasu mazabu da ya ziyarta.