Abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabta a yau

Shafi ne da ke kawo maku abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Karshe

    A nan muka kawo karshe kawo muku bayanan kai tsaye. Da fatan za ku kasance da mu gobe Asabar da misalin karfe 9:00 na safe domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa. Allah ya ba mu alheri.

  2. Shugaba Kiristoci reshen Kano da Sarki Sanusi

    Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II lokacin da Shugaban Kungiyar Kiristoci reshen jihar Kano, Samuel Adeolu Adeyemo ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Kano ranar Juma'a.

    Sarki Sanusi
    Sarki Sanusi
    Sarki Sanusi
  3. Hotunan shirye-shiryen zaben Bayelsa, Wasu hotunan ma'aikata da kayan zabe

    Bayelsa
    Bayelsa
    Bayelsa
    Bayelsa
  4. Hotunan shirye-shiryen zaben Kogi

    Ga wasu hotunan shirye-shiryen zaben Kogi.

    Zabe a Kogi
    Zabe a Kogi
    Zabe a Kogi
    Zabe a Kogi
    Zabe a Kogi
    Zabe a Kogi
  5. NNPC ya samu tallafi daga Amurka don gina tashar lantarki

    Kamfanin mai na Najeriya NNPC da kuma hukumar kasuwanci da ci gaba mai suna United States Trade and Development Agency (USTDA) za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar gina tashar lantarki mai zaman kanta a Abuja kan kudi dala miliyan 1.16 (naira milyan 361).

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin mai magana da yawun NNPC Samson Makoji ya fitar a Abuja ranar Alhamis.

    Ya ce yarjejeniyar ta biyo bayan wata ganawa ce da shugabannin bangarorin biyu suka yi a shedikwatar NNPC da ke Abuja.

    Mista Makoji ya ce aikin wutar lantarkin zai samar da megawatts 1,350 domin rage girman matsalar rashin wuta a fadin Najeriya kuma nan da 1 ga watan Disamba ne bangarorin za su kammala saka hannu kan yarjejeniyar.

    Tashar lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

  6. An sanya tsauraran matakan tsaro a Kogi

    An tsaurara tsaro a hedikwatar INEC da ke birnin Lokoja na Kogi.

    Jami'an tsaron na dauke da makamai da kayan aiki domin su tabbatar da tsaro sosai a ofishin hukumar zaben.

    Tuni dai INEC ta fara rarraba kayan zaben zuwa kananan hukumomi 21 na jihar, don tabbatr da cewa an fara zaben a kan lokaci a gobe.

    Kusan mutum miliyan 1.4 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu.

    Zabe a Kogi
  7. Kungiyar ma'aikatan shari'a ta Ghana ta dakatar da yajin aiki

    Kungiyar ma'aikatan shari'a ta Ghana JUSAG ta dakatar da yajin aikin da ta fara kwanakin biyu da suka wuce, bayan wata ganawa da manyan jami`an hukumar gudanarwa na sashen shari'a.

    Sai dai wasu rahotanni kuma na cewa dakatar da yajin aikin ya zo ne lokacin da kungiyar kwadago ta kasa ta samun izinin dakatar da yajin aikin na kungiyar daga wata babbar kotun birnin Accra, abin da kungiyar ta musanta.

    Tun a shekaran jiya ne dai kungiyar ma'aikatan shari'ar ta JUSG ta tsunduma cikin wani yajin aikin da ta ce sai abinda hali ya yi, don neman bukatar yin bitar tsarin albashin mambobinta.

  8. Lalacewar tarbiyyar matasa na damun al'umma a Agadez

    Majalisar jihar Agadez ta jamhuriyar Nijar ta shirya wani horo ga mambobin kwamitin kula da wanzar da zaman lafiya a jihar don nazarin yadda za a shawo kan tabarbarewar tarbiyyar matasa.

    Hukumomi sun ce matsalar na matukar ci musu tuwo a kwarya, shi yasa suka shirya tunkarar ta.

    Ga rahoton Tchima Illa Issoufou.

    Bayanan sautiRahoto kan tabarbarewar matasa a Agadez
  9. INEC ta ce dan takarar APC zai shiga zaben Bayelsa

    Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce APC za ta shiga zaben gwamna na jihar Bayelsa na gobe Asabar, duk da hukuncin kotu da ya ce jam'iyyar ba ta da dan takara a jihar.

    Mai magana da yawun hukumar INEC ta kasa Aliyu Bello ya yi wa BBC Huasa karin haske kan batun.

    A wata daban kuma, rahotanni na cewa, wata kotu a Yenagoa babban birnin Bayelsa ta soke takarar dan jam'iyyar PDP a zaben na gobe.

    Bayanan sautiKu saurari hirar mai magana da yawun INEC kan zaben gwamna na Bayelsa.
  10. Kotun Koli ta bayyana dalilan korar karar Atiku da PDP

    Kotun Kolin Najeriya ta ce Muhammadu Buhari "ya cancanci" ya yi takara a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2019 sabanin ikirarin jam'iyyar adawa ta PDP na cewa Buhari bai yi karatun sakandare ba.

    Kotun ta yi watsi da karar ne 'yan sa'o'i da fara sauraronta ranar 30 ga Oktoba ba tare da wani cikakken bayani ba, wadda Atiku ya shigar bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta sallami karar farko da ya shigar tun a ranar 11 ga Satumban 2019.

    Sai a yau Juma'a ne kotun ta ce za ta bayyana dalilanta na korar karar. Bisa wannan dalili ne kuma ta yanke hukuncin cewa korafin nasu bai karbu ba kuma ta kori karar tun a ranar 30 ga watan Oktoba.

    Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito Mai Shari'a John Okoro yana karanto hukuncin a madadin Alkalin Alkalan Najeriya Ibrahim Muhammad.

    Ya ce gazawar masu korafin na gabatar da kwararan shaidu shi ne dalilin korar karar, inda suka gabatar da shaidu biyar kacal cikinsu har da babban mai bayar da shaidar, wanda shi kuma ya bayyana jita-jita a matsayin shaida.

    Ya kara da cewa kazalika sun gaza gabatar da hujjar zargin da suka yi na yin aringizon kuri'u - sun gaza gabatar da takardar sunayen masu zabe domin tabbatar da hakan.

    Saboda haka Mai Shari'a Okoro ya ce hukuncin na yau (Juma'a), ya jaddada wanda kotun sauraron kararrakin zabe ta yi ranar 11 ga Satumban 2019, wadda ta tabbatar da zaben Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

  11. Masu kamfanin waya sun mayar wa Pantami martani

    Kungiyar masu kamfanin layukan sadarwa ta Association of Licensed Telecommunications Operators of Nigeria (ALTON) ta mayar wa Dr. Ali Isa Pantami martani game da umarnin da ya bayar na haramata wa kamfanonin tura sakon Voice Mail.

    A jiya Alhamis ne dai ministan sadarwar ya bayar da umarnin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ta fitar, inda ya ce "ana tilasta wa masu amfani da layukan wajen karbar sakon tare da cazar su sannan kuma ba a saba da shi ba a Najeriya".

    ALTON ta ce ta yi mamakin wannan umarni sannan ta bayyana matsayarta a kan tsarin kamar haka:

    "Wannan ba wani abin tayar da jijiyar wuya ba ne domin kuwa ba ya cikin manyan al'amuran da doka ta yi magana a kansu. Saboda haka hukumar kula da harkoikin sadarwa ta Najeriya wato NCC za ta iya shiga lamarin, ba lallai sai ministan ya saka baki da kansa ba, kamar yadda dokar Nigerian Communications Act 2003 ta tanada.

    "Voicemail tsari ne kari a kan sauran tsarukan da aka saba aiki da su kuma sai wanda yake so ne yake karbarsa a kyauta. An kirkire shi ne saboda a rage yawan kiran 'flashing' domin yana cushe hanyar sadarwa.

    "Dabi'ar da wasu kamfanonin suke yi a yanzu - idan mutum ya kira layi bai samu ba sai a ce masa ya bar sakon Voice Mail - ba hujja ba ce da za ta sahhale masu wuce gona da iri.

    Dr. Isa Ali Pantami

    Asalin hoton, Dr. Isa Ali Pantami

  12. Atiku da PDP sun kaurace wa zaman Kotun Koli

    Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ba ta amsa gayyatar Kotun Kolin kasar ba, wadda ta ce za ta bayyana dalilan da suka sa ta kori karar da Atiku Abubakar ya shigar a gabanta yana kalubalantar nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a zaben Fabarairun 2019.

    PDP ta kaurace wa zaman kotun a yau Juma'a sannan kuma ba ta tura wani wakili ba yayin da kotun ta ce za ta fayyace dalilanta game da hukuncin na ranar 30 ga Oktoban 2019.

    Kotun ta yi watsi da karar ne 'yan sa'o'i da fara sauraronta kuma ba tare da wani cikakken bayani ba, wadda Atiku ya shigar bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta sallami karar farko da ya shigar tun a ranar 11 ga Satumban 2019.

    A yayin zaman a yau Juma'a, in ji jaridar Premium Times, lauyan APC mai suna Alex Izinyon ya shaida wa kotun cewa lauyoyin PDP ba su halarci zaman ba kuma babu kananan lauyoyi abokan aikinsu.

    Ya ce ya jawo hankalin kotun ne game da rashin zuwansu saboda ya yi imanin cewa bin umarnin kotu wajibi ne. Kotun ta ce za ta ci gaba da zaman duk da rashin halartarsu.

    Zaman ya ci gaba a yayin da jaridar take hada wannan rahoto.

    Kotun Kolin Najeriya

    Asalin hoton, Premium Times

  13. 'Yan takara sun saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Kogi

    'Yan takarar jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kogi da na jam'iyyar adawa ta PDP sun bi sahun sauran abokan takararsu wurin saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin da ake shirin kada kuri'a a zaben gwaman jihar gobe Asabar.

    An saka hannun ne a ranar Talata amma ruguntsumin da ya faru a yayin taron da INEC ta jagoranta ya sa ba a samu tabbacin hakikanin abin da ya faru ba game da yarjejeniyar.

    INEC ta tabbatar da cewa an saka hannu kan yarjejeniyar, inda ta ce APC da PDP suna ciki. Sai dai 'yar takarar jam'iyyar SDP Natasha Akpoti ta yi zargin wasu matasa sun hana ta shiga zauren taron tare da ji mata rauni a ranar Talata.

    Sai dai INEC din ba ta yi wata-wata ba ta mayar mata da martani, inda ta ce ai laifinta ne saboda rashin halartar wurin taron a kan lokaci.

    'Yan takarar gwamna a jihar Kogi

    Asalin hoton, @inecnigeria

  14. Gafaranku dai masu bibiyarmu, barka da Juma'a, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta a yau

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka, barkanku da shigowa shafin rahotanni kai-tsaye game da abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta.

    Umar Mikail ne ke maku barka. To me za mu jira?

    Ai sai mu shiga aiki kawai.

    Umar Mikail

    Asalin hoton, Abdulbaki Jari

    Bayanan hoto, Umar Mikail