Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabta a yau

Shafi ne da ke kawo maku abin da ke faruwa kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Karshen rahotannin

    Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin.

    Bari mu bar ku da wannan hoton da muke son sanin sunansa da harshen Hausa. Da fatan za ku gano mana in kuma babu ku rada masa sabo.

  2. A shirya zabe na adalci a Kogi da Bayelsa - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su tabbata an gudanar da zaben gwamna lami lafiya ba tare da magudi ba a jihohin Kogi da Bayelsa.

    A wata sanarwa da mataimakin shugaban kan kafafen yada labarai Garba Shehu ya fitar wadda kuma gidan talabijin na NTA ya ruwaito, Buhari ya ce ya kamata a shirya zabe ba tare da nuna bangaranci ko alfarma ba.

    Sai dai tuni aka samu rahoton tashin hankali a jihohin biyu, inda mutum uku suka rasa rayukansu a Bayelsa sannan kuma 'yar takarar jam'iyyar SDP a jihar Kogi ta ce an ji mata rauni a wurin wani taron yarjejeniyar zaman lafiya da INEC ta shirya ranar Laraba.

    "Ina kira ga al'ummar jihohin Bayelsa da Kogi da su kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali da bin doka a duk inda suke. Jami'an tsaro wajibi ne su tabbata an kyale 'yan kasa sun kada kuri'arsu ba tare da tilastawa ba kuma a murkushe yunkurin satar akwati ta hanyar duk da ta dace.

    "Ana samun mai nasara da wanda ya sha kaye a kowane zabe saboda haka na Kogi da Bayelsa ma ba zai zama daban ba. Dukkanin 'yan takara su karbi kaddara inda kuma ba su gamsu ba sai su je kotu. Wajibi ne a guje wa daukar doka a hannu."

    Shugaban ya yi wa jama'ar jihohin fatan alheri yayin da suke shirin kada kuri'un nasu ranar Asabar.

  3. Rundunar sojin Najeriya ta taka rawar gani a gasar wasanni

    Rundunar sojin Najeriya ta yi nasara a gasar wasanni ta Military Skills Competition a Potchefstroom da aka gudanar a Afirka ta Kudu da wadda Majalisar wasannin sojoji ta kasa da kasa ta shirya a Jamhuriyar Guinea.

    Kakakin shelkwatar tsaro a Najeriya Kanal Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis.

    Ya ce rundunar ce ta zo ta daya a gasar da aka kammala kwanan nan a Afirka ta Kudu, yayin da ta zo ta uku a gasar dambe da aka yi a birnin Conakry na Guinea.

    Ya ce sojojin Najeriyar maza da mata ne suka shiga wasannin, kuma sun lashe lambobin yabo na Zinare guda shidda da Azurfa hudu da Tagulla daya.

  4. Ilimi garkuwar dan Adam

    Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Honorable Yakubu Dogara ya koma makaranta.

    Dogara yana halartar wani kwas ne na koyardar harkokin mulki a jami'ar Oxford da ke Birtaniya.

    Idan za ku iya tunawa Yakubu Dogara ya shugabanci Majalisar Wakilan Najeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2019, inda ya rasa kujerarsa ta shugabancin majalisar duk da cewa ya sake lashe zaben mazabarsa ta Bogoro / Dass / Tafawa Balewa daga jihar Bauchi.

  5. 'Nijar ta yi asarar naira biliyan N24 saboda rufe iyakar Najeriya'

    Kasashen Nijar da Benin da kuma Najeriya sun fara wani zama yau a Abuja domin duba halin da kasashen suka samu kansu tun bayan rufe iyakokin Najeriyar.

    Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa wannan mataki na rufe iyakokin ya janyo mata asarar kudin da suka kai CFA Milliards 40 (dala miliyan $67), kwatankwacin sama da naira biliyan N24.

    Ministan kudin kasar Diop Mamadou ya ce ya kamata a ce wannan kudi sun shiga baitulmalin kasar.

    'Yan kasuwa a Nijar sun ce su ma sun tafka asara, wasu daga cikinsu ma sun ce karyewa suka yi.

    Wani dan kasuwa Alhaji Mati a Yamai ya ce: "ya kamata a nemi hanyar warware wannan kikikaka saboda asarar da ake ta yi."

    Ya ce kayansa da yawa sun makale a iyaka kuma dole ya sa aka mayar da su Kano.

  6. Kotu ta ce APC ba ta da dan takara a Bayelsa

    Wata babbar kotu a jihar Bayelsa ta soke takarar dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APC a jihar.

    Kotun, wacce take zamanta a Yenagoa babban birnin jihar, ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis da safe.

    Hakan na nufin jam'iyyar APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben jihar da za a yi ranar Asabar.

    Mai shari'a Jane Inyang ta ce David Lyon bai bi dokokin tsarin mulki ba wajen zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

    Tun da fari kafin wannan lokaci, daya daga cikin 'yan takarar gwamnan na APC Sanata Heineken Lopkobiri, ya bukaci kotun ta ayyana shi a matsayin dan takara ba Mista Lyon ba.

    Lauyan Mista Lopkobiri ya ce hukuncin ya zo musu a ba zata, don ba abin da suka yi addu'ar ya faru ba kenan a lokacin da suka je kotun.

    An yanke wannan hukunci ne yayin da ya rage saura kwana biyu a yi zaben.

  7. Kotun Koli za ta fayyace dalilan korar karar Atiku

    Kotun Koli ta Najeriya ta sanya ranar da za ta bayyana dalilan da suka sa ta kori karar da Atiku na jam'iyyar PDP ya shigar yana kalubalantar zaben shugaban kasa da aka bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe.

    Atiku dai yana kalubalantar hukuncin farko ne da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke ranar 11 ga Satumban 2019 na yin watsi da korafin nasa, kuma tun a ranar 30 ga watan Oktoba ne Kotun Kolin ta yi fatali da karar ba tare da bayar da wani cikakken dalili ba.

    Gobe Juma'a 15 ga watan Nuwamba ita ce ranar da aka saka domin fayyace dalilan da suka sahhale korar karar, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ruwaito.

  8. Yawan mata ya karu a Majalisar Dattawan Najeriya

    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad lawan ya rantsar da Sanata Biodun Olujimi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu a yau Alhamis.

    Olujimi ta maye gurbin tsohon kakakin Majalisar ne, Adedayo Adeyeye, wanda kotun sauraron kararrakin zabe da kotun daukaka kara a Kaduna ta soke zabensa kwanan nan.

    Da wannan nadin dai yanzu mata takwas ne a Majalisar Dattawan Najeriya.

    Majalisar ta fitar da sanarwa a shafinta na Twiiter, inda ta ce tana fatan cewa zuwan Sanata Biodun zai samar da karuwar wanzar da ayyuka a majalisar.

  9. Kauyen Madaka da ke jihar Neja na cikin tasku

    Matsalar rashin kyawun tituna a Najeriya ba sabon abu ba ne, amma wasunku masu bibiyarmu ba su taba ganin irin halin da mutanen kauyen Madaka da ke jihar Neja suke ciki ba.

    Hanyar kauyen Madaka mahada ce ta kauyuka bakwai da suka hada da: Mgwa Magaba da Kompani da Rubo da Nafsira da daShikira da Wayam sai kuma kauyen Madaka.

    Mazauna kauyen sun ce sanadiyar rashin hanya mai kyau mata masu juna biyu da dama ne ke mutuwa a kan hanya kafin a isa asibiti, inda uwa da dan cikinta ke mutuwa.

  10. Mutum 13 sun mutu a hatsarin mota a Legas

    Mutum 13 ne suka rasa rayukansu wasu 10 kuma suka ji raunuka a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Laraba.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa abin ya faru ne a Saapade kusa da garin Ogere, kamar yadda Clement Oladele kwamandan hukumar kiyaye hadura mai kula da shiyya a jihar Ogun ya tabbatar.

    Mista Oladele ya ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe 5:00 na yamma a Saapade, inda kamfanin RCC mai aikin gyaran titin ya karkatar da hanya saboda aikin.

    Ya ce wata motar daukar kaya ce ta haddasa shi bayan tayarta ta fashe yayin da take tsaka da gudu a kan hanyarta zuwa Legas daga Ibadan.

    "A saboda haka ne motar ta afka wa wasu motocin guda biyu da suke nufar Ibadan bisa yunkurin da daya daga cikinsu ta yi na yanke dayar a daidai inda aka samu sauyin hanya," in ji shi.

    Ya kara da cewa motoci uku ne abin ya rutsa da su.

  11. Najeriya za ta shirya taron ministocin harkokin waje kan rufe iyakokinta, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya a yau da makwabtanta

    Ministocin harkokin wajen kasashen Najeriya da Nijar da Benin za su halarci wani taro a Abuja babban birnin Najeriyar domin tattaunawa game da rufe iyakokin kasar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi.

    Kasashen dai sun sha kokawa game da tasirin rufe iyakokin da kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka ta yi, wadda kuma ita ce babbar abokiyar huldarsu.

    Gwamnatin Shugaba Muhammadu Isufou na Nijar ta ce ta yi asarar kusan dala miliyan $67 kwatankwacin sama da naira biliyan N24 tun bayan da Najeriya ta rufe iyakokin a watan Agustan da ya gabata.

    BBC ta yi hira da shugaban hukumar Custom ta Najeriya Kanal Hamid Ali mai ritaya a watan Oktoba, ya ce babu ranar bude iyakokin.

    A farkon watan Nuwambar nan kuma kasar ta shimfida wasu sharudda wadanda ta ce sai an cika su ne sannan za ta bude iyakokin nata.

  12. An kashe mutum uku a wurin kamfe a Bayelsa, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya a yau

    Akalla mutum biyu ne suka mutu yayin da wasu matasa suka far wa gangamin yakin neman zaben jam'iyyar PDP a karamar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

    Wakilin gidan rediyon Najeriya ya shaida wa BBC Pidgin cewa wadanda suka rasa rayukan nasu sun hada da direban motar gidan rediyon jihar Bayelsa da kuma wani daban yayin da wadanda suka ji raunuka kuma suke karbar magani a asibitin Federal Medical Centre FMC Yenagoa.

    An yi ta samun rikice-rikice a wuraren kamfe na siyasa a jihar, yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar ranar Asabar mai zuwa.

    PDP dai ita ce mai mulkin jihar kuma sun shiga Nembe ne domin yin kamfe, inda rikici ya barke a yammacin jiya Laraba.

    Rahotanni sun ce matasan sun far wa filin taro na King Koko's Square da ke Ogbolomabiri Nembe yayin da magoya baya ke tsaka da jimurin isowar dan takarar gwamna na jam'iyyar ta PDP Sanata Douye Diri da kuma sauran jami'an jam'iyyar.

  13. Abubuwan da ke faruwa a Najeriya a yau da makwabta

    Masu bibiyarmu barkanku da wannan safiya ta Alhamis, wannan shafi zai rika kawo maku rahotanni kan abubuwan da suke faruwa a Najeriya da makwabtanta a yau.

    Umar Mikail ne ke maku sannu da shigowa.