Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Babu ranar bude iyakokin Najeriya - Hameed Ali
An wallafa
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron hirar:
Hukumar da ke yaki da fasa-kwauri a Najeriya ta ce za a ci gaba rufe kan iyokokin kasar da ke tudu har zuwa lokacin da Najeriyar za ta samu cikakken hadin kai daga sauran kasashen da take makwabtaka da su.
Hukumar Kwastam ta ce harkokin tsaron da na tattalin arziki sun inganta a Najeriya sakamakon rufe iyakokin kasar da ke kan tudu.
Kanar Hamid Ali mai ritaya shi ne shugaban hukumar, kuma ya yi wa Ibrahim Isa karin bayani.
Karin labaran da za ku so ku karanta