Abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta
Shafi ne da ke kawo maku abin da ke faruwa kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
AFCON 2021: Wasan cancantar shiga Kofin Kasashen Afirka, Nigeria 0-1 Benin
Yanzu haka Najeriya tana karawa da Benin a wasan neman gurbi a gasar cin Kofin Kasashen Afirka ta AFCON 2021, wanda kasar Kamaru za ta karbi bakunci.
Tuni aka cilla wa Najeriyar kwallo daya a raga minti 3 kacal da take wasa. Ana buga wasan ne a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.
Super Eagles dai na rukuni rukunin L tare da kasashen Lesotho da Sierra Leone da kuma Benin din.
Wasan da kasar take karbar bakunci shi ne zagayen farko na rukuni-rukuni da hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta shirya wa kasashen yankin.
Ana sa ran sai a tsakiyar shekarar 2020 Najeriya za ta yi tattaki zuwa gidan Benin a zagaye na biyu na wasan.

Asalin hoton, Getty Images
An kashe 'yan sanda uku a Kaduna
Wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda uku yayin wani kwanton bauna da suka yi masu yayin da 'yan sandan ke sintiri a kan hanyar Fadan Karshi zuwa dajin Nambia.
An kai masu harin ne a lokacin da suke sintiri a karamar hukumar Sanga a jihar ta Kaduna.
Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar ta ce jami'an nata sun yi musayar wuta yayin kwanton baunar da 'yan bindigar suka yi masu a cikin kungurumin dajin.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce 'yan sandan da suka mutu sun hada da Sufeto Bobai Bature da Inspecta Daniel Dogo da kuma Sajan Mamman Ahmadu.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ta jihar Kaduna ASP Sulaiman Abubakar ta ce sauran 'yan sandan sun kubuta ba tare da wani abu ya same su ba.
Daga baya an tura karin jami'an 'yan sanda domin kai wa 'yan uwansu dauki.
Rundunar ta ce tuni ta shiga farautar wadanda ake zargi da yi wa jami'an kwanton bauna.

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Rundunar 'yan sanda ta ce ta fara farautar miyagun El-Rufai ya yi rusau a Zariya
Gwamnatin jihar Kaduna ta fara aikin rushen-rushen gidaje a Zariya, kamar yadda Gwamnan jihar Nasir el-Rufai ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
Gwamnan ya ce an dauki matakin ne saboda aikin hanyar da za a yi na Fada-Rimin Kwakwa-Fanwanki-Kofar Jatau.
Sai dai bai yi karin haske ba dangane da adadin gidajen da aikin zai shafa ba.
Kuma ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar ta fara rusau ba a jihar.
Ba a harba wa shugaban INEC barkonon tsohuwa ba a Kogi - 'Yan sanda
Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta musanta rahotannin cewa an harba wa shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu barkonon tsohuwa yayin da yake halartar wani taron sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan takarar gwamnan jihar Kogi a ranar Talata.
Rahotannin sun ce sai da aka harba hayakin kafin a shawo kan wata hatsaniya da ta barke yayin taron, inda 'yar takarar jam'iyyar SDP Natasha Akpoti ta yi zargin cewa wasu tsagerun jam'iyyar APC sun hana ta shiga wurin tare da ji mata rauni.
Kakakin rundunar a jihar ta Kogi William Ovye Aya ya shaida wa BBC cewa ba shi da labarin yamutsin.
"Ban samu labarin wannann abu ba kuma babu wani barkonon tsohuwa da aka harba a wajen wannan taro," in ji shi.
Rundunar ta ce ta shirya tsaf game da zaben gwamnan jihar da ake shirin gudanarwa ranar Asabar, inda za su yi aiki tare da sauran abokan aikinsu masu damara.
"Babu abin da ya fi karfin 'yan sanda, ba yau suke ba da tsaro lokacin zabe ba, domin haka babu abin da zai faru. Akwai sauran ma'aikata da za mu yi aiki tare domin a tabbatar da tsaro."
A 'yan makonnin da suka gabata ne manyan jam'iyyun PDP, mai adawa, da APC mai mulkin jihar, ke zargin juna da tanadar 'yan daba tare da kulla makirce-makirce domin yin magudi a sakamakon zaben.
Kabilanci da addini na taka rawa sosai a siyasar jihar Kogi.
Gwamna Yahaya Bello shi ne dan takarar jam'iyyar APC yayin da Musa Wada ke yi wa PDP takara.
Musa Wada dan kabilar Igala ne mai ikirarin yawan jama'a a jihar, inda shi kuma gwamna mai-ci Yahaya Bello ya fito daga kabilar Ibira.
Ranar Asabar mai zuwa ne dai za a fafata a zaben gwamnan jihar.

Asalin hoton, @inecnigeria
Hotunan baje-kolin kayan sana'ar hannu ta mata a Nijar
Yau ce rana ta biyu da mata ke nuna kayan sana'arsu ta hannu a baje-kolin SANEF a jamhuriyar Nijar.
Mata daga yankuna hudu na kasar za su baje-kolin kayan ne a Yamai, babban birnin kasar.
Cikin kayan da za a baje akwai abinci da turaruka na jiki da na wuta da sabulai da man shafawa.
Ga wasu daga cikin hotunan da wakiliyarmu a Nijar, Tchima Illa Issoufou ta dakko:

Bayanan hoto, Wasu gada cikin matan sun kawo kayan gara na zamani da suka hada da kansu 
Bayanan hoto, Mata daga yankuna hudu na kasar za su baje-kolin kayan ne a Yamai, babban birnin kasar. 
Bayanan hoto, Cikin kayan da za a baje akwai abinci da turaruka na jiki da na wuta da sabulai da man shafawa 
Bayanan hoto, Za a kwashe tsawon kwana shida ana baje-kolin 
Bayanan hoto, Matan sun samu horo kan hada abubuwa da dama kamar sabulai da turauka 
Bayanan hoto, Wannan ne karo na uku da aka shirya wannan baje-koli 
Bayanan hoto, Matan na hada yaji da hadin ganyen shayi na gargajiya mai gyara jiki 
Bayanan hoto, Matan sun ce suna farin ciki da koyon sarrafa abubuwa da dama saboda a yanzu za su iya dogaro da kansu 
Daga Majalisar Dattawan Najeriya, Kudirin kafa kwalejin kirkirar mutum-mutumin komfuta a Najeriya
Sanata mai wakiltar jihar Abia ta Tsakiya Sanata Theodore Orji ya gabatar da kudiri a gaban Majalisar Dattawa a yau Laraba domin kafa Kwalejin Fasaha ta Tarayya, wadda za ta rika koyar da harkokin kere-keren kimiyya da fasaha.
Sanata Rochas Okorocha yayin da yake goyon bayan kudirin cewa ya yi: "Zai taimaka matuka idan aka samu jami'a mai kirkirar mutum-mutumin komfuta (robbotics) saboda ita ce hanyar ci gaba a yanzu. Akwai bukatar mu sauya tsarin ilimin kasarmu."
Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar Enyinnaya Abaribe, wanda shi ma yake wakiltar jihar Abia ta Kudu, ya bayyana cewa zai yi kyau a samu wannan kwaleji a jihar Abia.
"Muna godiya ga Sanata Theodore Orji da ya gabatar da wannan kudiri. Zai yi kyau a samar da wannan kwaleji a Abia domin kuwa ina da tabbacin cewa kudirin ba shi da wata illa ko kadan. Saboda haka kowa zai amince."
A jiya ne cibiyar The Massachusetts Institute of Technology da ke kasar Amurka ta kaddamar da wasu mutum-mutumin komfuta masu kafa hudu, wadanda ta ce a yanzu ana amfani da su ne kawai domin yin bincike amma ana sa ran nan gaba za a yi amfani da su a al'amuran gagggawa da ba da agaji.
Kalli irin aikin da suke iya yi a kasa
Kauce wa InstagramYa kamata a bar bayanan Instagram?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
'Yan bindiga sun saka haraji kan mazauna wani gari a Nijar, Sun kashe magajin garin
Rahotanni daga yankin Tillabery sun ce wasu 'yan bindiga sun saka haraji kan mazauna garin Boni/Anzourou na yankin Sakoira bayan sun kashe Magajin Garin.
Hakan ya kara ruruta rashin tsaron da kasar ke fama da shi, inda kungiyoyin 'yan bindiga suke kai hari kan sojoji da fararen hula.
'Yan bindigar da suka kwace ikon garin sun dora wa mazauna garin haraji, kuma wannan ya tursasa masu tserewa.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dattawa ta amince a bai wa jihar Kogi biliyan ₦10
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar biyan jihar Kogi bashin naira biliyan N10 daga gwamnatin tarayya.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya aike wa majalisar bukatar tun a watan Oktoba yana neman sahhalaewarta domin biyan bashin ayyukan da jihar ta yi a madadin gwamnatin tarayya.
Kafar talabijin ta Channels ta ce wasu daga cikin 'yan majalisar musamman na jam'iyyar adawa ta PDP sun nuna rashin amincewarsu, inda suka nuna damuwa ganin irin lokacin da aka zaba wurin bayar da kudin yayin da ya rage kwana uku a gudanar da zaben gwamna a jihar.
Yayin da yake magana a madadinsu, Shugaban Marasa Rinjaye Sanata Enyinaya Abaribe, ya bukaci majalisar da ta jinkirta amincewa da kudirin. Sai dai Shugaban Majalisar Dattawan Ahmed Lawan bai amince da kudirin nasa ba.
Ahmed Lawan ya ce ai bukatar ta shugaban kasa ta dade domin kuwa tun a majalisa ta tara ake tattaunawa kan batun.

Asalin hoton, @NGRSenate
Bayanan hoto, Shugaban Majalisar Dattawan Ahmed Lawan ya ce kudirin na majalisar da ta shude ne Shugaban Kamaru zai bai wa yankin rainon Ingila 'matsayi na musamman'
Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ce zai bai wa yankunan rainon Ingilishi biyu,wadanda mummunan rikicin 'yan aware ya mamaye tun shekarar 2017, 'matsayi na musamman'.
Biya ya sanar da haka ne jiya a wurin taron zaman lafiya na Paris Peace Forum.
Ya ce: "An rarraba kasata, Burtaniya ta yi wa kashi daya mulkin mallaka, daya kason kuma Faransa ce ta mulke shi. Wannan ya yi sanadiyyar hada mabambantan al'adu a kusa da juna kuma hakan ya sa abubuwa sun yi wahala."
Wannan ne karon farko da Shugaba Biya ya ce wani abu kan yiwuwar bai wa yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma matsayi na musamman tun bayan da aka bayar da shawarar yin hakan yayin wani taron kasa da aka gudanar a farkon watan Oktoba.
Tashar talabijin ta kasar ta ce Biya ya kasance cike da koshin lafiya yayin ziyararsa a kasar Faransa.

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da Shugaba Biya ya ce wani abu kan rikicin Rikici ya barke a wurin yarjejeniyar zaman lafiya a Kogi
Wasu masu dauke da makamai sun yi yunkurin tarwatsa taron da hukumar zaben Najeriya INEC ta shirya domin saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a jihar Kogi, yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jihar.
Rahotanni sun ruwaito cewa ana tsaka da taron ne wasu tsageru suka shiga wurin taron, duk da irin jami'an tsaro masu dauke da makamai da ke wurin, kuma suka yi yunkurin hana 'yar takarar gwamna a jam'iyyar SDP Natasha Akpoti shiga wurin taron.
'Yar takarar gwamnan ta wallafa wani hoto a shafinta na Twitter tana nuna yadda aka ji mata rauni tare da yin kira ga Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya da ya dauki mataki.
Ta kuma ce an gayyace ta taron ne a matsayinta na mai ruwa da tsaki a al'muran jihar.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
An dauki tsawon minti 20 ana sa-in-sa tsakanin wadanda suke kokarin shigo da ita da kuma wadanda ke yunkurin hana ta shiga a bakin kofar shiga, kamar yadda rahoton jaridar The Nation ta Najeriya ya nuna.
Da yake bayar da bayanai kan abin da ya faru, mai magana da yawun INEC Rotimi Oyekanmi ya yi Allah-wadai da abin sannan ya zargi 'yar takarar da cewa "ba ta je wurin taron da wuri ba", kuma abin da ya kara ta'azzara lamarin kenan.

Asalin hoton, @NatashaAkpoti
Bayanan hoto, Natasha ta ce a gaban shugaban hukumnar INEC abin ya faru Kotu a Abuja ta soke takarar dan takarar mataimakin gwamnan Bayelsa
Babbar kotu a Abuja ta soke takarar dan takarar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa karkashin jam'iyyar APC, Sanata Biobarakuma Degi-Eremienyo.
Kotun ta ce ba zai tsaya a zaben gwamna da za a yi ba ranar Asabar din nan 16 ga watan Nuwamba saboda rashin ''cancantarsa.''
Kotun ta soke takarar Sanata Degi-Eremienyo ne saboda bayanan da ya saka a fom din CF0001 da ya mika wa hukumar zabe ta kasa INEC ba daidai ba ne.
Mai shari'a Inyang Ekwo wanda ya yanke hukuncin soke takarar ya ce, sunayen da dan takarar ya sa a takardunsa na kammala makarantar firamare da na digirinsa na farko da na biyu da kuma takardar sauya suna sun sha bambam.

Asalin hoton, Sanata Degi-Eremienyo
'APC' ta dakatar da Adams Oshiomole
Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa Comrade Adams Oshiomole.
Shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomi 18 a jihar ne suka kada kuri'ar yanke kauna kan Adams Oshiomole a ranar Talata, kamar yadda shugaban jam'iyyar na jihar Aslem Ojezu ya shaida wa manema labarai.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamna Oshiomole da kuma mai-ci Godwin Obaseki suna kokawar neman iko ne da jam'iyyar a jihar ta Edo.
Sai dai Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar, sannan kuma babu tabbas kan yadda hakan zai shafi aikace-aikacensa a matakin kasa a matsayinsa na shugabanta.
Rikicin ya samo asali ne tun daga watan Yuni lokacin da 'yan majalisa tara cikin 24 na majalisar jihar suka zabi kakakin majalisar da sauran shugabanninta.
Za mu ci gaba da bin wannan labari domin kawo maku karin bayani da zarar mun samu.

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar Barka, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabta a yau
Masu bibiyarmnu barkanku da safiyar Laraba. Wannan shafi zai rika kawo maku rahotanni kai-tsaye game da abubuwan da suke faruwa a Najeriya da makwabta a yau.
Umar Mikail ne ke maku barka da shigowa da fatan za ku kasance da mu.
