Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

APC na murna, PDP na korafi

Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Shari'ar Buhari da Atiku

    Kuna iya kallon yadda shari'ar ke gudana kai-tsaye a Facebook a BBC Hausa.

  2. Tarihin Atiku Abubakar a takaice, Shari'ar Buhari da Atiku

    • Shekararsa 73
    • Ya yi gwamnan jihar Adamawa
    • Ya yi mataimakin shugaban kasa 1999 zuwa 2007
    • Hamshakin dan kasuwa ne
    • Ya rike mukami a hukumar Customs
    • Ya sha fuskantar zarge-zargen cinhanci da rashawa
    • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  3. Tarihin Muhammadu Buhari a takaice, Shari'ar Buhari da Atiku

    • Shekararsa 77
    • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
    • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1983 zuwa 1985
    • An hambare shi a juyin mulki
    • Kungiyoyin kare hakkin dan adam na zarginsa da kin bin umarni kotu
    • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
    • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  4. Ra'ayoyinku daga Facebook, Shari'ar Buhari da Atiku

  5. Zauren kotun shari'ar Buhari da Atiku

    Harabar kotun kenan yayin da lauyoyin da ke wakiltar bangarorin biyu ke ci gaba da jiran hukunci.

  6. Kofar shiga kotu

  7. An girke jami'an tsaro a hanyar Kotun

  8. Sunayen alkalan da ke yin shari'ar

    Alkalai biyar din da za su yanke hukunci a zaman kotun na yau sune:

    ·Mai Shari’a Abdul Aboki daga Abuja

    ·Mai Shari’a Joseph Ikyegh daga Benin

    ·Mai Shari’a Samuel Oseji daga Legas

    ·Mai Shari’a Peter Ige daga Abuja

    ·Mai Shari’a Muhammad Garba

  9. Shugabannin APC da PDP da hadiman Buhari sun halarci kotu

    Tuni kotun ta cika da manya-manya daga jam'iyyun guda biyu, yayin da kowane bangare ke sanin makomarsa a yau din.

  10. Za a yi ta ta kare tsakanin Buhari da Atiku

    Yau Laraba kotun sauraron kararrakin zabe take yanke hukunci dangane da karar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya shigar a gabanta ta kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

    Atiku Abubakar ya shigar da karar ne bayan da hukumar zaben kasar INEC ta bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya ci zaben ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2019.

  11. Barkan mu da warhaka

    Masu bibiyarmu barkanku da safiyar Laraba, Umar Mikail ke maku fatan an tashi lafiya.

    Za mu kawo maku rahotanni kai-tsaye game da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya tsakanin jam'iyyun APC mai mulki da kuma PDP mai adawa.