Karshen rahotannin, Kotu ta yi watsi da karar Atiku da PDP
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin. Muna godiya da kuka kasance tare da mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.
Umar Mikail
Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin. Muna godiya da kuka kasance tare da mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Zuwa yanzu ba a samu martani ba daga Atiku Abubakar ko jam'iyyar PDP game da hukuncin kotun.
Jam'iyyar PDP da dan takararta suna da damar daukaka kara a kotun kolin Najeriya.
Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.
Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Muhammad Garba ta tabbatar da Shugaba Buhari na jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben watan Fabrairun 2019.
Sakamakon da hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar ya nuna cewa Shugaba Buhari, mai shekara 76, ya samu kuri'a miliyan 15 da dubu 200 yayin da Alhaji Atiku Abubakar, mai shekara 72, na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a miliyan 11 da dubu 300.
Kotu ta yi watsi da ikirarin Atiku da PDP cewa su ne suka samu mafi yawan kuri'u a zaben shugaban kasa na 2019 bisa sakamakon da suka tattara daga rumbun tattara sakamako na intanet.
Mai Shari'a Muhammed Garba ya ce a dokar zaben Najeriya "ana aikewa da sakamakon zabe ne kawai a fili ba ta intanet ba a kowane mataki tun daga jiha har zuwa kasa baki daya".
Ya kara da cewa: "Babu wata doka da ta bai wa INEC ko wani jami'i damar tura sakamakon zabe ta intanet. Sannan kuma babu dokar da ta bai wa INEC damar yin amfani da na'urar card reader wurin tattara sakamakon zabe."
Kotu ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai cancanci ya tsaya takara ba saboda bai je makaranta ba.
Daya daga cikin korafe-korafen da PDP da Atiku suka gabatar a gabanta shi ne cewa Buhari ba shi da takardun shaidar zuwa makaranta sabda haka bai cancanci ya yi takarar ba baki daya.
Kotun ta ce dokar zabe ba ta tilasata wa dan takara ya hada da takardun shaidar kammala karatunsa ba yayin mika fom mai lamba CF001 kafin a tabbatar da cancantarsa.
Mai Shari'a Muhammed Garba ya ce Atiku da jam'iyyarsa ta PDP sun gaza gamsar da kotu cewa takardun da Buhari ya gabatar ba na gaskiya ba ne.
Sannan kuma sun yi zargin cewa Buharin ya yi karya game da takardun shaidar kammala karatunsa, abin da kotun ta yi watsi da shi domin, a cewarta, tun kafin zabe ya kamata a duba shi ba bayan zabe ba.
Zaman kotu ya ci gaba bayan dan gajeren hutu da aka tafi.
Yanzu za a gabatar da hukunci ne kan korafe-korafen da suka shafi kafin zabe.
Mai Shari'a Muhammed Garba shi ne shugaban rukunin alakalan da ke sauraron karar, kuma a nan gaba ne za su bayyana hukuncinsu kan zaben da INEC ta ce Muhammadu Buhari na APC ne ya lashe shi a watan Fabararairun 2019.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya jagoranci zaman majalisar ministocinsa a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.
Ya yi hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman shari'arsa tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar a kotun sauraron kararrakin zabe.
Kuna iya kallon yadda shari'ar ke gudana kai-tsaye a Facebook a BBC Hausa.
Kazalika, kotu ta yi watsi da batun cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karya game da takardar shaidar karatunsa, inda ta ce abu ne da ya shafi harkoki kafin zabe.
Tun farko ita ma INEC ta ce ya kamata ne a gabatar da korafjn tun kafin zabe, yanzu kuma kotu ta goyi bayan hakan.
Game da batun da lauyoyin jam'iyyar APC suka gabatar a gaban kotun cewa Atiku Abubakar ba dan Najeriya ba ne, kotun ta yi watsi da ikirarin da cewa abu ne da ya shafi harkoki kafin zabe, ita tana sauraron abin da ya biyo bayan zabe ne.
APC dai na cewa ne Atiku dan kasar Kamaru ne, wanda hakan ya haramta takararsa ta shugabancin Najeriya.
Tun farko INEC ce ta fara cewa lamarin na kafin zabe ne, inda ita ma kotun ta tabbatar da haka a yau.
Kotun ta umarci Buhari da jam'iyyar APC da su sake shirya sabon korafin da za su gabatar wa kotu a kan hakan domin tun a baya ya kamata su yi hakan.
Wani magoyin bayan Buhari mai suna Kenneth Cole ya wallafa a Twitter:
"Mutum zai yi kuka yau din nan"
Jam'iyyar APC ta yi imanin cewa 'yan Najeriya ne suka zuba wa Shugaba Muhammadu Buhari kuri'u, shi yasa ma har suka shiga Next Level, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.
Wani mai suna Aliyu Dahiru Bello @ADB_Gombe
Ya rubuta cewa: ''Idan Atiku ya samu nasara a yau zan rabawa mutum 20 naira 200,000, kuma zan zabo mutanen ne ta hanyar canki-canka kawai. #PEPTSAVENIGERIA''
Tuni dai mutane a shafukan sada zumuntar Najeriya musamman Twitter suke ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan hukunci da za a yanke.
Magoya bayan ATiku Abubakar tuni sukaa kaddamar da wani maudu'i mai taken #AtikuIsComing.