Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai da martani kan dage zaben Najeriya

Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni da bayanai har ma da martani kan matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na dage zaben.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahya and Mohammed Abdu

  1. Masu sa ido a zabe 'sun gamsu' da shirye-shiryen INEC

    Masu sanya ido a zabukan Najeriya na 2019 sun ce sun gamsu da shirye-shiryen da hukumar zaben kasar take yi na gudanar da zabe a jihar Kano da ke arewacin kasar. Sun bayyana wa taron manema labarai anar Juma'a cewa ba su da ja game da yadda INEC ke raba kayan aikin zabe.

  2. Kalli bidiyon yadda ake shirye-shiryen zabe a Yola

    Yadda ake shirye-shirye da tantance kayayyakin zabe a hukumar zabe mai zaman kanta reshen Yola dake jihar Adamawa.

  3. Yadda ake shirye-shiryen zabe a sansanin 'yan gudun hijira

    A yanzu haka dai an fara shirye-shiryen zabe a sansanin 'yan gudun hijira dake Abagana a jihar Benue.

  4. Bidiyon yadda ake kasa wasu kayayyakin zabe a Kano

    A yanzu haka an fara warewa da kasa wasu daga cikin kayayyakin zabe a Kano domin saukin tantancewa.

  5. Wasu daga cikin kayayyakin zabe kenan a jihar Benue

    Tuni dai kayayyakin zabe suka isa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta a Makurdi dake jihar Benue. Wasu daga cikin kayayyakin sun hada da na'urar tantance masu kada kuri'a watau card reader

  6. Malam Gambo ya kawo kwandon tumatir shida don zabe

    Mallam, Gambo kenan mai sana'ar siyar da kayan miya a Kano inda a yau jajibirin zabe ya kawo kwandon tumatir shida a maimakon daya domin yana tsammanin jama'a da dama za su shigo kasuwa domin siyan kayan miya saboda hutun zabe.

  7. Jami'an tsaro za su raka kayan zabe

    Hukumar zaben Najeriya ta hada gwiwa da jami'an tsaro musamman 'yan sanda inda za su raka kayan zaben da za a kai sassa daban-daban a kasar, kamar yadda kuke iya gani a wadannan hotuna da abokin aikinmu na sshen turanci, Chris Ewokor, ya aiko daga jihar Adamawa.

  8. An soma rarraba takardun kada kuri'a a Adamawa

    Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Adamawa ta soma rarraba kayan zabe masu matukar muhimanci, ciki har da takardun kada kuri'a ranar Juma'a. Ma'akatan zabe da masu sanya ido na cikin wadanda suka halarci wurin rarraba kayan zaben.

  9. Masu zabe karon farko a Najeriya

    Mun tattauna da wasu matasa da za su yi zabe karon farko a Najeriya. Ga abin da suke cewa:

  10. Ra'ayoyinku na Facebook

    Masu bibiyarmu a shafin Facebook suna can suna tafka muhawara kan shirye-shiryen zaben Najeriya. Ga wasu daga cikinsu:

    Belo IssaToh Madalla,Allah ya tabbatar mana da alheri a wannan zabe. 'Yan uwanmu 'yan Najeriya, muna fatan Allah ya ba ku shugaba mai tsoron Allah. Bello issa Damagaram Jamahiriya Niger

    Alh Hassan MaiWaya Kangiwa muna tare da ku min a bangaren a sauraronku na rediyona tun jiya kuma ba zan kashe ba sai naji samakon zabe!! Haka ma abun yake a bangaren Wayata ta Salula na sayi (Data) ta wata daya domin bibiyarku a shafukan sada zumunta!! Sabida haka kuja kawai muje Allah ya bada sa'a.

    Malam Shamsu Maigari Danzomo: Za mu tsaya mu yi zabe ingantacce,mu zabi shuwagabanni na gari domin gudun kawowa kanmu matsala.

  11. Matar da ta shafe shekara 36 tana sayar da abinci a ofishin INEC

    A yayin da ake shirye-shiryen zaben Najeriya, BBC ta tattauna da Mama Amina wacce ta kwashe sama da shekara 36 tana sayar da abinci a ofishin hukumar zaben jihar Kano. Ta ce irin wannan lokaci shi ne ta fi yin ciniki.

  12. INEC ta shirya tsaf a jihar Nasarawa

    Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Nasarawa ta raba kayan zabe zuwa ga kananan hukumomi takwas ranar Alhamsi da yamma inda ta ce za ta ka kayan zuwa ga sauran kananan hukomomi biyar ranar Juma'a, in ji wakiliyarmu, Raliya Zubairu.

  13. An soma raba kayan zabe a Benue

    Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Benue ta soma rarraba kayan zabe, kamar yadda kuke gani a wadannan hotunan da wakilin da muka aika jihar, Abdussalam Ibrahim Ahmed ya aiko mana.

  14. Masu kada kuri'a a Adamawa sun yi wa ofishin INEC tsinke

    Masu kada kuri'a a Yola ta Kudu da ke jihar Adamawa sun yi wa ofishin hukumar zabe, INEC tsinke domin su duba sunayensu. da dama daga cikinsu sun dauki hotunan jerin sunayen da INEC ta manna a bangon ofishin domin kada a samu matsala idan sun koma jefa kuri'unsu.

  15. An kama 'yan daba a Kano

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama mutanen da take zargi da daba da bangar siyasa, da kuma sayar da kayan maye dauke da makamai gabanin zaben kasar.

  16. Adamawa ta dauki harama

    Wakilinmu Muktari Adamu Bawa ya isa birnin Yola na Adamawa inda zai aiko mana da labarai da rahotanni daga jihar ta dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar. Ya zagaya sassa daban-daban na jihar, ciki har da kasuwanni domin ganin halin da ake ciki.

  17. An kama samfurin takardun zabe a Kano

    Rahotanni daga jihar Kano na cewa 'yan sanda sun kama wasu takardun kada kuri'a na gwaji da aka nufi yin amfani da su a jihar Jigawa.

    Batun dai ya janyo takaddama tsakanin jam'iyyar PDP da ta APC kan abin da ake shirin yi da takardun.

    Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama buhunhuna makare da takardun kada kuri'a na gwajin, da aka ce za a kai su jihar Jigawa ne da ke makotaka.

  18. Shirye-shiryen zuwa kai kayen zabe a jihar Borno

    Kafar watsa labarai ta BBC ta aika wa masu aiko mata da rahotanni zuwa dukkan jihohin Najeriya domin ba ku rahotanni kan wainar da ake toya wa, kamar yadda wadannan hotunan da Abdu Halilou ya turo mana kan shirye shiryen zuwa kai kayen zabe a jihar Borno

  19. Tsarin zaben 2019 ya bambanta da na 2015

    Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci mabiyanmu da masu saurare su aiko da tambayoyinsu kan abin da suke son sani game da zaben Najeriya.

    BBC Hausa ta mika tambayoyin da aka aiko ga Mallam Aliyu Bello, kakakin Hukumar zabe Najeriya, INEC, wanda kuma ya yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko. Ku latsa nan Shin INEC ta yi karin rumfunan zabe?domin karin bayani

  20. Kun san yawan 'yan takarar shugaban Najeriya?

    Hukumar zaben Najeriya ta tantance mutum 73 domin fafatawa a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, sai dai gumurzun zai fi yin zafi ne tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubaar na jam'iyyar PDP.

    Mutanen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kafin da kuma bayan zaben.