Zauren muhawara ya soma dinkewa
Zauren muhawara ya soma dinkewa da bakin da aka gayyata domin kallon yadda za ta kaya. Tuni dai 'yan takara uku suka isa wurin muhawarar.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Kano.
Nasidi Adamu Yahya and Mustapha Musa Kaita
Zauren muhawara ya soma dinkewa da bakin da aka gayyata domin kallon yadda za ta kaya. Tuni dai 'yan takara uku suka isa wurin muhawarar.
'Yan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyun PDP da PRP da NPM, Abba Kabir Yusuf da Salihu Sagir Takai da kuma Mustapha Getso sun iso wurin da za a yi muhawara.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PRP, Salihu Sagir Takai, ya ce a shirye yake ya fafata a muhawarar da BBC Hausa ta shirya kuma zai ba da amsa ga dukkan tambayar da aka yi masa.
'Yar takarar gwamnan Kano a jam'iyyar UPP, Maimuna Muhammad, ta bukaci magoya bayanta da dukkan al'umar jihar Kano su yi mata tambayoyi domin ta ba su amsa kan kudurce-kudurcenta na ci gaban Kano.
Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar NPM Mustapha Getso ya ce zai halarci muhawarar da BBC Hausa ta shirya ranar Asabar a Kano, yana mai cewa zai amsa dukkan tambayoyin da za a yi masa "daidai gwargwado".
Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya ce yana alfaharin kasancewa daya daga cikin mutanen da BBC ta zaba domin tafka muhawara ranar Asabar. Ya bukaci duk mutumin da ke son yi masa tambaya ya aiko ta, yana mai cewa a shirye yake ya amsa kowace tambaya.
Bakin da muka gayyata domin halartar muhawarar sun soma isa wurin inda suke yin rijistar sunayensu.
Za a gudanar da muhawarar ce a wannan babban zauren da ke Jami'ar Bayero ta Kano da karfe goma na safe a agogon Najeriya da Nijar.
'Yan takara biyar ne ke tafka muhawara wadanda suka hada da Abba Kabiru Yusuf na jam'iyyar PDP, Abdullahi Umar Ganduje jam'iyyar APC, Salihu Sagir Takai na jam'iyyar PRP, Mustapha Getso na jam'iyyar NPM da kuma Maimuna Muhammad ta jam'iyyar UPP.
Da fatan kun wayi gari lafiya. Ni ne Nasidi Adamu Yahaya tare da Mustapha Kaita za mu kawo muku bayanai kai tsaye kan muhawarar da BBC Hausa take gabatarwa tsakanin 'yan takara biyar da ke neman gwamnan jihar Kano. Sai ku biyo mu.