Gombe
jiha ce da ke arewa maso gabashin Najeriya, haka kuma babban birnin jihar shi ne Gombe.
Gombe dai jiha ce da ke cikin jihohi 36 na kasar.
An kirkiri Gombe ne a lokacin mulkin soji
na General Sani Abacha inda aka cire garin daga jihar Bauchi a 1996.
Gombe tana da iyaka da jihohin Borno,
Yobe, Taraba, Adamawa da kuma Bauchi.
A 2006, an kidaya yawan mutanen jihar da
yawan su ya kai 2,365,000.
Gombe dai jiha ce da ke da kabilu daban-daban
amma kabilar Fulani sune
mafi rinjaye,
musamman a arewacin jihar.
Akwai 'yan kabilar Tangale wadanda sune suka
mamaye kudancin jihar, sai kuma sauran kabilun da ke cikin jihar sun hada da
Hausa, Tera. Waja, Bolewa da kuma Kanuri.
Kabilar Tera a jihar na daga cikin Kabila mai
yawan jama'a idan aka cire Fulani da Hausa, domin kuwa kabilar Tera ne suka
mamaye karamar hukumar Deba.
Gombe dai tana da kananan hukumomi 11 da suka
hada da Akko, Balanga, Billiri, Dukku, Funakaye, Gombe, Kaltungo, Kwami,
Nafada, Shongom, Yamaltu/Deba.
A yanzu haka dai, gwamnan jihar shine Ibrahim
Hassan Dankwambo.
Gombe tana da 'yan majalisar jiha 24 sai na
tarayya 6, sai kuma 'yan majalisar dattawa 3.
Gwamnonin jihar Gombe a baya sun hada da
Group Captain Joseph Orji1996-1998
Abubakar Habu Hashidu1999-2003
Mohammed Danjuma Goje 2003-2011