Umaru Aliyu Doma gogaggen dan kasuwa ne da ya yi karatukansa a makarantunr Kasuwanci ta Harvard Business School, da ke Boston a Amurka da kuma wata Cibiyar Fasaha a Amurka wato Massachusetts Institute of Technology.
Ya yi karatun firamare da na sakandarensa a Baptist High School da ke Jos da kuma Corona Private School a Bukuru , duk a Jihar Filato.
Dan kasuwa ne da ya fi sha'awar ayyukan noma da fasaha da harkokin yawon bude ido da sauran su.
Umaru ya yi aiki a bangarori da dama a cibiyoyi masu zaman kansu.
Shi ne shugaban kamfanjn Oriya Farms, wani kamfani na harkokin kasuwancin noma da kuma kamfanin Boltzman Engineering Ltd ,na bangaren Fasaha. Shi ne daraktan kamfanin sadarwa na
BCTEK Engineering.
Umaru ne ya kirkiri kamfanin Hyatt Consult Limited kuma shi ne shugabansa.
Ya taba zama mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan Nasarawa a baya.
Shi ne Garkuwan Doma kuma Ajiyan Keana.
Yana da mata da yara.
Yanzu yana takarar gwamnan Nasarawa a karkashin jam'iyyar ZLP a zaben 2019.