Gawar Shehu Shagari ta isa Sakkwato daga Abuja, Shehu Shagari ya rasu
Gawar tsohon Shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari ta iso jiharsa ta Sakkwato domin yi masa jana’iza.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karanta bayanai da labarai game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari, shugaba na farko mai cikakken iko wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a.
Awwal Ahmad Janyau and Haruna Shehu Tangaza
Gawar tsohon Shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari ta iso jiharsa ta Sakkwato domin yi masa jana’iza.
Alhaji Shehu Shagari ya fara harkokin siyasa ne tun shekarun 1950 gabanin samun ‘yancin kan Najeriya lokacin da ya jagoranci wata kungiyar matasa da ta taimaka wajen kafuwar jam’iyyar NPC wadda Ita ce jam’iyyar da ta fara mulkin kasar a jamhuriyya ta farko.
Ya kwashe kusan shekaru talatin yana taka rawa a fagen siyasar kasar abin har ya kai shi ga zamowarsa zababben shugaban farar hulla na farko a Najeriya.
Kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara a sakon ta'aziyarsa ya ce Najeriya ta yi rashin uba mai son zaman lafiya da kishin kasa tare da cewa an rasa dan kasa nagari.
A sakon da ya fitar ta shafinsa na twitter Shugaban Majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya roki Allah ya jikan marigayi Alhaji Shehu Shagari.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ce bayyana Shagari a matsayin wanda ba ya da kabilanci wanda ya bauta wa Najeriya tun yana matashi da malami da har ya zama shugaban kasa.
A sakon da ya aika kan rasuwar Shagar, tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce za a tuna mamacin a matsayin wanda ya gudanar da harkokin siyasa ba tare da gaba ba, kuma wanda bai nuna bambanci tsakanin al'ummar kasar ba.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a sakon ta'aziyarsa ya ce yana alhinin mutuwar dan kasa nagari da ya yi wa Najeriyta aiki da gaskiya. Ya ce Shagari mutum ne da ke da daraja ga 'yan Najeriya ko bayan ya bar mukamin shugaban kasa.
Alhaji Bello Idris shugaban gidan ajiye kayan tarihi na Waziri Junaidu da ke Sakkwato ya shaida wa BBC cewa kakannin Alhaji Shehu Shagari suka kafa garin Shagari wadanda Fulani ne da suka taso daga Kauran Namoda yanzu a Jihar Zamfara suka shiga cikin rundunar mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio lokacin jihadi inda suka kafa garin da suka kira Shagari da ke jihar Sakkwato.
- Dan asalin jihar Sakkwato ne a arewa maso yammacin Najeriya
- An haife shi a shekarar 1925 a garin Shagari
- Shi ne na shida ga maifinsa Aliyu
- Dan siyasa ne Manomi kuma makiyayi
- Malamin Makaranta ne marubucin wakoki da tarihi
- Ya zama shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar NPN
- Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983
- Bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa, Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a mulkin soja
- Kafin Shagari ya zama shugaban kasa ya taba zama sakataren majalisar Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa
- Ya rike mukaman minista daban-daban
- Ya taba zama ministan ci gaban tattalin arziki a shekarar 1960
-Ya taba zama ministan kula da harkokin cikin gida a shekarar I962
- Ya taba rike ministan ayyuka da safiyo (1965).
- Shagari ne Turakin Sakkwato, wanda babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Sarkin Musulmi.
Tsohon shugaban ya rasu ne ranar Juma'a a asibitin kasa da ke Abuja bayan fama da jinya.
Muna maku barka da rana a wannan lokacin da za mu kawo maku bayanai kai-tsaye game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari da Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a.