Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hatsaniya ta kaure a zaben fidda gwani

Labarai da sharhi game da yadda ake zaben fidda gwani na 'yan takaran gwamna a jam'iyyar APC da jam'iyyar PDP.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan

  1. Babu mutane a wasu mazabun Kano

    Babu mutane a wasu rumfunar zabe a Kano, yayin da wasu 'yan jamíyyar APC ke dakon kayayyakin zabe da jamiáin zabe. Har karfe 11 na safe dai ba a fara zaben ba a wasu wurare a Kano.

    A jihar Kano mutum daya ne yake neman ya zama dan takara, gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, wanda ke son ya yi wa'adi na biyu a kujerar gwamna.

  2. An dage zaben fidda gwanin APC a Zamfara

    An dage zaben fidda gwanin 'yan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

    Sakataren watsa labaran jam'iyyar APC, Shehu Isa Gusau, ne ya bayyana matakin ga manema labarai.

    Ya ce an dage zaben ne saboda jinkirin da aka samu na zuwan jami'ain zaben da kuma kayan zaben.

    Sai ranar Litinin za a yi zaben.

  3. Gwamnan Borno ya bayyan wanda yake son ya gaje shi

    Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana wanda yake son ya zama dan takaran gwamnan jihar Borno karkashin inuwar jam'iyyar APC.

    A wata sanarwar da mai taimaka masa kan lamuran watsa labarai, Isa Umar Gusau ya aika wa manema labarai, gwamnan ya ce ya fi son farfesa Babagana Umara Zulum ya zama dan takaran gwamnan jihar bayan zaben fidda gwanin da ake yi a ranar Lahadi.

    Sai dai kuma, Kashim ya ce son da yake yi na Zulum ya zama dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC bai kamata ya hana kowa takara a zaben fidda gwamni ba.

  4. APC da PDP sun daga zabe a wasu jihohi

    Jam'iyyar APC ta daga zaben fidda gwani a jihohin Legas da Imo yayin da ita kuwa PDP ta daga zaben a jihohoin Lagos da Imo da kuma Kano.

  5. Barka da shigowa

    Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku labarai da sharhi kai tsaye game da yadda ake zaben fidda gwani a jam'iyyar APC a mafi yawan jihohin Najeriya.