Dan takarar ADP ya kada kuri'a
Dan takarar jam'iyyar ADP, Moshood Adeoti, ya kada kuriarsa.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai da sharhi game da yadda ake zaben gwamna a Osun wanda ake ganin zai nun irin yadda zaben 2019 zai kasance a Najeriya.
Abdulwasiu Hassan
Dan takarar jam'iyyar ADP, Moshood Adeoti, ya kada kuriarsa.
BBC ta yi tir da yadda maogaya bayan 'dan takarar jam'iyyar ADP, Moshood Adeoti, suka saka rigarta zuwa wajen zabe.
Sun samu rigunan ne a lokacin da aka yi wata muhawara da BBC ta shirya wa 'yan takarar gwamna a jihar domin mutane su san manufofin 'yan takarar da ke neman mukamin gwamnan jihar.
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan da ake yi a jihar Osun, Alhaji Gboyega Oyetola ya kada kuri'arsa.
Babbar jam'iyyar adawar Najeriya, PDP, ta yi zargin cewa jami'an jam'iyyar APC mai mulkin kasar da jihar Osun inda ake zaben gwamna sun raba kudi wa masu zabe a rumfar zabe ta 8 a mazaba ta uku a karamar hukumar Olorunda da ke jihar.
Bayan an gama zaben gwamnan jihar a shekarar 2007, sai Rauf Aregbesola ya kai kara a kotu.
Ranar 26 ga watan Nuwambar shekarar 2010 ne kotun daukaka kara ta ce Rauf Aregbesola ne gwamnan jihar.
Kuma ranar 27 ga watan Nuwamba ne aka rantsar da Rauf a matsayin gwamnan jihar Osun.
A halin yanzu Rauf ya kammala wa'adinsa na biyu. Kuma lokaci ya yi da zai mika wa wani ragamar mulki.
A lokacin da dai ake wanan zabe na gwamna masu abinci sun fito domin sayar wa mutane abinci.
A zaben na jihar osun ba a bar masu larura a baya ba domin su ma sun fito zabe.
Ministan Lafiyar Najeriya, Isaac Adewole, ya isa rumfar zaben da ke mazabarsa.
Masu zabe dai a jihar ta Osun sun fara duba sunayensu ne dai a rijistar zaben da ke rumfunar zabensu da sanyin safiyar Asabar.
Jami'ai masu sa ido zabe na kasa-da-kasa suna nan a jihar ta Osun don ganin yadda ake gudanar da zaben.
Dan takarar PDP a zaben Sanata Nuruddeen Adeleke ya kada kuri'a.
Jama'a, barka da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku yadda ake zaben gwamna a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya.